NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 43 of 44

Sappa tayi masa sai ya kasa cewa kai tsaye bazai bayar ba, yasa habar taguwarsa yana share zufa daga goshin sa daya tuno irin soyayya da shaquwar dake tsakanin Ishaq da Aisha, ya kauda idonsa daga kwarjinin Nenne yana fadin “akwai wanda ke neman aurenta tun tana kankanuwa, amma ban tari hanzarin ki ba inna tambayi cewa shi Abdulrasheed dinne ya ga Aisha yace yana so? Ko kuwa shi Abdulrasheed ne yace a nemo masa matar aure? Ke kuma hakannan kika ga dacewar zaba masa Aisha-Siddiqarmu? Nenne Sappa ta saka habar mayafinta tana share hawayen da suka kawo mata a idon ta, ta kwashe labarin su kaf ta baiwa Malam Yunus, da yawan shekarun AbdulRasheed a duniya amma bai taba aure ba. A karshe ta gaya masa halin tsangwamar da take fuskanta daga dangin mijinta akan rashin auren Prince, kowa ya bude baki laifinta yake gani, sabida mijinta baya son laifinta, da yadda take raba dare bata barci saboda damuwa da addu’ar Allah ya yanke masa, in yana da rabon aure a rayuwarsa Allah ya nuna mata, don ita bata yarda da wai aljana ta aure shi ba, tafi yarda in za’a ce yawan sabgogin Polo da ya saka a gabansa ne suka cire masa tunani da sha’awar aure kwatakwata. Har mafarkin fuskar Petel data sha yi sai da ta gaya masa a duk ranar data yi istikhara, Malam Yunus ya tausaya ma damuwar da Nenne ke ciki akan dan nata, ya kuma dan tsorata duk da bai gaya mata ba, shima fa yanata mafarkin mutum akan doki a ‘yan kwanakinnan, gashi tace dan nata mai hawa Doki ne. Nenne Sappa ta katse masa tunani da cewa, “na yarda Ubangiji ya aiko ni Gombe ne wannan karon don lokacin da nake ta addu’ar zuwan sa ya zo ga AbdulRasheed, kada ka juyawa wannan alkhairin da nake nufin mu kulla nida ku baya. Ka yiwa Allah malam Yunus mu taru mu taimaki juna ta hanyar kulla aure mai albarka tsakanin ‘ya’yanmu. Wanda zai mikar da zumunci na daku har illa ma sha Allahu. Na amince daku dari bisa dari ba tun yau ba, haka na amince da Siddiqah ce kadai zata zama surukata a cikin duk matan dake garinnan, da wadanda ke garinsu mijina (Ilorin) dama kasar Najeriya gabadaya Siddiqah nake fata da addu’ar ta zame min suruka. Malam Yunus ya nisa, duk da yayi na’am da komai da Haj. Sappa ke furtawa amma yace tayi hakuri, ba zai yi gaggawar amsawa ba sai yayi shawara da na gaba da shi, kuma sai ya san hakikanin abinda ya hana Abdulrasheed yin aure har zuwa wannan lokacin sannan zai yarda ya bashi Aisha, shima kuma sai idan Ishaq bai tashi aure yanzu ba. Yace ya gaji da yawan maneman auren Aisha, kullum masu zuwa yau daban dana gobe, yace gara ya aurar da ita haka ya huta, kowa ya huta, dama bai mata alkawarin samun ilmin gaba da sakandire ba. Amma shi baya ra’ayin karatun boko mai zurfi sam a gareta. Burinsa shine tayi aure da wuri ta haifa masa jikokin da zai kalla a matsayin ‘ya’yan da shi Allah bai yi nasa sun zauna a raye ba, don mahaifiyarta ma iyakacin ta firamare ya aure ta. A karshe yace ya ji bukatar ta na son tafiya da Aisha taga likitan Asthma, sai kuma yace bai yarda ta zauna a Lagos har sai hutu ya kare ba, saboda tana zuwa Tahfiz yin haddar Al’qur’ani a kowanne hutu anan kusa dasu a unguwar Dawaki, da ta gama ganin likitan don Allah a dawo da ita gida ta karasa hutunta tare da su don suma sun jima basa tare da ita tun tafiyarsu aikin Hajji. Nenne Sappa tayi ta mamakin wannan soyayya ta iyayen Aisha ga diyarsu Aisha, ta dauka Haj. Zainab ce kawai ke mummuken Siddiqah ahe har baban nata, ta amince da yadda Malam Yunus ya zaba cewa Aisha zata yi sati daya a Lagos ta dawo musu da ita gida. Malam Yunus ya bukaci sanin waye mahaifin AbdulRasheed da kuma asalin ita Nenne anan Gombe. Nenne ta bashi damar yayi duk wani bincike da addini ya bashi dama akan Prince AbdulRasheed dasu iyayensa. Sun rabu akan cewa zai yi bincike zai kuma yi shawara da maidakinsa da Yayansa, sannan zai sa Zainaba ta sanar da ita abinda suka hadu suka yanke. An samu shawo kan Aisha da kyar da sudin ludayi ta yarda zata bi Hajiya Sappa Lagos bayan ta ci kuka ta koshi ta gode Allah a toilet don kada Hajiya Sappa ta ga kukanta, wai sati guda! Sati guda babu Umma yaya rayuwa zata yi dadi ga PETEL?! Sati gudan da a cikinsa dukkkan kundin kaddarar rayuwar Aisha take, tareda dan kabilar Yarbawa. Nenne da Aisha suka kama hanyar Lagos ta jirgin sama, domin daga Gombe kai tsaye suka tashi a jirgin Azman mai zuwa Ikko. **** ***** **** MURFIN LITTAFI NA DAYA Ga dai Aisha-Siddiqah a hanyar zuwa Lagos gidansu Prince ABDULRASHEED IDRIS (KEHINDE) AKANNI, gidan da ga dukkan alamu zai zame mata fadar rayuwar aure da surukuntaka, ga dai Aisha da Prince (Fullatana da Bayarabe) na shirin zama mata da miji kamar yadda manyan alamu suka nuna, alhalin Aisha ga hasashenta da alkiblarta da take-takenta akan kabilar Yarbawa. Mu biyo Siddiqah Petel ‘yar Ummanta, don jin cikakken labarinta, yadda zata kaya tsakanin ta da Polo Leg
🏠