ya sami waje ya kwanta a kan 3-seater. Ya dubi Khadijan yace ‘Ita Nasreen ba a biya mata karatun?’
'Tace sai ta gama yiwa ‘yar tsanarta kitso.’ ta bashi amsa ba tare da ta dubeshi ba.
Nasreen tace ‘Na ma iya karatun Abba, kitson nan nake so na gama tukunna.’
Yayi dariya ya cigaba da danna wayarsa.
Bayan sun gama karatun ta koma daki ta kwanta su kuma suka cigaba da kallonsu na TV.
………
A kwance take a gefen gadon da alawar tomtom a bakinta saboda yawu, ya zauna a kan kujera. Ta juyo ta kalleshi ta koma ta cigaba da kwanciyarta don bata son magana. Jimawa kadan ya kirawo sunanta, ta amsa sannan ta juyo.
Ya kalleta yace ‘Wai me yasa bakwa karatun ne da Nasreen?’
Tace ‘Bata so ne, ni kuma ba dadi nake ji ba shi yasa ba zan iya surutu da ita ba kawai na kyale ta.’
‘Ya kamata idan ma wani abu kika saka a ranki game da Nasreen ki cire, duk abinda zaki yiwa yaran nan kiyi musu gaba daya kuma kiyi musu adalci. Ina kula komai zakiyi sai ki kyale Nasreen, idan banda haka ya za ayi ace Shukra ma da bata shiga islamiyya ba kina biya mata karatun amma ita Nasreen kin yi banza da ita.’
Tunda ya fara zancen ta mike ta zauna akan gadon tana kallonsa, maganganun da take so ta fada masa suna da yawa sai dai tana bude bakinta yawu ya cika bakin. Ta taune ‘yar guntuwar tomtom din ta hadiye da kyar, ta tabe baki ta kawar da kai kawai tace ‘Kayi hakuri za a gyara.’
'Ya kamata dai ki dinga yi musu adalci don dukansu ‘yayana ne.’ ya fada.
PAGE 29
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta zame ta kwanta zuciyarta har turiri take saboda takaici; shi yake hanata takurawa Nasreen, shi yake nuna baya son a dinga yi musu fada amma kuma yanzu yana mata maganar ba a karatu da ita. To ya zata yi da ita? Ita adalci ne wannan yake mata da zai ce ta dinga yiwa ‘yayansa adalci? Ta share kwallar da ta gangaro a idonta tayi kwafa.
Jimawa kadan ya tashi ya fice daga dakin.
………
Wannan wunin da kowa yake yi a gida ba karamin takurawa Khadeeja yake yi ba; tana cikin laulayi sannan ga hidimar gida da ta yara. Wuni suke cin abinci don haka gidan kullum kace-kaca ga wanke-wanke baya yankewa. Wasu lokutan tana samu ta danngyara amma wasu lokutan haka take kyalewa saboda ba zata iya ba.
Yau kwana biyu kenan dan almajiri da ta dauka yake zuwa yayi mata wanke-wanke da sharar tsakar gida bai zo ba; bata sani ba ko suma lockdown din ya shafe su don da dai suna fitowa tunda makarantarsu nan cikin unguwa take. Gidan gaba daya yayi kaca-kaca don kitchen har warin lalatacce abinci yake yi.
Suna gama cin abincin safe Abbansu ya mike ya shige daki.
Nan da nan ta saka yaran a gaba suka tayata suka fitar da wanke-wanken suka kai fanfon waje, ta turasu waje ta gyara cikin gidan tsaf. Tana yi tana hutawa tana tofar da yawu, zuwa karfe goma na safe ta gama.
Ta fito tsakar gidan ta tara yaran a waje daya, ta dubesu tace ‘Afaf muje fanfo ni da ke mu wanke kwanukan can, kai kuma Yaya Habib dauki tsintsiya ka share compound din nan, ka fara daga kan baranda. Nasreen da ke da Shukra ku tsince toys dinku ku zuba a kwando, duk wadda bata tsince ba ba zan bata sweet ba.’
Nan da nan kowa ya fara aiki.
Ta saka kujera a bakin famfo tana wanke kwanukan Afaf tana mata dauraya. Sai da suka cika karamin kwando da kwanukan ta kirawo Habib wanda ya kusa gama sharar tace ‘Ya Habib zo ka dauki wannan kwandon ka kai kitchen ka kwashe kwanukan a kan sink sai ka dawo da kwandon mu cigaba da zubawa.’
Ya dauka a nufi cikin gidan; a kan baranda suka ci karo da Abbansu yana fitowa. Ya dan ja baya don ya bawa Abban hanya ‘Kai ina zaka da kwanuka haka.’
'Anti ce ta wanke zan kai mata cikin gida.’
PAGE 30
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Yana daga kansa ya hango Afaf a tsakiyar kwanuka suna ta wanke-wanke ita da Khadeejan. A fusace ya karasa wajen, cikin tsawa yace ‘Ke Afaf me kike a nan? kalli yanda kike jika jikinki sai kin gama kiyi ta mura.’ Ya dubi Khadeeja yace ‘Ina yaron naki?’
Ta tofar da yawun bakinta a gefe sannan tace ‘Kwana biyu bai zo ba, nima ban san dalili ba.’
Ya dubi Afaf wadda ta cigaba da aikinta ba tare da ta kula da shi ba, ya daka mata tsawa yace ‘Ki fita daga cikin ruwan nan nace, me kika iya?, sai sanyi ya kama ki kina ta faman jika jiki. Fice kije ki canza kaya kuma kada ki sake fitowa nan.’
Ta dubeshi tace ‘Kwanukan ne da yawa, ni din kuma ba dadi nake ji ba idan muka gama gaba daya zata canza kayan ai.’
Habib ya karaso ya ajiye kwandon yana cewa ‘Anti gashi.’
Ya juya ya cigaba da shararsa.
Abbansu ya sake dakawa Afaf tsawa don haka ta fice daga wajen wanke-wanken ta shige gida. Har ya bude baki zai cigaba da magana ya hango Habib yana kwashe shara ‘Kai Habib wa ya saka sharar nan?’
Yace ‘Anti ce Abba, ai na ma gama kwashewa zan yi.’
'Ajiye tsintsiyar nan ka shige cikin gida ka bani waje.’ ya fada a fusace.
Ya jefar