NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 7 of 44

kidaya su twins ne na musamman ta fannin fahimtar juna da kaunarsu da juna, haka kulawarsu ga damuwar kowannensu mai girma ce, don ta zarta ta common Yaya da kaninta, saidai ace ta wadanda suka fito duniya daga mahaifa daya, sannan a lokaci guda. Ubangiji Subhana da kansa yaga damar ya dunkulesu ya haliccesu tare a mahaifa guda, don haka zukatansu sau tari suna aiki da bugawa tare ne. Taiwo ke yiwa (twin brother) din nata Prince Abdulrasheed magana cikin lallashi na hikima da taushin murya. “Kehinde, me ke faruwa tsakaninka da Hasinah haka? How can I let her back to orphanage a shekarun girmanta don kawai ta bata maka rai? A kowanne relationship, na soyayya ko mu’amala, dama ai akan samu sabani which is normal, amma a wannan lokacin hankali bata yake yi bat, sai ayi kokari asa hankali ya nemo shi. Dama ka daukota da niyyar watarana in ta bata maka rai zaka maidata ne? Ko kuwa ka daukota ne don ka aureta ba don tun asali ka taimaketa ba?” (Daga ita sai Kakansu Emir da Babansu Dade suke kiransa Kehinde, kowa PRINCE yake cewa) kannensu kuma suce masa HAMMA. Maimakon ya bata amsar tambayarta kamar yadda ta bukata sai taji muryarsa (in despair) cikin wani yanayi yana fadin. “Taiwo Please! Let that PIG go I said! (Ki bar wannan Aladen ta tafi nace), in kuma kin ki toh, ya rage naki. For now, ki hada ni da Kiki!”. A yadda Murjanatu taji muryarsa kadai ta fahimci yana cikin matsananciyar damuwa da kunar zuciya, kuma da gaske yake muryar Kiki kadai yake son ji da shirmen zantukanta ya fiye masa zacennan da take masa na wadda ya kira “karya” kuma “alade” Hasinah. Kiki kadai yake bukatar saurare a wannan lokacin, baya son wani zance bayan nata, koda ABCD dinta zata yi masa ya fiye masa wannan wa’azin na Taiwo mai kama da a kafa mata drum ta hau kai tayi ta yiwa wasu amma bas hi ba. Jiki sanyaye Murjanatu tabi umarninsa, ta fito da wayar a hannunta zuwa dakin da Kiki-Ruqayyat take wasa da mai rainonta. “Uncle AK wants to speak with you Kiki!” Taiwo ta fadama Kiki, tana mika mata kan wayar. Da zumudi mai yawa yarinyar ta dirgo daga dan gadonta ta amsa, tana dokin jin muryar Kawun nata, wanda koda take yarinya karama ta san girman kaunarsa gareta ko Daddynta Toufeeq albarka. Sabida yadda yake janta a jiki har ta saba dashi a waya. Balle kuma in ya zo gidansu, tayi ta sukuwa a jikinsa kenan. Taiwo ta koma gefen gado ta zauna cikin damuwa ta zuba tagumi tana kallon shirmen da Kiki ke masa a waya na sunayen dabbobi da suka fara da harafin “A” fuskarta fal annashuwa, shi kuma Uncle din ya dage yana biye mata cooly. Dama tone na muryarsa kullum is cool amma na yau is more than cool is despair. A tunaninsa a wannan yanayin da yake ciki muryar Kiki-Ruqayyat kadai da shirmenta ne zai mantar dashi ya debe masa kewa, ya rage masa zogin zuciya da radadinta kan abinda ya gani, wato ya mantar dashi abinda Hasinah tayi masa. Kiki his beloved little niece, amma ina! Ko Kiki ta gaza yau, domin ta kasa mantar da shi bacin ran Haseenah dake kasan ransa, still yana nan yana sakadar ruhinsa har zuwa lokacin. Kiki ‘yar lukuta yarinyar data shiga ran Engnr. Abdulrasheed matuka, itace diyar Taiwo ta biyu bayan Hakeem. Ganin sun ki gama shirmensu shi da Kiki, ita kuma an barta cikin ci da zuci, yaki ma ya saurareta balle ya gaya mata hakikanin abinda ya faru, sai Murjanatu ta karbi wayar daga hannun Kiki ta bar dakin, don ita tafi kowa sanin yanayin da Abdulrasheed zai iya kasancewa a wannan lokacin in har da gaske ya yanke shawarar rabuwa da Hasinah kwatakwata. Ta san Abdulrasheed bai iya sabo ba, sabo yana wahalar dashi, wholeheartedlhy yake sabawa da mutumin da ya kwanta masa, balle sabonsa da Haseenah na kusan shekaru biyar, kasancewar ta san ba karamin so yakewa Hasinan ba, kafin ya iya yakiceta daga ransa zai sha matukar wuya. Hausawa suka ce wai sabo akewa kuka ba mutuwa ba! sabon da yayi da Haseenah shi zai fi wahalar dashi fiyeda soyayyarta, wadda dama tausayi ne jigonta da wasu hujjoji nasu. Don haka ta bar dakinsu Kiki ta soma takawa zuwa dakin ta don kaucema kunnen Bunmi. Sai da ta zauna a gefen gado ta tattaro nutsuwarta sannan ta sake koro masa tambaya, (wannan karon sounding absolutely serious with seniority domin kuwa da sunansa na yanka ta kira shi, wanda da wuya kaji Taiwo tayi hakan. Itada Kakansu Emir (Kehinde) kawai suke kiransa wato sunan shi na al’ada wato (Hassan). “I said what’s happening ABDULRASHEED? Tell me! Nace me ya faru? Ko me ke faruwa tsakaninka da baiwar Allah Hasinah haka?” A shaqare (kamar wanda aka shaqe maganar a makogaronsa AbdulRasheed yace da ita. “Babu komai! Ki yarda babu komai! Amma ki sani KARYA ce kuma ALADE ce!!!” “Naji na kuma yarda, amma yanzunnan ta kira ni tana kuka, kuka fa as in screaming any how, tace ka daina daga wayarta yau kwana biyu kenan, kuma kayi mata iyaka da zuwa inda kake…. Kace kada ta kara nuna maka mummunar f
🏠