a kwarin da zata iya doguwar magana don kishiruwa ta galabaitar da ita a wunin yau. Ta tashi ba tare da tace komai ba ta wuce kitchen, ta zubar da shayin ta dauko wani kofin ta dawo ta sake hadawa Shukra wani shayin. Haka suka gama shan ruwan ba tare da ta kula kowa ba sai Shukra da suke cin abinci daga kwano daya.
…….
A kwance ya sameta a daki, ba wai bacci take yi ba kawai rufe ido tayi tana hutawa saboda yanda jikinta yake ciwo. Duk da babita tayi aikin gidan ba yau amma ta gaji, musamman da yake an yi kishiruwa. Gashi bata son ta ajiye azumin saboda ko bata yi ba ma bata iya cin abincin kirki; garama da tayi azumin ta samu bayan shan ruwa ta ci couscou ta koshi.
PAGE 40
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Da sallama ya shigo dakin, ta dan juyo ta amsa sallamarsa, bayan ya zauna yace ‘Sai yaushe zaki shirya yaran su kwanta ne?’
Tace ‘Barinsu nayi da yake daren na azumi ne kuma gobe ba fita za ayi da safe ba, zuwa 10pm sai a kwanta.’
'Ok, haka ne kam.’
Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace ‘Ina ga kiyi hakuri da aikin nan wannan yarinyar ta daina shigowa gidan nan. Ki bari a sami saukin cutar nan tunda kina ji tace cutar ma ta masu kudi ce don haka ba zata daina yawonta ba.’
Ta tashi zaune takalleshi sosai tace ‘Don Allah ka bari, wallahi nayiata magana kuma gobe ma zan sake mata magana. Ka ga ga azumi wallahi abincin shan ruwa kawai ya isheni balle ga su wanke-wanke da shara, zan mata magana na san in sha…’
Kafin ta karasa ya katseta yace ‘Ki fahimceni ba wai don bana son ta tayaki aiki bane, nima na fi so a tayaki. But she's putting all of us at risk, tunda zata ke ta gama yawonta a gari sannan ta dawo ta shigo mana gida tana mu'amala da yara da kuma ke anyhow. Bana son a sami matsala please ki sallameta kawai, idan pandemic din nan ya wuce zata iya dawowa ai.’
‘To ya zan yi da aikin? Gashi ba dadi nake ji ba, kamar kana mantawa da cikin jikina.’
'Ni ban ce miki na manta na, Amma aikin gidan nawa yake? Duka ba wani abu ne da zai gagareki ba fa, kina ma fa da damar ki ajiye azumin idan yana wahalar dake ba wani abu bane. Amma aikin gida ai ba abinda zai gagareki bane, itama Ma'un haka take hadawa da ciki da goyo kuma da aikin gaba daya. Amma gaskiya a hakura da shigo da kowa gidan nan for now, gaskiya. Da safe ma idan ta zo daga gate zan ce ta koma. Kiyi hakuri ki fahimceni, ke kanki you are at risk idan ta kwaso cutar nan ta shigo mana da ita gidan nan.’
Cike da takaici ta sunkuyar da kai tace ‘Shikenan, duk yanda kayi.’ Ta zame ta kwanta.
Ya bude baki zai yi magana sai kuma ya ga gara ya kyaleta ta huce zuwa an jima ya sake yi mata bayani, amma ba zai iya bari ba ga halin da ake ciki kuma a dinga shige da fice a gida. Idan cutar nan ta shigo gidan ya zai yi da ita? Ya mike ya fice ya turo mata kofar.
PAGE 41
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta juyo ta kalli kofar ta harareta kamar shine a wajen sannan ta ja tsaki ta juya. Ta San akwai cutar to amma ai ta yiwa Ummin magana, yanzu ya yake so tayi da aikin gidan nan ga azumi? Da ma ace zai tayata aikin me ko kuma ya bari yaranshi su dinga tayata to da sauki. Amma haka zai zuba yaranshi a gaba suna zaune suna kallon TV ita kuma tana kitchen ita kadai. Ta share kwallar da ta gangaro a idonta ta gyara kwanciya; bata san yanda zata kasance ba sai dai kawai ta bari taga yanda hali zai yi goben.
……..
Ko da gari ya waye Khadeeja bata ma San lokacin da Ummi ta zo ba don tun daga bakin gate ya tareta yace ta koma kada ta sake zuwa sai bayan Sallah.
Sai wajen Sha daya sannan ta fito ta dan gayggyara gidan, wanke-wanke ne ma ya bata mata lokaci don yana da yawa sosai. Haka ta wankesu gaba daya a famfon waje sai da shigo kifewa sannan Afaf ta tayata.
Tana gamawa ta shige dakinta ta kwanta; bata taba jin gajiya irin wannan ba a rayuwarta, gashi duk wata gaba da take jikinta ciwo take yi.
Tun 3pm ta shiga kitchen ta fara kokarin hada kayan Shan ruwa; dankali da kwai zata soya sai jollof sphagetti sannan ga peppersoup din nama. Da akwai ragowar zobo na jiya don haka ba zata sake hada wani ba.
Yaran suna zaune a parlor ta zo ta wuce ta shiga kitchen, tana wucewa Afaf ta bi bayanta. Ta so ta Koro Afaf din daga kitchen amma dai ta hakura ta barta, suna yin aikin. Basu dade da farawa ba Habib ya shigo kitchen din, ya kalli dankalin da aka ajiye a tsakiyar kitchen din yace ‘Anti wannan ferayewa za ayi?’
Tace ‘Eh, so nake na dora kifin nan sai na zauna na feraye shi.’
'Kawo wuka na feraye Anti.' Ya fada yana Bude cabinet, ya zaro roba ya tara ya debu ruwa.
Tace ‘Ka barshi Habib zan feraye.’
Ya sa hannu ya dauki wuka a kan sink yana cewa ‘Na iya feraye dankali fa Anti, idan na feraye miki sai ki yanka.’
Bai saurari amsarta ba ya tsuguna ya fara feraye dankalin.
Afaf ta ajiye kayan miyan da ta gama wankewa a kusa da Khadeejan tace ‘Anti na wanke kayan miyan.’