NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 8 of 44

uskarta. Me tayi maka haka da zafi? Bansan yaushe ka koyi wannan halin na saurin yanke hukunci da daukarsa a hannunka ba. Anya Kehinde, ba zaka dinga hakuri kana sassauta fushinka akan kananan abubuwa ba ga na kasa da kai alhalin kaida ita kuna shirin zama abu daya??? Mu fa mata duk inda muke sunanmu mata, daga lankwasashshen kashin hakarkarin kirjinku aka halicce mu, dole ayita hakuri damu, balle Hasinah da har gobe yarinya ce da bata kai ashirin da biyar ba, kuma marainiya… sannan…. sannan…kasan batada ko….”. Cikin karaji da nashi screaming din da ya firgita Murja. Wanda ya dame na Haseenah AbdulRasheed ya katse Taiwo, da iyakacin muryarsa yace. “Maraici nasa mace zama Alade ko dabba mai iya saduwa da shaqiqin mijin da zata aura, saduwar ma irin ta dabbobi? Irin…irin…”. Ya kasa karasawa sakamakon wani makoko da yazo ya tokare a makoshinsa, image din nasu ya kara gilma masa. “Hasbunallawu wani’imal wakeel”. Inji Taiwo “ko dai ka sha kwaya ne Kehinde?” Ya rintse ido da karfi. “Don Allah don Annabi daga yau sai yau…. Maman Kiki, na rokeki da darajar iyayenmu, ki manta da mun taba saninta, kada ki kara yi min maganar wata Hasinah daga yau na rufe babinta a rayuwata. Nenne ta fimu gaskiya, tsintacciyar mage bata mage, matsiyaci matsiyaci ne ko a tandun mai ka saka shi kandas dinsa zai fito ya nuna asalinsa na zina da halinsa na kwadayi, kada ki kara tuna min ita! I AM PURE AND I LOVE PURITY. Ni dan Sunnah ne cikin Uwa da Ubana, daga tsafta na fito ba najasa a jikina. Ki manta kin taba sanina da wata halitta wai ita Hasinah saboda Dabba ce…. karya ce! In dai a sanadina kika santa, kike kuma alaqar uwardaki da abota da ita, to daga yau na raba ku nasa almakashi na datse duk wata alaqa tsakanin ku, from thousand milestones. I hate them, I repeat I hate them! Har abada bani ba su!!!”. Murjanatu Taiwo, taji hankalin ta yafi nada matukar tashi, maganganun da yake yi are very dirty. Daga inda ya dauko Hasinah kadai, ya kawo ta kusa dashi, cikin rayuwarsa, zaka shaida girman son sa gareta. Tabbas ruwa baya tsami a banza inji Murjanatu, kalamansa kadai sun gama bayyana komai duk da cewa indirect ya fadesu. Taiwo sai nan da nan ta soma kuka don tana tsoron kada yayiwa kansa lahani. Gashi babu kowa a tare da shi a inda yake. “Abdulrasheed, my Kehinde, I am your only twin sister TAIWO! Gaya min me ya faru daku, ka ji Kehinde dina? As always, ka sani, zan rufe sirrinka, kuma ni zan fahimceka in karbi uzurinka, koda duk duniya bata fahimceka ba ni zan fahimta, zan kuma kasance a bayanka kamar kodayaushe, koda duk duniya bata bayan ka, be rest assured that your Taiwo will stand by you!”. Da irin wannan lallashi da ban bakin Taiwo take shawo kan Abdulrasheed, to yau ma da irin sa ta dage don ya gaya mata abinda ya faru tsakaninsa da Hasinah Ambursa exactly, ita da wa yake cewa ya tsane su haka babu ko sakayawa? Kalamansa dai, da wasu daga na Hasinah sun gama tona komai na kazantar da Hasinah din ta aikata, amma so take ya gaya mata abinda ya faru da bakinsa don tana shakka tana kuma tabaab Hasinan zata iya aikata hakan. Tunda dai a sanin ta da Abdulrasheed baida abokin fada balle masoyiyarsa, matar da yake burin zai aura yana kammala project na masters dinsa wanda Polo ya dauke masa hankali da tun shekaru biyun baya ya kammalashi? Inda wanda bazai taba boyewa damuwarsa a duniya ba komai girmanta ko muninta to Taiwo ce, abokiyar tagwaitakarsa, his very own twin, his confidant Murjanatu-Taiwo, duk abinda yake ciki a rayuwa ita yake fara fadamawa kafin kowa, komai zafinsa. Taiwo da Abdulrasheed sunada wani irin (twin bond) ga junansu da ko mahaifiyarsu Nenne Sappa, wani sa’in bata sanin girman sirrin amanar dake tsakaninsu. Itama kuma Taiwo hakan yake a gareta, Abdulrasheed shine confidant dinta, har sirrinta na mata wanda a matsayinsa na namiji bai kamata ya sani ba, amma Adulrasheed ya san komai na mata akan ‘yar uwarsa Taiwo, kamar lokacin da Taiwo ta samu girma wato lokacin data fara jinin al’ada lokacin suna ‘yan shekaru sha biyu shi ta fara sanarwa cikin tashin hankali da tsoron ko wani mummunar abu ta aikata, Abdulrasheed shi yaje chemist aka hado shi da always pad ba tare da Nenne ta sani ba, sai daga baya ne Nenne ta sani, bayan tuni Murjanatu ta iya kula da kanta da taimakon kaninta, akan Taiwo zai iya batawa da kowa itama haka, in yace kowa yana nufin KOWA! Itama din kuma haka yake a gareta, idan Taofeeq ya bata mata rai Abdulrasheed kadai take iya kira ta gayawa, domin a wurinsa ne kadai zata samu duk wani lallashi da shawarwari da kwarin guiwa da kuma goyon bayan da duk take nema cikin kowanne yanayi duk da kasancewarsa namiji. Abdulrasheed ne ya fara sani lokacin da ta samu cikin Hakeem, ko Toufeeq din bai sani ba yana can yawon duniyarsa, saida cikin ya girma. Abdulrasheed shi yayi ta kula da ita har ta haihu don gidanta ya koma da za
🏠