NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 16 of 105

ifiyarta ce bata da lafiya don haka wanen mai magani suka je, sai dai ko zuwa lokacin da za a sake bude gari shine zata samu ta taho idan mahaifiyar tata ta sami lafiya. Kamar tayi kuka haka ta ji domin tana ganin kamar dawowar Baba Habi zai rage mata wata wahalar; gashi azumi saura abinda bai fi kwana goma ba. A take dabara ta fado mata, ta dauki wayarta wadda ta juye; har ta nemo lambar Mommy zata kirawo sai kuma ta fasa ta kirawo lambar Baffa. Bayan sun gaisa ta sanar dashi tana so Nabila ta zo ta tayata zama zuwa lokacin da za a sake Bude gari in ya so sai ta tafi. Sai da ya Dan yi jim sannan yace ‘Kiyi hakuri Khadeeja,ba zata zo ba, haka aure yake. Kanwarki balagaggiya ba muharramar mijinki bace gashi gidanku ba wani Kato ba, ba zai yi ma'ana ba ana wannan zaman na wuni a gida na turo miki ita. Amma dai zuwa lokacin da za a sake Bude gari zan sa Mommy ta duba Miki dattijuwa wadda zata zo idan Kuma Mai aikin naki ta dawo ma shikenan. Kin gane ko?’ 'Na gane Baffa.' Sukayi sallama ta ajiye waya. Wani malolo ne ya taho ya tokare mata makogoro saboda takaici; yanzu Baffa ba zai bata Nabila ba kenan yana wani zance? Take hawaye ya wanke mata fuska, ta dauki wayarta ta shige daki saboda kada yara su sameta tana kuka. Tana ji tana gani aka sake mayar da garin aka kulle babu Baba Habi babu Nabila, haka ta cigaba da bautawa Mukhtar da ‘yayansa babu abinda ya sauya. ………. Saura kwana biyu azumi aka sake bude garin na wuni daya saboda a dan yi sayayyar azumi. Tun da safe Mustapha ya sa ta shirya yaran ya kwashesu sai gidan Hajiya. Basu dade da fita ba aka buga mata kofa, kamar ba zata Bude ba da oda tana tunanin ko almajiri ne. Amma sai ta daure ta fito don ta bude da aka cigaba da bugawa. Tana budewa ta ci karo da Mommy tare da Nabila, Ahmad ne ya ajiyesu ya juya sai da yamma zai dawo ya daukesu. Tun a bakin gate ta rungumo Mommy suka shigo gidan tare tana ta murna. A nan parlor suka baje, ta sa Nabila ta dauko musu ruwa da lemon suna Sha suna hira. PAGE 36 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Daga baya Nabila ta tashi ta fara gyara mata gidan; ta barsu a zaune ita da Mommy suna hira. Mommy tace ‘Baffa dai yace kada a bar Miki Nabila, Mai aiki Kuma Ina ta cigitawa. Kin san yanzu duk tsoro ake ji saboda wannan lockdown din.’ 'Watakila ma yau Baba Habin zata dawo, zai iya yiwuwa ma tana can gidan Yayarsa tasa sai ya taho da ita idan zasu dawo.’ Mommy tace ‘To Allah yasa.’ 'Ya jikin naki?’ 'Da sauki Mommy, yawun nan ne bana so wallahi ga wani yawu da bana iya hadiyewa.’ 'Wannan Kam hakuri Zaki yi, Allah ya raba lafiya.’ Jimawa kadan Mommy tace ‘’yayan naki basa baki matsala ko?’ 'Babu matsala Mommy,shine ma yake sa mana Ido wallahi amma da zai barsu yaran basu da matsala.’ 'Da sauki ma idan hakane, Shima a hankali Zaki dinga nuna masa in Sha Allah zai gane idan ya ga kun hade Kai.’ 'Hmmm!’ Haka Mommy ta wuni a gidan nan tana kokarin ganowa ko da matsala, sai dai har ta tafi bata ga inda gagarumar matsalar take ba. Ta dai bawa Khadeeja shawarwari kuma da alkawarin sami mata mai aiki da zarar gari yayi lafi. La'asar tana yi Ahmad ya zo ya daukesu suka tafi. Suna tafiya ta dauki waya zata kirawo Mustapha taji ko Habi ta dawo, sai dai kafin wayar ta shiga ta jiyo motsinsu yana Bude gate don haka ta mayar da wayar ta ajiye. Tun kafin ya zauna ta kula kowa ya shigo bata ga Baba Habi ba, tace ‘Ina Baba Habi? Na zata tare zaku taho.’ 'Hm! Wai mahaifiyarta ta rasu jiya don haka ba zata dawo ba sai bayan Sallah, lokacin an yi 40 days.’ Tace ‘Subhanallahi. To don Allah kace da Yaya Jiddan ta sami mana wata saboda azumi, wallahi hidiman da yawa ga lockdown.’ Ya karaso ya a zauna sannan yace ‘Na gaya mata, ta dai ce wai wahala suke saboda lockdown tsoron baro gidajensu suke yi.’ 'To ga mu ga Allah, Mommy ma ta zo bayan kun fita itama na ce ta cigita mana.’ A ranar haka Khadeeja ta kwana cikin zulumi saboda fargabar yanda zata yi da aikin azumi. Kafin gari ya waye dabara ta fado mata, tana fatan Allah ya sa kada wani abu ya kawo matsalar. PAGE 37 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ko da gari ya waye sai wajen 10am sannan ta yiwa Mustapha bayani wanda ya bata dama sannan ta tafi gidan su Ummi; makotansu inda a nan ake yiwa su Afaf kitso. Ta samu ta roki arziki a wajen mahaifiyar Ummi a kan ta dinga zuwa tana tayata aiki zuwa bayan Sallah. Ba tare da wata matsala ba ta amince mata tunda dama ita kewa yaran kitso. Tun a ranar Umminta fara taya Khadeeja aiki, gashi bata da kuwa don haka cikin walwala suka wuni. Kullum haka zata bata abinci ta ce ta koshi sannan Kuma idan zata tafi ta zuba mata a falsak; ga alkhairi Kuma kullum tana yi mata. —---- Ranar da aka tashi da azumi Alhaji wato mahaifin Mustapha ya kirawoshi da safe ya sanar da shi rasuwar abokinsa Alhaji Rilwanu; nan yayi masa bayani cewa ai Covid 19 ce t
🏠