NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 100 of 105

bawa direban taxi din kudinta. Suka ja mota shima ya koma ya shiga motarsa ya kama hanya. Ya dai ji tace ba zata taba sake aurensa ba amma tabbas bai yarda ba, yana ji a jikinsa in sha Allahu zata yarda su mayar da aurensu. Yanda zai yi da baffa ne ma yafi damunsa domin ya san tabbas Baffa ba zai saurara masa ba. Haka har ya isa gida yana wannan tunanin, sai dai yana saka kafarsa cikin gidan ransa ya kara baci. Bai san a yanda zai je ya sami yaran ba sannan kuma ita kanta Najan yana jin haushinta do ba zai taba bata dama ta wulakanta masa yara ba. ____ Ana cikin kiran sallar magriba ya shiga gidan, don haka ko zama bai yi ba ya daura alwala ya ja Habin suka wuce masallaci. Ko da aka idar da sallar a can ya tsaya wajen magidanta unguwar suna hira, har sai da suka yi sallar isha’i sannan suka tashi daga hirar kowa ya koma gida. A parlor din kasa ya sami yaran suna harkokinsu, ya wuce ya haye sama. Tana zaune a parlor tana jiransa saboda bata son yanda tun da safe ya ki ya ko kalli inda take. Ita idan ana fada ta fi so ayi hayaniya kowa ya fadi abinda yake ransa, amma ya ma ki ya tambayeta me yasa ta yiwa yaran haka balle ta samu tayi masa bayani. Ba ta jin ya amsa sannu da zuwan da ta yi masa, idan kuma har ya amsa to tabbas ita dai bata ji ba. Ba tare da ya kalli inda take ba ya shige dakinsa. A fusace ta mike ta bi bayanshi. PAGE 238 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Yana tsaye a gaban mudubi yana rufe durowa ta shiga ta turo kofar, ta tsaya a bayan kofar ta rungume hannu tace ‘Ga abinci can a dining table.’ Ba tare da ya kalleta ba yace ‘Ki sauka da shi kasa a can zan ci ni da yara.’ ta sunkuyar da kai ‘To bari nace su hawo sai kuci a nan, duk da suma na zuba musu nasu abincin kuma duk tuwon ne dai.’ ‘Ba sai sun hawo ba ni zan sauka, ki dauka ki kai can.’ Ya fada sannan ya juya ya zauna a gefen gado. Ta karasa ta zauna a kusa da shi, ta dafa gwiwarsa ta dan marairaice tace ‘Don Allah ka bawa Hajia hakuri, wallahi abinda ta gani ba haka bane. Kai ma ka san babu yanda za ayi na ci wani abu na hana yara. Hawowa ne basuyi ba na ajiye musu nasu a kitchen kuma da ka shiga zaka gani.’ Ya kalleta shekeke yace ‘Ai ba yau kika fara ba, kuma ba yau na fara yi miki magana ba. Babu wani akuri da zan bata idan kin gyara halinki su yaran zasu gaya mata ai. Mugun halin da kike nuna musu kuma ki cigaba kada ki fasa.’ Ya mike zai fita, ta kama hannunsa itama ta mike tana cewa ‘Don Allah kayi hakuri, yaran da nake hidimarsu tun kafin na aureka kuma yanzu ribar me zan ce idan nayi musu mugunta?’ ‘Nima shine abinda nake mamaki, watakila daman ba don Allah kike yi ba ko kuma zugaki aka yi kika canza hali ni ban sani ba. Abinda na sani kawai shine kusan tun da Khadeeja ta bar gidan nan kika dage sai kin raba rayuwarki da ta yaran nan, ina kula da yanda kike kokarin ganin basu hawo benen nan ba saboda tsabar samun waje…’ ‘Don Allah ka dai wannan maganar, wallahi kai ma ka san ba haka bane. Naga dai ko gidan waye akwai part din mai gida inda ba a bari yara su shiga, amma in sha Allahu ba zan sake hakan ba tunda na ga kai ba haka ne tsarinka ba.’ Ta katseshi cikin kosawa. Ya zare hannunsa da ta rike ya mike yana cewa ‘Ki kawo min abincin parlor din kasa yanzu.’ Ya fice ba tare da ya saurari amsarta ba. Haka ta gama zumbura baki ta sauko ta kawo masa abincin nan parlor din kasa inda a zauna suka ci da yaran; duk da sun nuna msa suma tuwo aka basu irin nashi. PAGE 239 MIJIN MARIGAYIYA A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal) Haka ya kafa mata dokar idan dai yana gidan to a parlor din kasa zai dinga cin abinci wajen yara, babu rokon da bata yi masa ba a kan ya bari yaran su dinga hawowa saman ana cin abincin tare amma ya ki ya saurareta. Ya kula cewa ganin saman bene take kamar wani abu na musamman don haka ya yanke shawarar bar mata saman benen ita kadai. Ya yanke shawarar a kasa zai dinga zama hira kuma a nan zai dinga kallo yana cin abinci, in ya so idan zai yi bacci ya dinga hawa saman ya kwanta. Tayi yanda take so da saman ita kadai. ……. Yana sane ya ki zuwa gidan Hajia a ranan sai washegari; ya san idan ya je zancen nan bai huce ba Hajia da Alaji haduwa za suyi a kansa har sai ya rasa binda yake masa dadi. Don haka washegari yana tashi daga office ya wuce gidan Hajia. Bayan sun gaggisa ya sami Alhaji a parlor, yana gama amsa gaisuwarsa yace ‘Mustapha me yake faruwa ne a gidan naka? Ban ji dadin bayanan da na samu daga wajen Habib ba kuma sai ga Hajia ta je ta gani da idonta. Me yake faruwa ne?’ Ya gyara zama ya shafa kansa sannan yace ‘Wallahi Alhaji ‘yar matsala ce aka samu kuma na ma yi mata magana in sha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba.’ Ya tashi daga kashingidar da yake yana cewa ‘Yar matsala? ‘yar matsala fa kace Mustapha? An bar yara a kasa kamar masu zaman kansu amma kana cewa ‘yar matsala? Gidan naka har ya kai an raba tukunya, ta marayun yaranka da ban t
🏠