An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
๏ปฟA hankali take tafiya domin ba sauri take yi ba, duk da dai magriba ta kusa amma ta san zata kai gidan nasu kafin a fara kiran sallar. Karar wayarta ce ta katseta, ta dan rage sauri a tafiyar tata sannan tayi kokari ta zaro wayar daga jakarta. Tayi murmushi bayan da ta ga wanda yake kiran nata. Ba tare da bata lokaci ba ta amsa wayar ta kara a kunnenta.
'Hey Babe.' Ta fada tana wani rangwada kai tare da juya kwayar idonta kamar dai ga Babe din a gabanta tana kallonsa.
'Mai kyau, ya kike?โ Ya fada daga daya bangaren.
'I'm fine. Yanzu nake dawowa daga school gashi nan na kusa shiga gida.โ
'Oh, nima yanzu na mayar da su Afaf gida wajen Hajiya. Mun je shopping ne and I bought a few things for you nake so na kawo miki later. Is that ok?โ
'Yes Babe, kai ma ka san ina nan idan dai kaine kake son ganina. Ya yarana? Hope suna lafiya?โ
'Alhamdulillah ga su nan. I just can't wait to have you so we can all live in one place na huta da visiting yarana.โ
'Aww! Kada ka damu, very soon in sha Allah. We will talk more about it idan ka zo in dha Allah don yanzu zan shiga gida ka san Mommy ta hanani waya a kan hanya.โ
Yayi โyar dariya yace โKuma fa hakane, to sai mun hadu.โ
Suka yi sallama suka ajiye wayar.
Da sallama ta shiga gidan tana ta fara'a kamar wadda aka yiwa wani babban albishir. Babu kowa a parlor din sai Mommy tana shirin tashi ta shiga sallar Magriba. Bayan ta amsa sallamarta tace โYau kuma haka kike tafe kina tallan macleans?โ
'Kai Mommy! I'm just Happy.' Ta fada tana dariya.
Ta wuce dakinsu yayinda Mommy ta shige nata dakin.
Tana sane da yanda take tafiya tana murmushi din kuma tana jin dadin hakan. Idan dai a kan Mistapha ne fiye da haka ma zata yi. Muryarsa kawai take bukatar ji ta shiga farin cikin da baya misaltuwa. Wata bakwai da suka wuce suka hadu, amma saboda yanda ya iya soyayya da tarairaya ya shiga zuciyarta kamar wanda suka yi shekaru a tare. Da ya sami yanda yake so ma da tuni an daura musu auri don shi a shirye yazo, itace take dan dakatar da shi don tana so ta gama level 1 kafin ayi mata auren.
2
Sai dai a daren jiya Baffanta ya sanar da ita cewa ta gaya masa ya turo maganar aurensu.
Ta jefa Jakarta a kan gadonsu wadda ta fada kan kanwarta Nabila. Nabila ta make jakar ta ja tsaki tace โAโa, mus