in maganar ma sai ciza lebe. Aunty Taiwo ta sake cewa “In ji dai lafiya kuke keda shi? I mean Prince din? Kuma yaya kuke coping da wheather din sanyinnan na winter da karatun naku ke da shi?”
Amma ga mamakinta sai taji kamar Hasinah sheshshekar kuka take yi. Kukan ma irin na fitar rai da ta kasa dannewa, irin mai cin zuciyar mai yinsa, da dugunzuma zuciyar wanda ake yimawa.
Murjanatu was shocked! Stunned daga zaunen da take a cikin mota, duk da ta kashe motar a ma’adaninta kukan Haseenah yasa ta kasa fitowa kuma.
Da kyar taji muryar Haseenah na fita zuwa cikin kunnenta, cikin sauti mai nuna matsananciyar nadama.
“Ki taimakeni ki bashi hakuri Aunty Taiwo, kaddara ce!!!”
Murjanatu ta zaro ido, kafin tace komai Haseenah ta sake cewa “kema kin san ba halina bane, kullum kina gargadina akan hakan, kuma na dade ina kiyayewa, kun sani lafiya kuka dauko ni a ‘virgin’ daga Ambursa, wallahi kafin na zo school ban taba yi ba, sau daya ne, sai wannan na biyu, shima kuma wallahi da kudi Tokumbo yake jan ra’ayi na, na dade ina kaucewa fitinarsa, wannnan din ma akasi aka samu, tsautsayi ne.
Nayi masa babban laifi Aunty Taiwo, kaddara ce ta fada mini.
Zina ba hali bace afkawar kaddara ce da karfin sha’awar da ya gagari dan adam.
Prince ya daina daga wayata yau kwana biyu kenan…. ya min iyaka da zuwa gidansa…. Ya ce kada in kara nuna masa mummunar fuskata ko a lahira!
Laifina bai kai haka ba. I didn’t deserve such a severe punishment, zan jure kowanne hukunci banda na rabuwa da Prince. Na shiga uku Aunty Taiwo, yau kwana biyu ban saka Prince a idanuna ba…
I am dying without him! Truly I am dying! Aunty Taiwo ki taimakeni! Ki cece ni ki ceci marainiya, ke kadai nake da yanzu, a duniya banda kamar ki, ki ceci soyayyar gaskiya da Prince yake yi mun, nasan Tokumbo ba aurena zai yi ba ya cuce ni ne kawai!”. (She screamed!!!). Irin ihunnan na girgiza zuciyar uwardaki. Har cikin kwakwalwar Murjanatu ihun nata ya ratsa ya kusa kurumta kunnuwan Murjanatu.
Ta shiga afi da hurwa, tana tumami a kasa cikin hawaye da majina, kamar Murjanatu na kallonta, kalamai take na tuba da nuna nadama, amsar kaicon kai, da kuma daukar alkawarin bazata sake ba. Begging for “one more last chance”.
Amma taki fadin hakikanin laifin nata, cikin matsanancin kuka na tashin hankali kawai take rokon Taiwo kamar itace Prince AbdulRasheed din da kansa.
Ta kwana da sanin idan Aunty Murjanatu ta yafe mata, tamkar Abdulrasheed da kansa ya yafe mata ne.
Kasancewar kowa dake tare dasu ya san Prince (AbdulRasheed) bai iya tsallake rarrashin Taiwo dinsa. Kamar yadda bai iya tsallake abinda ta umarceshi inta bullo masa da lallashi da banbaki ta bayan gida wanda ita kadai ta san lagonsa.
Amma itama Hasinah duk da wannan tabbacin data ke dashi, ita da kanta wannan karon tana shakka.
Ta yaya take da tabbacin laifin nata mai yafuwa ne ga Taiwo dinma? Since they sometimes share the same feelings itada kaninta Prince? Akan-karan kanta ta san laifinta ba mai yafuwa bane saboda girmansa. Musamman ga babban mutum, mai kishin kansa, dan babban gida da yasan ciwon kansa kamar PRINCE ABDULRASHEED.
Wannan shine babban tashin hankalin Hasinah Bello, idan ta tuna lokaci yazo da Prince da zai barta (lokacin rabuwa da gatanta Prince Abdulrasheed yazo) ko taki ko ta so, duka wannan ihu ne take yi bayan hari Abdulrasheed bazai taba mantawa ba balle ya yafe mata, wanda shine komai nata kuma masoyin da suka kulla alkawurran soyayyar da bazasu lissafu ba, soyayya mai tsabta wadda ikon Allah ce kadai ta wanzar da ita don ta san bata kai nan ba, bata is aba, bata kai matsayin ba. Haba! Wannan tunanin yasa sai ihunta ya ninka na baya.
Ta kuma kasa ambaton sunan Allah don tasan shima Ubangiji bata da uzuri a wurinsa don bata yi godiya da ni’imar da yayi mata ba ta bata sahihiyar soyayyar Abdulrasheed ba don isarta ba.
Bata taba tunanin akwai abinda zai iya yin sanadin da Prince zai ce mata “You! The bastard WHORE! Don’t dare show me your ugly face again!!!”.
Wadannan sune kalaman Prince na karshe a gareta, mafiya daga hankalinta, domin a sanda ya fadesu ta tabbata ya fadesu ne baka da zuci babu wata rana da zaiyi nadamar furtasu.
Tunda abinda yayi Kehinde shi yayi Taiwo. And they often share the same feelings, kowa nasu ya san hakan. To idan har Aunty Taiwo ta ji laifinnata ma, anya zata kara kallonta da idanun rahma? Ko dubanta da aminci da kaunar da take mata wanda duk sanadin Prince dinne???
Kowa bai ishi Murjanatu kallo ba, in dai baida sarauta, mulki ko dukiya, itama din albarkacin Prince ta ci hawa-hawa a wurinta tunda har ta riketa na shekaru a hannunta, sai kuma jininsu yazo ya hadu daga bisani saboda dukkansu halayensu yazo daya masu son rayuwa ne sosai.
Wannan tunani ya kara dugunzuma zuciyar Hasinah, ta kara kururuta kukan da take yima Dr. Taiwo a waya kamar zata fasa dodon kunnenta, fatan ta dai Murjanatu taji tausayin