NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 14 of 105

da tsintsiyar ya shige gidan. Ya juya kan Khadeejan wadda take cigaba da wanke-wankenta yace ‘Wai me kika mayar da yaran nan ne? Habib ne zai iya share wannan tsakar gidan ga kura ga komai. Itama Afaf din wannan uban ruwan ai sai tayi mura. Ke kika ce a bar mai aikinki ta tafi gida, da kin bari ai da yanzu tana nan; sannan kuma ki dinga basu aikin da ya fi karfinsu? Bana son irin wannan; bana son ki dinga yiwa yaran nan kallon wasu manya, ki dauke su kamar ke kika haifsu shine zaki iya yi musu adalci. Idan an ji wani almajirin yana bara sai a kirawoshi ya karasa wannan aikin ko kuma tunda kun kusan gamawa ki karasa zuwa gobe a sami wani almajirin.’ Ko kallonsa bata yi ba ta cigaba da wanke-wankenta, ya ja tsaki ya juya ya nufi cikin gidan. Ta share hawayenta ta cigaba da wanke-wankenta. Ba zata iya dogon surutu ba sannan kuma bata son tana biye masa suna fada a gaban yara, ita yanzu duk wani abu da zai sa ayi magana ma bata so; shi yasa ta gwammace tayi masa shiru. PAGE 31 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Sai da ta gama wanke-wanken nan tsaf sannan ta kwashe sharar, ta debi kwanukan ta shigar cikin gida. Suna zaune a parlor suna kallon TV. Tana kitchen din tana kife kwanukan Afaf ta shigo ta sameta, ta dauki kwanukan ta fara kifewa. Ta dubeta tace ‘Afaf je ki zauna ai na kusa gamawa.’ Tace ‘Bari na tayaki Anti, ai nan babu ruwa.’ Ba don ta so ba ta kyaleta sai da suka kife kwanukan gaba daya ta mayar da komai inda yake sannan ta wuce daki su kuma suka cigaba da kallonsu. Can wajen 1pm bayan sun yi sallar azahar ta fito daga daki ta shiga kitchen; tuwon alkama da miyar danyen kubewa ta dafa jiya da daddare amma duk sai suka ki ci. Da yake akwai biscuits da cake sai kowa ya ci ya sha lemo, ita da abbansu ne kawai suka ci tuwon gashi ta dafa shi da yawa. Da safe kuma da kwadayi ta tashi don haka wainar fulawa ta soya kowa yaci. Wannan ragowar tuwon shi ta dauko daga fridge ta dumama shi, ta dumama miyar wadda ta sha kaza da nama. Ta zubawa kowa abincinsa sannan ta kirawosu kowa ya dauki nasa suka zauna a table. Kallon tuwon kawai Habib yakeyi yana juyashi amma yaki ya fara ci, tana kallonsa tayi banza da shi ta cigaba da kai lomarta tana bawa Shukra don ita tuwon yayi mata dadi. Jimawa kadan ya dubeta yace ‘Anti tuwon jiya ne fa?’ 'Eh, shine, ko ci ko bari.’ ta fada a gajarce ta ci gaba da cin abincinta. Daidai nan Abbansu ya fito ya zauna a table din, ta tura masa flask da plate. Ya bude flask din ya kalli fuskokin yaran sannan ya kalleta yace ‘Wannan ai tuwon jiyane, ba a yi abincin ranar bane?’ ‘Shine abincin ranar ai, dumamawa aka yi tunda babu abinda yayi.’ Nasreen wadda itama take ta juya nata tuwon tace ‘Abba wallahi tuwon ba dadi, ni bana son bakin tuwo gaskiya.’ Shi din yana son tuwon alkama don shine ma ya sa aka yi tuwon da daddare, don haka ya zuba malmala guda ya fara ci. Ya sake duban fuskokin yaran, bayan ya hadiye lomar da take bakinsa yace ‘Yanzu ba wani abu da za a iya dafawa yaran nan, Afaf ce kawai take cin tuwon nan.’ Ba tare da ta kalleshi ba tace ‘Babu.’ Ta cigaba da cin tuwonta kamar bata san da su ba a wajen. Jimawa kadan Nasreen tace ‘Abba ni a hada min cornflakes. PAGE 32 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya dubi Khadeeja yace ‘Akwai cornflakes ko?’ Cikin halin ki in kika tace ‘Akwai.’ 'Da Allah a hada mata ta samu ta ci kafin ayi abincin dare.’ Tace ‘To.’ Ta ci gaba da cin tuwonta tana bawa Shukra a baki, yayinda ita kuma Nasreen ta tashi ta koma gaban TV. Jimawa kadan Habib ma ya mike, ya dauki kwanonsa da na Nasreen yana cewa ‘Abba nima na sha cornflakes din kawai.’ Ya wuce ya kai kwanukan kitchen ya dawo shima ya zauna a gaban TV. Bai dade da tashi ba kuma itama Khadeejan ta gama cin nata tuwon, ta dauke kwanonta ta kai kitchen. Ta fito daga kitchen din ta wuce daki ba tare da ta kallesu ba. Tana shiga ta saka pillow ta kwanta a tsakiyar gadonta, da yake ta gaji sannan kuma ta koshi tana rufe ido bacci ya kwasheta. Bata sani ba ko ta dade da kwanciya ko bata dade ba, kamar a mafarki taji Mustapha yana dan buga kafarta yana cewa ‘Khadeeja, Khadeeja, barci ma kike yi? Kin bar yara da yunwa fa ki zo ki hada musu cornflakes ko ki dafa musu indomie.’ Ta dan janye kafarta tana kokarin tashi; kafin aurensu fa baya kiran sunanta sai dai yace ‘yan mata, mekyau ko kuma yace babe. Tayi zaton idan sun yi aure next level zasu shiga a kara mata matsayi amma zata iya cewa tunda ta shigo gidan nan sau daya ya kirawota da babe a daren da suka tare. Yanzu kam yaci duba sai ceto don gatsal yake kiranta Khadeeja. Ta gyara zama tace ‘Me kake cewa?’ 'Baki bawa yara abinci ba kin zo kin kama bacci.’ Tana jijjiga kai tace ‘Kowa fa na bashi abinci baka gani bane?’ 'Habib da Nasreen nake magana fa.’ 'Oh, ba sun ce cornflakes zasu sha ba, ai akwai a kitchen din.’ ta fada tana kokarin kwanciya.
🏠