e ‘Anti wallahi idan aka biye mata sai an yi sati ana wannan tsifar, kullum haka ake fama da ita.’
Khadeeja tace ‘Ai ba a ma yi zaniyar ba ta bari an tsefe.’
Ta tsuguna ta gaida ita yayinda shi kuma ya ja hannun Nasreen din suka shige ciki.
Sai da ta kawowa Yaya Jidda ruwa sannan ta bi shi dakin. Tana shiga ta sameshi a tsaye yana cire kaya yayinda Nasreen take kwance a kan kujerar dakin, kafin tace wani abu yace ‘Wai me yasa ne sai an yi duka sannan za a yi tsifar? naga tun tuni dama ana mata kitson ban taba ji an doketa ba.’
Tace ‘Yanzun ma ba a doketa ba, ko Nasreen? Ta dai ki tsayawa a tsefe ne na takurata na tsefe mata, amma ba ayi duka ba.’
Ya kawar da kai ‘Ni dai bana son dukan yara, don Allah duk abinda yaro yayi kada a dokar min shi. Uwarsu ma bata dukansu, bana bari gaskiya.’
Ta sunkuyar da kai cikin kosawa tace ‘In sha Allah za a kiyaye.’
PAGE 22
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ta ajiye masa ruwan da ta kai masa tana cewa ‘Lunch dinka yana nan a table.’ sannan ta fito ta barshi a dakin.
Bayan ta dawo parlor din ta tarar Yaya Jidda tana ta yiwa Afaf tambayoyi, ta wucesu ta shige kitchen.
Ta tsaya a tsakiyar kitchen din gaba daya kanta ya kulle; daga shigowarsu suna nema suce ta doki Nasreen, to yanzu haka suke so a bar Nasreen din ta dinga yawo da kanta? Gashi Afaf tace makarantarsu ana duba kitso duk ranar Monday. Ta jijjiga kai ta karasa ta dauki saucer ta zuba cake da cin-cin ta debo lemo a fridge ta jera a tray ta kawowa Yaya Jidda da yaranta, bayan ta ajiye a gabanta tace ‘Ya wajen su Hajiya?’
'Lafiya kalau.’ Ta amsa ba yabo babu fallasa.
Sukayi shiru sai surutun Afaf da take ta bawa Naja labari. Shukra ta matso ta kwanta a jikin Khadeeja tace ‘Anti nima lemon.’
Ta shafa kanta ta dubi Afaf tace ‘Yaya ki dauko mata lemon wanda babu sanyi.’
Ta mike, har ta kama hanyar kitchen din Yaya Jidda tace ‘Ku ba zaku sha lemon ba?’
Afaf tace ‘Ai da shi muka je school.’
Shukra tace ‘Anti tace idan an kawowa baki abinci mutum ya daina cewa zai ci, ni ma dai kawai lemon zan sha.’
Khadeeja tace ‘Ki dauko muku lemon idan kuna so.’
Jimawa kadan Abbansu ya fito daga dakin ya wuce dining ya zauna ya fara cin abinci; yana cikin cin abincin ya juyo yace ‘Kai Habib kun ci abinci ne?’
Yace ‘Tun dazu Abba, acici har tayi round 2.’ Ya fada yana zungurar Nasreen.
Khadeeja ta mike ta shige daki, don gaba daya jikinta yayi sanyi. Ta kula kiri-kiri neman laifinta ake yi; kamar ma Yaya Jiddan zuwa tayi ta binciketa. Ta karasa ta zauna a kan gadonta ta zuba tagumi.
Bayan ya gama cin abincin ya shiga daki ya fito da mukullin motarsa, ya dubi Khadijan yace ‘Idan kun shirya muje na Kai ku saloon din.’
Gaba daya suka fice harda su Yaya Jidda, ya ajiyesu a hanya sannan ya wuce.
………
Tun daga wannan lokacin kuma sai Yaya Jidda ta mayar da shi dabi'a, duk Juma'a sai ta zo gidan. Haka zata zauna a parlor tayi ta kare musu kallo tana kula da duk wani motsinsu, ga tambayoyi wadanda idan ta gama yiwa yaran zata bi Khadeeja da neman karin bayani.
.........
PAGE 23
MIJIN MARIGAYIYA
A Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)
Ranar talata ce Kuma a ranar Khadeeja take sa ran zata koma makaranta, tun dare ta sanarwa Mustapha. Ya amsa mata ba tare da wata matsala ba.
Haka ta tashi tun kafin asuba ta shirya yaran tsaf, suna tafiya makaranta tayi Maza tayi wanka sannan ta dan rage aiki don tana da lecture 9am.
Bayan sun gama breakfast ta mike daga dining table tana tattara plates din tana cewa ‘Babe bari na saka hijabi na sai kayi dropping dina a school.’
Yace ‘Ok, but kada ki bata lokaci don kada ki makarar da ni.’
Kusan a lokaci guda suka fito daga dakin kowa a shirye, sun kawo tsakiyar parlor ta dubeshi tace ‘Yau Kai zaka dauko yara ko? Don ni Ina da lectures 9am to 4pm.’
Ya dan bata rai cikin nuna damuwa yana cewa ‘I thought Zaki dawo ki daukosu, kin san ni sai 5pm nake tashi daga wajen aiki.’
'To ai ka ga nima sai 4pm.zan tashi, Kuma I can't miss these lectures don last week ma ka ga ban je ba. Gara dai ka sami wani ya dauko su kawai.’
Ya Bude motar ya zauna yayinda itama ta zauna a kujerar gaba, yace ‘To ai ko an daukosu ma wajen wa za a kawo su tunda ba kya gidan?’
'Haka ne fa, most days ma lectures dina har 4pm ne.’
Suka yi shiru na dan lokaci; gaba daya ma shi ya manta tana wata makaranta. Yanzu ya take so yayi da yaran? Wa zai daukosu Kuma wa zai zauna da su? Wannan ai shine an gudu ba a tsira ba.
Muryarta ce ta katse masa tunani tana cewa ‘Babe ka ga da muna da Mai aiki sai ta daukosu ta shiryasu su tafi islamiyya kafin na dawo; musamman idan Babba ce.’
Cikin jin dadi yace ‘kwarai kuwa, zan yiwa Yaya Jidda magana sai a sami Mai aikin kafin next week.’
'No, ka bari idan na yiwa Mommy magana zata sa a sami kla garinsu, mutanen suna da Amana sosai ga aiki.’
Ba tare da ya kalle