a matar gida da ban. Anya kuwa Mustapha? Rashin uwa ai ba hauka bane da zaka wulakantasu saboda Allah ya dauki ran mahaifiyarsu.’
Ya sake shafa kansa ‘Wallahi Alhaji akasi aka samu kuma in sha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba.’
Ya kawar da kai cike da damuwa yayi shiru, jimawa kadan ya cigaba ‘Ita Khadeeja ya wajen nata da Muhamadun? Kana zuwa dai?’
Ya gyara zama yana murmushi ‘Eh, ina zuwa. Jiya ma na je.’
‘To ya kamata dai ka san yanda za ayi ku daidaita tsakaninku tunda dai ka ga ita ba a taba samun wata matsala tsakaninta da yaran nan ba, hadawa tayi ta rikesu tun kafin ma ta sami nata. Kuma da ta sami natan ma babu abinda ya canza. Ka ga itace ta zama uwa ta gari a wajensu tunda gasu kalau da tarbiyyarsu.’
PAGE 240
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
‘Hakane Alhaji, in sha Allahu zamu daidaita.’
‘Ya kamata dai ka san abun yi tunda ka san dai yanzu a kasuwa take, idan baka maida hankali ba wani zai iya yi maka shigar sauri.’
Suka karasa hirarrakinsu sannan yayi musu sallama ya wuce office.
PAGE 241
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Dole tana ji tana gani ya kafa mata doka idan dai har zai ci abinci to parlor din kasa zai ci. Babu yanda bata yi da shi ba yaran su dinga hawowa sama amma yace ba zasu hau ba tunda ita saman take so a bar mata, haka ta hakura ta saka masa ido saboda abun yana nema ya zama matsala a tsakaninsu.
Duk wani taimako da aiki da malamai zasu yi mata tana kan yi sai dai abun yaki yi, idan yayi kamar zai kama sai kuma ya sake botsare mata. Idan dai tana son ganin walwalarsa to ta yiwa yaran nan yanda suke so kuma ba tare da ta yi masa wani korafi ba.
Burinta daya yanzu a aurar da Afaf domin haka ne kawai take ganin zata sami natsuwa a gidan nan. Don a halin da ake ciki komai zai yi da Afaf yake shawara, wasu lokutan ko ta bashi list din cefanen gidan sai ya tambayi Afaf abinda take bukata ita da kannenta ya siyo musu. Idan kuma ya kawo kayan sai ya tsaya a kasa Afaf din ta ware nasu kayan sannan ya hau mata sama da sauran. Haka dai take hakuri, musamman da yake ya iya lallabata ya tsarata kawai dai ya nuna mata yaran nan nasa ba zasu tabu ba.
Haka rayuwarsu ta cigaba.
¬-------
Duk yanda yake jin zai samu Khadeeja ta saurareshi ya gagara, gashi kuma sai a yanzu Allah ya jarrabeshi da kaunarta.
Kusan kullum sai yayi mata waya, idan ta ga dama ta dauka idan kuma ba ta ga dama ba taki dauka. Ya mayarwa kansa duk Juma’a da yamma sai ya je gidan duba Hammad, sai dai hakan bai bashi damar ganinta ba. Domin idan yaje ko da yayi mata waya haka zata saka a bude masa parlor din baki ta turo masa Hammad, har ya gama hirarsa da Hammad ya tafi ba zata fito ba. Don haka wasu lokutan sai kawai ya rutsata a office inda dole ta zauna su gaisa har su dan yi hira.
Abu daya ne yake hanashi zakewa a kan maganarta saboda har yanzu yana jin kunyar Baffanta, baisan da wane bakin zai je yace masa ya sake bashi auren Khadeeja ba. Shi yasa ya dage yake kokarin ganin ya gamsar da Khadeejan ta jewa Baffan da maganar da kanta.
PAGE 242
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Kwanci tashi har shekara ta zagayo.
Tun da ya gama hada takardun yake cike da farin ciki, haka ya kwana cike da zakuwa sabodan yanda yake son gari ya waye ya jr ya sami Khadeeja yayi mata albishir.
Yana fita office dinta ya fara tsayawa, yayi sa’a kuwa ta riga ta zo.
Kamar yanda ya saba a cikin office din ya sameta tana zaune tana editing script din da zata yi amfani da shi wajen gabatar da show dinta.
Yana shiga ya tura kofar sannan ya yiwa kansa mazauni a kujerar gabanta cike da walwala. Bayan sun gaisa yace ‘Kina jin dadinki fa, kin ga yanda kike sheki kuwa.’
Tayi dariya tace ‘Don Allah ka bari, haba. Ko waya ma baka yi min ba kace min zaka zo to da ka zo na riga na shiga studio fa?’
Shima dariyar yayi yace ‘Sai na jiraki mana. Ai idan kina son na daina zuwa wajen nan to ki yarda mu mayar da auren mu mu huta, in ba haka ba dole kullum na zo nan nayi attendance don duk masu shirin yi min shigar sauri su ganni su san ina nan ba fashi.’
Ta sunkuyar da kai don bata san me zata ce masa ba, amma dai yawana zuwan nashi office din ya fara gundurarta. Ba wai don bata so a ganshi bane kuma ba wai tana jin ya isa ya hanata kula wanda take son kulawa ba; kawai dai tana so ya dana bata space tunda ita dai ta gama magana a kan lallai ba zata koma gidansa ba kuma har yanzu hakane a ranta.
Muryarsa ce ta katse mata tunanin da ya kirawo sunanta, ta dago ta kalleshi suka hada ido sannan ta kawar da kai.
Yace ‘Ki sauwake mana wahala ki yarda mu mayar da aurenmu, duk wani abu da ya bata miki rai a baya nayi miki alkawarin ba zaki sake gamuwa da shi ba a zamanmu.’
Ta jijjiga kai ‘Na fahimceka Mustapha, amma dai kayi hakuri. Ba wai kaine ba zan aura ba, auren ne gaba daya ba zan yi ba. Don allah ka daina wannan maganar, ka mayar da hankali wajen kula