NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 102 of 105

da iyalinka. Ka ga yanzu ni babu aurenka a kaina, idan taji kana zuwa wajena zaku iya samun matsala. Kazo kai baka sami natsuwa da ta gidan ba kuma ni ba aurenka zan sake yi ba.’ PAGE 243 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Ya jijjiga kai don baya son wannan maganar, shi yana ji a jikinsa Khadeeja matarsa ce shi kadai don haka duk tsawon lokacin da zata dauka tana yi masa yanda zai jure. Ya zaro envelope daga aljihunsa ya dora a kan tebur din ya tura mata gabanta yana murmushi yana cewa ‘Wannan na zo kawo miki daman.’ Ta dauko tana dubawa tana cewa ‘Me na samu.’ Ta zaro takardun daga envelop ta fara dubawa; kujerar Hajji Mustapha ya bata. Tana dubawa tana murmushi saboda yanda tunanin zata je Hajji ya faranta mata zuciya. Ta ninke takardu ta fara mayarwa cikin envelop din a daidai lokacin da murmushinta ya ragu. Ta tura masa gabansa tace ‘Na ji dadi Abban Hammad, na gode Allah ya kara arziki da rufin asiri. Amma kayi hakuri ba zan iya karba ba, ba wai don na raina ba ko wani abu. Na gaya maka ba zan sake aurenka ba so kaga babu wani dalili da zai sa na karbar maka kujerar Hajji. Kuma ko na karba ma Baffa ba zai taba barina naje ba sai dai a daura mana aure kafin na tafi; kuma wannan ba zai yiwu ba. Please kayi hakuri! Amma na gode sosai.’ Kafin ta gama bayanin fuskarsa ta canza gaba daya, ba tare da ya dauki takardun ba yace ‘To ki karba mana Khadeeja ki bari a daura mana auren, please ki daina guduna haka.’ Ta sunkuyar da kanta cikin damuwa tace ‘Ba gudunka nake ba, amma dai ba zan iya karaba ba.’ Suka yi shiru na dan lokaci. Jimawa kadan yace ‘To yanzu ya kike so ayi? Ni da sunanki na biya wannan kujera.' ‘Kayi hakuri ba zan iya karba ba.’ PAGE 244 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Suka sake yin shiru na dan lokaci. Kafin suyi magana aka kwankwasa kofar, ta amsa ta bada izini aka shiga. Wata mace ce abokiyar aikinta ta dan leko tace ‘Anti Khadeeja yallabi yace ke ake jira a studio za a fara.’ ‘Yanzu zan shigo.’ Ta fada tana shirin mikewa. Ta dubu Mustapha tace ‘Bari naje kada ka sa a koreni aiki.’ Yayi dariya shima ya mike, sai dai tana kula dashi bai dauki takardun ba. Ta mika hannu ta dauka sannan ta zagayo ta tsaya a gabanshi, ta mika masa takardun tana murmushi tana cewa ‘Kayi hakuri ka tafi da wannan, wallahi ba zan iya karba ba. Idan na karba ba zan iya da rigimar Baffa ba tunda na san ba zan aureka ba. Kayi hakuri please.’ Ya mika hannu ya karbi takardun yana tsareta da ido kamar mai binciken wani abun a idonta, har sai da ta kawar da nata idon. Ta wuce ya biyota a baya suka fito daga office din, suka jero har zuwa reception sannan tayi masa sallama ya fice ita kuma ta mike ta nufi studio din. Tana fatan Allah ya sa dai kada ta kwafsa saboda yanda Mustapha ya jagula mata lissafi; me zata yi da kujerar makansa? Wato ma shi har yanzu tunani yake saboda kujerar Makka yasa ta ki komawa gidansa? Bai ma san wacece ita ba kenan, zaman da suka yi tare bai sa ya fahimceta ba. Ba ta bukatar kujerarsa kuma ta san tabbas idan ba aurensa ta kuma yi ba ko kashi ta kai gida tace shi ya bata sai sun yi rigima da Baffa, kuma bata shirya karya ba saboda Mustapha wanda take so ya rabuda ita ya daina damun rayuwarta. …….. Tana tashi daga waje aiki ta wuce gidan Yaya Mama, tayi sa a yaran duk sun tafi islamiyya don haka ta sami Yaya Mama ita kadai. Bayan sun gaisa Yaya Mama tace ‘Bari na samo miki ruwa ko lemo.’ Ta dafe cinyarta tace ‘Barshi kawai sai da na tsaya na ci abinci sannan na karaso.’ Ba tare da bata lokaci ba ta fara bata labarin kujerar Makkan da Mustapha ya kawo mata dazu. Sai da ta gama bata labarin suka sheke da dariya a lokaci guda sannan tace ‘Wai ni zai saya da kujerar Makka dan rainin hankali.’ PAGE 245 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Yaya Mama tace ‘Ai kuwa dan rainin hankali lamba daya, wato tunda ki ce ya sakeki saboda kujerar Makka bari ya biyaki sai ki yarada ya mayar da aurenku.’ ‘Ashe kin gane.’ Suka cigaba da hira suna tuna abubuwan da Mustaphan yayi a baya. Sai da Magriba ta fara kawo jiki sannan Khadeeja ta fara shirin tafiya. ‘Bari na wuce kada magriba tayi min a nan.’ Yaya Mama ta dafa hannunta tace ‘Khadeeja, idan fa zaki koma gidan Mustapha kin san babu wanda zai hanaki ko? Don ni ina ganin ma gara ki koma can din tunda kin ga ko babu komai ga Hammad. Kuma naga har yanzu baki da wani manemin; duk da ma duk wanda zaki aura mijn wata ne don haka kin ga dole ki zauna da kishiya. Ni ina ga gara gidan Mustaphan tunda dai yayi nadama har yana kokarin ya faranta miki.’ Nan take ta bata rai, ta zare hannunta ta dan matsa daga kusa da ita sannan tace ‘Ba zan taba komawa gidan Mustapha ba, aure kuma baya gabana balle na fara damuwa da rashin manemi. Idan Allah ya saka ina da rabon aure a gaba to duk wanda Allah ya sa shine mijina zan aura amma fa in sha A
🏠