NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 6 of 44

ta. Ta kuma tuna ita marainiya ce, da bata da kowa sai su. Murja ta kasa gane komai akan kukan Hasinah da maganganunta, wadanda bata san ina suka dosa ba, ta bata su ne a lullube, a kudundune, amma hakika ta daga mata hankali fiyeda yadda Hasinan tayi zato, kasancewar Taiwo a very cool and reserved person, wadda ko kusa bata son iface-iface da hayaniya yasa ta sa hannu ta toshe kan wayar da hannunta, ita dai ta san daga ita Hasinah har ubandakinta AbdulRasheed son juna suke kamar su hadiye juna don soyayyah, AbdulRasheed na takun-saka da mahaifiyarsu Nenne akan taki yarda ya auri zabinsa Haseenah, wani cikinsu bai taba kawo karar dan uwansa gareta ba sai yau da Haseenah ta kawo karar Prince, don haka Taiwo ta kasance a uku, ta rasa bayan wa zata bi a cikinsu. Da kyar ta nisa tace da Hasinah cikin lallashi, da gajiyawa da jin kukan da ihun nata na marassa tawakkali, cikin nuna matukar concern ga damuwarta tace. “Hold on Hasinah, kina ji na ko? Ki bar kukannan haka take it easy Hasinahty, ki tsaya har in yi magana da shi yanzu, idan na samu ya daga kirana, I will get back to you ASAP. Nima yau kwana uku kenan ban ji shi ba, bai kira ni ba, nima kuma ban samu na kira shi ba, abin yana raina matuka amma yawan karatun dake gabana kuma bai barni na bi ba’asin long unusual silence dinnasa ba”. Irin kukan da Hasinah ke yi har zuwa lokacin yayi matukar daga hankalin Murja, duk kuwa da cewa Hasinah ta rage karfinsa sai sheshsheka da jan majina, maraicinta da rashin gatanta in babu su a tare da ita, ya fito karara ta cikinsa. Kamar ance karshenta yazo ne, idan Prince AbdulRasheed ya juya mata baya. Kamar zautatta sabon kamu haka sai ta hau sakin zance a kunnen Taiwo. Ni Hasinah da ba Uwa ba Uba ba dangi, ba asali ba nasaba ba tushe, sai Abdulrasheed da Taiwo dinsa, da suka karbeni a hakana, duk da rashin asalin nawa. I was ungrateful, selfish and greedy. Shine komai nawa, my life support and also a guardian, idan ya bar ni a dalilin kuskurena ina zan koma yanzu a karbeni banda GIDAN MARAYUN AMBURSA? Zancen zucinta kenan da har bata san yaushe ya fito ya subuce daga bakinta yake shiga kunnen Taiwo ba. Taiwo ta tabbatar al’amarin da ya saka Hasinah mai soyayyen idanu kuka da nadama irin haka akan AbdulRasheed, harta zauce haka, wanda kusan a baya sai abinda tace masa yake yi, saurayin kan-tace ne Abdul. Abdulrasheed din da ransa ne kawai bai fitar ya baima Hasinah ba don SO na gaskiya, ko meye wannan laifin zai kasance ba karamin laifi bane tayi masa da bazai iya yafewa ba. A takaice zamu ce Taiwo tafi kowa sanin irin son da Abdulrasheed ke yiwa Hasinah sabida itace confidant dinsa. Don haka ta katse wayarta da Hasinah ta dauko komatsanta ta fito daga motar zuwa ciki, tana shiga gida bata nemi su Kiki ba, da mai rainonta Bunmi, ta tadda babban danta Hakeem yayi dai-dai yana barci a falo, da alama ya kwaso gajiyar makaranta ne, a gigice take sosai da lamarin nasu, don haka sai ta wuce dakin barcinta kai tsaye ta rufo kofa jikake bamm! Kafin daga bisani ta zauna a bakin gado, tana warware mayafin laffayar jikinta, sannan ta ciro wayarta da gaggawa ta kira dan uwan nata. Wayar ta jima tana ringing har saida ta katse kanta, akalla Murjanatu ta kira ta kara kira ya kai sau uku kafin tayi sa’ar samun Prince ya daga, shima kuma ba tare da yace da ita komai ba. In da sabo ta saba da sarautarsa da ginshirarsa. Amma yau bayan jan aji na sarauta da ginshirar ma tabbas akwai wani abun. Tunda akalla duk jan ajinsa shi zai fara gaisheta. An dauki lokaci tana maimaita masa sallama cikin kwantar da murya da nema masa sassauci, tareda nema masa amincin Ubangiji ta hanyar cikakkiyar sallama, har saida ta kai ga jawo masa Hadisin daya yi umarni da wajabcin amsa sallama ga musulmi da mafi kyawunta ko mayar da martini da makamanciyarta. Kafin ta samu Engnr. AbdulRasheed (Kehinde) Idris Akanni, ya amsa mata da kyar. Kuma ciki-ciki. Ta hanyar cewa; “Wa’alaykumussalam-warahmatullah”. Bayan haka sai bai kara cewa ko uffan ba. Wannan wani abu ne weird daga Abdulrasheed zuwa gareta a wurin Murjanatu-Taiwo. Ko Prince zai ma kowa kyaliya irin wadda ya saba yiwa wanda ya bashi haushi banda ita Taiwo dinsa, amma me? He has his reason. Wato tuni ya riga ya san zancen da Taiwo tazo zata yi masa, bana komai bane na ‘yar dakinta Hasinah ne, ya riga ya san yadda soyayyarsa da Hasinah ta assasa aminci mai girma tsakaninta da ‘yar uwar tagwaitakarsa, Taiwo, sanadin zamanta tare da ita na wasu shekaru tana karatu a hannunta. Ya riga ya kwana da sanin cewa ta kanta Hasinah zata fara bi, da sunan a sulhuntasu, a bashi hakuri ko a lallashe shi. Yau ba Taiwo ba ko lallashin Nenne ne bazai ji ba, in dai akan matsiyaciya Hasinah ne. “Let her GO please! I will take her back to where I adopted her!”. Cikin murya ta lallashi da nuna kauna, irin tasu ta ‘yan biyun Nenne Sappa da kowa ya sani, wadanda ko a cikin tagwayen duniya ba
🏠