i irin wadda suka dade basu sha ba. Kafin ya gaya mata maqasudin abinda yasa shi kiran da yayi mata, wanda dama ta tsammace shi tun ma kafin ta ji shi. Maganar dai guda day ace. Gabadaya danginta da iyayenta da dangin mahaifinsa da nasa mahaifin basu da damuwa yanzu sai ta auren Prince.
“Ki turo AbdulRasheed ya zo ya ga ‘yar uwarsa Naziha, malaman fada sun gayamin idan har ba auren muka yi masa da kanmu ba, a haka zai kare rayuwarsa bazai taba kawo mace yace yana so ba don sunce aljana ta aure shi.
Sannan ance dani akwai aguminsu na maketan Yarbawa makiya Kakansa, akwai kuma sihiri irinna magauta gidansu duk a jikin sa, bazai taba ganin mace yace yana so ya aura ba”.
Nenne tayi ajiyar zuciya cikin damuwa, bata son irin wannan false beliefs din ita sam, gasgata malaman tsubbu da Yayanta Uban kasa ke yi a rayuwarsa yana damunta, ita tafi yarda da cewa auren Abdulrasheed LOKACI ne bai yi ba, kuma koda yayi din, duk da za’a kira shi ‘LATE MARRIAGE’ tofa ba zai wanke masa tarihin cewa ya jima bai yi aure ba, don haka ba kowacce mace zata yarda ya aura ba musamman cikin ‘ya’yan ‘yan uwa don kada abata zumunci in ya jingine musu ‘ya’ya saboda Polo.
Ta rasa abinda zata ce da Uban kasa, a karshe ta samu bakinta yana bashi hakuri, tana fadin ta yi wa AbdulRasheed mata, kuma anan Gombe, sannan cikakkar bafullatana diyar dattijai. In sha Allahu data koma Lagos zata gabatar da maganar ga mahaifinsa.
Uban kasa bai ce a’a ba, duk da yafi matukar son Abdulrasheed yayi aure a cikin gidansa, saidai ya nemi jin su waye iyayen yarinyar data ke ikirarin ta samar masa ta kuma fada masa, yace zai yi bincike akan Malam Yunus din da sana’arsa da gaggawa.
Ba’a kwana ba, ba’a yini ba saida komai na Malam Yunus ma’aikacin hukumar Alhazai tsohon malamin federal government na jihar Gombe ya zo kunnen Uban kasa har asalinsa, duk wata shaidar arziki da kyakkyawar nasaba malam Yunus Hamza da maidakinsa Haj. Zainab Hamza sun gama samun ta a unguwarsu Jeka da fari.
Sunyi waya da Haj. Zainab a ranar da zata wuce Lagos bayan an sallamesu daga FMC cewa tana tafe a hanya zuwa gidan Malam Yunus.
Yau ko fita Abba bai yi ba, yana jiran zuwan Haj. Zainab. Bakuwar da matarsa take ambata da alkhairi kamar tafi kowa kirki da darajta dan adam a duniya.
Nenne ta iso wajejen karfe goma na safe don taredasu ma ta karya kumallo da kunun gyada da kosai mai zafi a falon Haj. Zainab.
Aisha na daki tana ta kumburi, Ummah tace wai zata bi kawarta Lagos tayi hutu kuma taga likita.
Tunda Aisha take a duniya bata taba barin garin Gombe ba, kai ko Azare bata taba shiga ba banda Billiri makaranta, balle akai ga kwana da wani wuri da ba makaranta ko dakin ta ko na Ummanta ba.
Aisha akwai makon UWA, irin yaran nan ne da gasu dai sun girma, amma kamar yaran goye suke agaban iyayensu mata, ko kusa bata son gusawa daga jikin Ummanta.
Amma yanzu maganar zata je tayi sati biyu a Lagos ake yi. Tun jiya da taki hada kayanta Umma da kanta ta hada mata. Tana ta lallashin ta da cewa Haj. Zainab bazata roki alfarma ta kasa yi mata ba. Kuma dai lafiyarta ake son ingantawa.
Budar bakin Aisha sai cewa tayi (cikin alamu na karyewar zuciya da damuwar cewa yau Umma tace zata tafi wani gari ta kwana ba tare da ita ba).
“Amma dai Umma kinsan ba yau na fara ciwona ba ko, wane irin likita ne ban gani ba? Kuma Umma kin dai san Asthma bata da wani magani bayan inhaler ta da wadanda nake sha yanzu ko?”
Umma ta girgiza kai itama ranta a dame da damuwar Aisha tace “babu ciwon da bashi da magani sai tsufa sai mutuwa kinji ko Petel, shi magani dace ne, shin Siddiqah in baki koyi shiga mutane yanzu ba sai yaushe ne?
Ko wajen yan uwana ko na Abban ki ba kya yarda ki je ki kwana, kada ki manta watarana aure ne zai raba mu gabadaya”.
Ai kuwa Aisha ta balle da kuka tana fadin “Umma in kika sake cewa zamu rabu in nayi aure to bazan yi auren ba har abada”.
Umma na dariya tace “to ai Ishaq din bazai yarda ya daukemu mu biyu ba, mun yi yawa a gidan Ishaqa”.
Aisha ta hau rantsuwa, kan cewa sun dade suna kulla alkawari itada Ishaq cewa in yayi kudi ya tashi ginin gida zai ginawa Umma daki a gidan sa, in ba haka ba bazata yi auren ba”.
Umma abin ya bata dariya sosai, da yake lallabata take don ta yarda ta bi Hajiya Sappa sai tace toh ya isa haka ta ji, ta kuma amince ita din itace ‘yar zaman dakin Petel (Siddiqah)”.
Suna daki suna dambarwa ita da Aishah Haj. Zainab na can gaban Malam Yunus a falonsa tana gabatar masa da uzurinta na nemawa tilon dan ta wanda a cewarta ya manyanta auren Aisha-Siddiqah daga mahaifin ta Malam Yunusa Hamza.
Tace masa in ya amince da ta koma Lagos zata sanar da mahaifin Abdulrasheed, cewa tayi masa matar aure a Gombe, ba jimawa iyayen Abdulrasheed maza zasu zo da komai na dukiyar aure, basa bukatar komai, amarya kawai za’a basu su dauka.
Malam Yunus ya hau zufa nan take, sabida kwarjinin da Nenne