NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 103 of 105

llahu ba zan sake auren Mustapha ba. Mutumin da ya daukeni ne kawai a matsayin solution to his problem. Ko yanzun ma da yake ta kokarin na koma gani yayi kirikiri matar tasa ta kasa kula masa da gidan da yara kamar yanda nayi. Shi yasa ya lallabo ya mayar da ni cikin wahalar da Allah ya rabani da ita. Ba zan koma na, can su karata.’ Ta mike ta dauki jakarta, don haka itama Yaya Maman ta mike. Ta san idan ta fiya takurawa da maganar yanzu zasu yi fada don haka sai ta kyaleta suka yi sallama ta kama hanya. _____ Wunin ranar gaba daya bai yi masa dadi ba. Ko da dai bai sa ran Khadeeja zata karbi kujerar ba tare da an kai ruwa rana ba amma kuma bai sa ran zata ki karba haka gaba daya ba ba tare da wata kofa ta sulhu ba. Haka ya wuni a office din babu walwala. Sai da yamma tayi sannan ya kwashi kayansa ya koma gida. Yana shiga dakinsa ya ajiye takardun hannunsa a kan mudubi; takardar kujerar da ya bawa Khadeeja ce a sama tare da wasu takardun na office. PAGE 246 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Tunda ya je sallar magriba masallaci ya dawo yayi zamansa a kasa shi da yara. Da farko ta dan zauna a wajensu ana hira gaba daya, daga baya kuma sai ta tashi ta haye sama ta barsu. Dakinsa ta shiga don ta samu ta huta domin nan ne kawai idan ta rufo kofar Rukayya ba zata so ta buga ta tasheta ba. Har ta wuce mudubin sai kuma ta koma da baya, ta sa hannu ta dauki envelope din da ta ja hankalinta. A bude take don haka sai kawai ta zaro takardun ta fara karantawa. Nan da nan kanta ya kulle; tabbas wannan sunan Khadeeja ne. To me hakan yake nufi? Suna tare kenan yanzu ta zama bazawararsa ko me? Tunda idan ba wata alaka ce tsakaninsu ba me zai saka har ya biya mata kujerar Makka? Kenan ma ita Mustapha zai rainawa hankali, ya saki matar sannan ya koma yama binta? Gaskiya ba zata yarda ba.’ Ta daga kanta ta hango wayarsa tana chaji a kan bedside durowa; nan da nan ta ajiye takardun ta karasa ta dauki wayar. Ta riga ta san PIN din don haka kai tsaye ta bude ta fara duba whatsapp; sai dai har ta gama dubawa bata ga sunan Khadeeja ba. Tana duba calls taga sunan ‘Sweetheart’ shine sunan da yayi saving lambarta tun yana zuwa zance kuma bai taba canzawa ba. Bayan rabuwarsu Najan ta goge ta saka maman Hammad amma bata san yanda aka yi ya mayar ba. Ta mayar da wayar ta ajiye cike da damuwa da takaici. Ta tashi ta dawo daya gefen gadon ta zauna ta zuba tagumi; tabbas zasu yi rigima da Mustapha don ba zai yiwu ba ya dinga zagayawa wajen tsohuwar matarsa suna raina mata hankali. Sai wajen karfe tara na dare ya hawo saman, lokacin ya je sallar isha’i ya dawo kuma sun gama cin abinci da yara. Zuwa lokacin itama ta gama duk abinda take yi ta kwantar da yara tana kwance a kan gadon dakinsa sanye da rigar bacci ta mike kafa tana kallo a waya ya shiga daki. Bayan ta masa sallamarsa ta mayar da hankali kan wayar hannunta. Kai tsaye ya wuce ciki ya canza kayansa sannan ya zauna a kan carpet din dake gaban gadon ya mike kafa ya janyo computer dinsa ya kunna ya kama aiki. PAGE 247 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Yawanci idan dai har yana da aiki to ya kan kai dare sosai a zaune yana aikin, ita kuma ba zata iya jira ba. Don haka ta mike ta zauna ta ajiye wayar da take hannunta tayi gyaran murya sannan tace ‘Uhm, na ga wata takarda, wai Maman Hammad ka biyawa Makka?’ Bai yi mamakin jin tambayar daga gareta ba duk da bai sa rai da ita ba, amma dai ya san ya manta ya ajiye takardun a kan mudubinsa. Ba tare da ya bar aikinsa ba yace ‘Eh ita na biyawa, akwai matsala ne.’ Cike da neman rigima tace ‘To kuma a yanzu meye tsakaninka da ita tunda naga dai babu aure. Ko kuma kun mayar da auren ne nice ban sani ba.’ Har yanzu hankalinsa yana kan aikin yace ‘Bamu mayar ba muna dai kan hanya.’ ‘To shine kuma ka biya mata Hajji.’ Ya dago ya dubeta yace ‘Eh, akwai matsala ne?’ ‘Gani dai nayi bai dace ba tunda babu aure a tsakaninku.’ ‘Wannan ra’ayinki kenan.’ Ta kula so yake yayi mata wulakanci don haka ta mike ta zauna sosai tace ‘Ina fatan dai ka san yanzu ita din ba muharramarka bace, kuma ina fatan ka san ba zai yiwu ina nan gida ina maka biyayya wai ni matar aureba ka dinga zagayewa wajen tsohuwar matarka wadda ka saka da hannunka, ba zan dauka ba gaskiya.’ Ya dago ya kalleta rai a bace yace ‘Sai ki dau mataki a kai.’ Ta kula kamar haushinta yake ji sai dai bata san dalili ba, don lafiya kalau suka rabu da safe ya ajiyeta a office sannan ya fice; to meye ya harzukoshi hakan daga yin magana? ‘Kada fa ka gaya min magana daga tambaya, na dai gaya maka ba zai yiwu ba ina nan ka kulleni a gidanka a dinga ganinka a gari kana yawo da wata matar banzan.’ Ta fada tana mikewa tsaye. A fusace yace ‘Khadeejan kike cewa matar banza saboda wulakanci?’ Sai dai kafin ya rufe bakinsa ta fice daga dakin ta rufe masa kofar; wanda wannan dabi’arta ce idan dai ya bata mata rai sai ta gaya mas
🏠