NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 104 of 105

a magana mai zafi sannan take fita daga inda yake. Yayi tsaki ya cigaba da aikinsa don so yake ya gama aikin kafin ya kwanta. PAGE 247 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Haka rayuwarsu ta cigaba. Khadeeja taki yarda a mayar da aurensu sannan shi kuma ya kasa tunkarar Baffanta da maganar don ya san ba za a yi mata auren dole ba. Amm kuma ya ki ya daina bibiyarta; har ta kai baya iya sati bai nemeta yaganta ba. Idan ya je gidansu wajen Hammad ta ki fitowa to tabbas zai sameta a office. Waya kuwa daman bata yankewa don idan ma ta ki dauka haka zai yi ta kiranta har sai ta gaji ta dauka. Duk wata kalma da zai yi amfani da ita wajen ganar da ita ta yarda su mayar da aurensu yayi amma ta sanar da shi ba zata iya komawa ba. Duk lokacin da ta ji kamar zata hakura su koma idan ta tuna yanda yake banzatar da ita a gidan kuma ta tuna yanzun ma sai da ya rasa yanda zai yi da gidan sannan ya fara nemanta sai kawai ta ji ta fasa. Tana sane da duk wata rigima da ta faru a gidan tunda kusan duk asabar a wajenta Habib yake wuni, duk abinda ya dameshi sai ya je ya sameta ya gaya mata. Lokaci zuwa lokaci tana samun masu nuna sha’awar aurenta sai dai auren gaba daya ya fice mata daga rai; don haka yawancinsu bata ma bari su zo gidansu. Kuma duk inda taje idan dai ba an santa a wajen ba to tana gabatar da kkanta ne a matsayin matar aure don ma kada wani ya zo mata da wata magana; don haka mutanen da suka santa sai suka kasu kashi biyu, wasu suna ganin tana da aure wasu kuma suna ganin bata da aure. Amma kuma yawancin mutane kasa tambayarta sukeyi. ______ EPILOGUE Bayan shekaru 3. An yi auren Afaf an kaita gidanta, yaron da ta aura kanin abokin Abbanta ne. da kanta taje ta kaiwa Khadeeja katin bikin nata wanda ta karba cike da girmamawa. Tayi mata magiya a kan taje amma duk da haka ba taje ba, domin bata son abinda zai hadata da Naja da dangin Mustapha a cikin taro. Kuma duk yanda Mustapha ya so ya sakata a cikin shawarar bikin Afaf din da inda zai sayi furniture haka ta zame da wayo da dabara har ya gaji ya rabu da ita. Yana nan dai yana bibiya da kuma addu’ar ta yarda su mayar da aurensu. Kuma a yanda yake fuskanta tabbas hakansa ya kusa cimma ruwa. PAGE 248 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Yana zaune a dakinsa a kan dadduma yana hutawa bayan sallar la’asar kwana biyu bayan auren Afaf haka kawai ya dauki waya ya kirawo Khadeeja. Ya gyara zama ya jingina da bangon da kofar dakin take jiki ta yanda idan aka budo kofar aka shigo zai zama yana bayan kofar kenan. Bayan ta amsa suka gaisa suka shiga hirarrakinsu, tana tambayarsa labarin biki. A haka har yace ‘Kin ga da kin yarda ai da tare da namu za adaura.’ Tayi dariya tace ‘Kai kuwa ka ki ka bar maganar nan.’ ‘Ba zan bari ba Khadija, har sai kin amince. Ko na tsufa ma sai na dawo dake ko da takaba ne kya yi min sai mu hadu a aljannah.’ Dariya kawai tayi don bata da amsar da zata bashi. Suka yi shiru na dan lokaci sannan yace ‘Duk wani condition da kike so Khadeeja ki saka nayi miki alkawarin zan cika in dai zaki zama mata ta. Just one more chance Khadeeja, ki daina wahalar da zuciyata haka.’ Tayi murmushi mai sauti ba tare da ta ce masa komai ba; tabbas yana nema ya gamsar da ita ta sake amincewa da aurensa, amma a halin yanzu bata san amsar da zata bashi ba. Ya gaji da shirun kuma yana ji a jikinsa cewa kalamansa sun fara yi mata tasiri. Ya katse shirun yace ‘Gobe da safe zan shigo, ok?’ ‘Ok, Allah ya kai mu. Amma ina da programme da safe so ka bari sai bayan azahar.’ ‘Ok, I will take you out to lunch then. No execuses.’ Tayi dariya ‘Ka dai san ba zan je ba ko? Kada ma ka fara wata rigimar da ban.’ ‘In dai rigima ce ai a wajenki na koya. I will see you tomorrow at lunch.’ Ya ajiye wayar ba tare da ya bari tace wani abu ba. Ko da ba zata yarda ya fita da ita lunch din ba ya fi so ta barshi ya kwana da murnan zai fita da Khadeeja gobe, in ya so idan yaje office din suyi fadan da suka saba. Tana tsaye a jikin kofar dakin tana jinsa, duk abinda ya fada tana ji. Sai da ya ajiye wayar sannan ta banka dakin ta shiga a fusace. Firgigit ya juyo ya kalli kofar da aka mako, yace ‘Ya haka kamar zaki fizge kofar? Me ya faru ne? ko wani abun ya biyoki?’ PAGE 249 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ta tsaya tana masa kallon raini tana jijjiga, sai da gaji da kallon nasa sannan a fusace tace ‘Mustapha na gaji da wulakancin da kake mina akna matar nan, shekara hudu ana abu daya saboda tsohon naci. Wallahi babu ruwan Allah da kun taba aure alakarku haramtacciya ce. Kuma idan ma zina kuke Allah zai kama ku.’ Fadan nata bai harzukashi don ya saba ji, idan ma bata ji yana waya da Khadeejan ba kulllum cikin duba masa waya take. Basa magana ta whatsapp don haka kullum cikin duna calls take, da zarar ta ga call din Khadeeja to sai tayi wannan masifar. Ya mike ya nade daddumar yana cewa ‘Kada k
🏠