NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 17 of 105

a kashe shi don haka mutane kadan ne ma suka je jana'iza. Matarsa ma tana kwance Kuma itama COVID 19 din ake tunani don har an kaita isolation center. Khadeeja tana shiga dakin ya bata labari, tace ‘Allah ya sa ya huta. Ashe Corona din nan gaske ce.’ Da mamaki ya kalleta yace ‘Oh, ke da baki ma yarda ba kenan? To wallahi ki kula sosai don babu wahala an dauka. Ai shi yasa ma aka saka lockdown don idan dai mutane suna yawo to zasu yi ta rabata a junansu. Kina ji dai Baba Rilwanu ya rasu kuma an saka matarsa a isolation. Garama ki San wa kike bari yana shigowa gidan nan kada ki kwaso mana, especially ke da kike da ciki.’ Ta Dan zaro ido ‘Allah ma ya kiyaye, in Sha Allah we are safe.’ Suna nan zaune ya daga waya ya kirawo Alhaji yayi masa gaisuwar abokinsa, suka dauki lokaci suna waya tana jinsa yana ta amsawa da eh, ava, toh, haka har suka gama wayar. Yana ajiye wayar ya dubeta yace ‘Ai muna da Dettol ko?’ 'Eh akwai babbar roba ma kuwa.’ 'Don Allah a dinga goge duk wani surface na gidan nan da ruwan Dettol, musamman hannuwana kofa da guraren da mutane suke tabawa. Duk wani shige da fice ma a hakura da shi don wallahi corona Dina nan da gaske take, sai mutuwa ake. Gara a daina shigowa gidan kada a kwasawa yara muna zamanmu lafiya.’ Ta gyada kai ‘Hakane, ai da yake ma babu wanda yake shigowa gidan sai Ummi, itama da ta gama aikinta take fita.’ PAGE 38 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta gyada kai ‘Hakane, ai da yake ma babu wanda yake shigowa gidan sai Ummi, itama da ta gama aikinta take fita sai dai da yamma kuma nace ta dawo ta tayani girkin Sha ruwa ta tafi.’ 'To sai kun yi taka tsan-tsan.’ ……… Har azahar tana ta jiran Umminta zo ta gyara gidan amma bata zo ba. Can wajen 2pm suna zaune a parlor gaba dayansu aka buga gate. Da kansa ya tashi yake ya bude, jimawa kadan ya shigo Ummin tana biye da shi. Ya koma ya zauna a inda ya tashi. Ummi na shiga gidan Shukra ta tashi da gudu ta rungumeta tana cewa ‘Ummi na tsefewa Baby na kanta yau ita Zaki yiwa kitso.’ Ta dauketa ta mika mata hannu suka tafa tana cewa ‘Yauwa kawas, bari nayi sauri na gama shara mu zauna kitso don babynki anti yalash ce.’ Ta sauketa tana ta murna. Ta rage tsawo ta gaida Khadeeja, har zata shige kitchen Khadeejan tace ‘Shine baki zo da wuri ba yau Ummi? Gashi annfara azumi.’ 'Wallahi Anti cikin gari muka shiga.’ Da mamaki tace ‘Ke Ummi ana lockdown din kike fita.’ 'Yo Anti ai mu a kasa muke yawonmu, babu inda bam zuwa.’ 'Ai kuwa za a kamaku Ummi ko ku kwaso cutar da ake gudu.’ 'Ta masu kudi ce Anti.' Ta shige kitchen tana dariya. Bata dade da shiga kitchen din ba Shukra ta dubi Khadeeja tace ‘Anti zan Sha ruwa.’ Daga nana ta kwalawa Ummi kira ta debo ruwa ta mikowa Shukra. Kadan ta kurba har Ummin ta juya zata koma kitchen din Shukra ta kurbi ruwan ta mika kofim tana cewa ‘Na Sha Ummi tafi da shi.’ Ta karbi ruwan a Kofi ta juya ta nufi kitchen din, tana juyawa ta kafa kai ta shanye ragowar ruwan sannan ta wuce kitchen din. Mustapha ya kalli Khadeeja yace ‘Wannan yarinyar kuwa ta san me take yi? Ana maganar Corona tana abubuwa anyhow. Ta gama yawonta a gari Kuma ta zo tana daddumar abubuwa kuma har tana using utensils din yara? Corona din nan fa is real.’ Khadeeja ta kalleshi ta langabar da Kai tace ‘Kayi hakuri zan yi mata magana.’ 'To Allah ya kiyaye.’ PAGE 39 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Nan da nan Ummi ta gama aikin gidan ba tare da wata matsala ba. Bayan la'asar Kuma ta dawo. Itace tayi komai don Khadeeja kujera ta saka ta zauna a kitchen din tana gaya mata abinda zata yi, shi kuma Mustapha yana zaune a parlor shi da yaransa suna kallon TV. Kafin magriba sun gama komai Khadija ta kawo ta jera a kan carpet domin Mai gidan ya ce yau a kasa zasu Sha ruwa ba a table ba. Zobo ne mai sanyi, sai dankali da kwai, daga gefe kuma ga farfesun kaza da kuma couscous da sauce. Kafin a fara kiran Magriba ta zubawa Ummi komai ta sallameta ta tafi. Sai da aka idar da sallar Magriba sannan suka zauna shan ruwa; kowa da plate dinsa wanda Khadeeja ta zuba masa abinci ga soup bowl a gefe, ita kuma Shukra kwanonsu daya da Khadeejan. Bayan ta gama zuzzuba abincin kuma ta fara kokarin hada musu shayi. Bayan ta gama ta hada nata sannan ta dauki karamin kofi zata zubawa Shukra daga nata login, Mustapha ya dubi kofin yace ‘Wannan ba kofin da yarinyar nan ta sha ruwa da shi dazu bane?’ Ta cigaba da juyewa tana cewa ‘Shine, ai ta wanke shi.’ 'Kika sani? Bayan ruwa kawai aka Sha da kofin kuma kina zaune a nan tayi wanke-wanken, idan fa kifewa kawai fayu bayan ta gama dambara baki a jiki?’ Ta gyara zama zata mikawa Shukra shayin yace ‘Ya zaki bata, ki canza mata cup mana. Ba kya jin me nake fada ne.’ Ta kalleshi kamar zata yi magana sai kuma ta fasa; ba zata iya fara musu da shi yanzu ba domin bata ma d
🏠