NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 41 of 44

fadi aranta “ba inda zata iya bari Petel taje inba cikin dakinta ba, in ka san soyayya ta rabin rai ta Aisha-Siddiqah da Ummanta ne”. Mintuna ashirin ta kawo su har kofar dakin da Aisha Siddiqah take kwance, sai Nenne ta kira Haj. Zainab ta sanar da ita suna bakin kofa. Hajiya Zainab ta fito ta yiwa Nenne jagora zuwa cikin dakin har gaban gadon Aisha-Siddiqah. Wanda daki ne na mutum daya (sideroom) a sashen kwanciya na bangaren mata. Nenne ta sa kai a dakin bakita dauke da sallama. Kallo daya Nenne Sappah ta yiwa “AISHA-SIDDIQAH YUNUS” dake kishingide a gadon marassa lafiya da karin ruwa a hannun ta taji wani bakon yanayi a tare da ita. Idanun Nenne basu sauka a ko’ina ba sai akan warawaran zinaren dake hannun ta wadanda suka kawata halittar fatar hannunta fara sol. Ga yarinyar ‘yar karama da ita (mai karamin ruwa) wato irin amsu karamin jikin nan ce siririya sosai kamar in ta sunkuya karyewa zata yi. Idanunta kamar na kwan zabo, masu haske da kyau. Nenne tayi birki a gaban gadon Siddiqah ta kama hannunta mara allurar a jiki tana kallonta da murmushi, Siddiqah wadda ke kishingide akan filo, rike da dan littafin addu’o’I na hisnul muslim a hannunta ta daga fararen idanunta a hankali tana kallon Nenne Sappa. Umma bata lura da yanayin kallon kaunar uwa da Haj. Sappa ta fada akan Siddiqah ba, tana ta faman lale-maraba da Hajiyar Lagos, (jabbama-jabbama), ta bata farar kujerar roba ta ‘yan dubiya don ta zauna amma ina! Hankalin Nenne Sappa ya tafi ga wani tunani daban. Ya bar jikin ta gabadaya. Domin dai yau ji take a jikin ta ga uwar jikokin ta, wato ga matar Prince Abdulrasheed Kehinde Idris Akanni, yau Allah ya nuna mata da sauran numfashinta, wadda ta dade tana ganin surarta a cikin mafarki duk ranar data yi istikhara akan sha’anin auren Prince Kehinde. Ta dade, ta jima tana ganin wannan kyakkyawar fuskar a cikin barcin ta, bata taba sanin alaqar yarinyar da mafarkan istikhararta ba. Taji a ranta bata iya barin Gombe ba tareda Aisha-Siddiqah ba. Lokacin da Aisha-Siddiqah ta bude baki tana gaida Nenne da sassanyar muryarta ta mai jinya Nenne kasa amasawa tayi, domin Aisha da komai nata ya shiga ran Nenne farat daya (daga gani na farko). Ji tayi kamar ta sace ta kawai ta gudu da ita Ikko, in yaso ta aurawa Prince Abdulrasheed Kehinde. Ta san dai ko zaiki kowacce mace banda wannan kyakkyawar halittar dake gabanta. Da kyar ta iya amsa gaisuwar Siddiqah da wani kyakkyawan (maternal feeling) akan fuskarta. Kafin su zauna su bude babin hirar Saudiyyah tsakanin Hajiyar Lagos da kawarta Hajiya Zainab irinta wadanda suka aminta da juna, tabbas kawancensu hadin Allah ne kawai, domin ajin rayuwarsu ko kusa ba daya bane. Allah shi yake hada mutum da mutum su kaunaci juna saboda Allah. Nenne tace da Haj. Zainab ta nema mata iznin Baban Aisha tana so ta tafi da ita Lagos taga likitansu Firdausi, kwararre ne sosai akan lalurar huhu da numfashi, wanda shi yake duba Princess Firdausi (itama asthmatic ce), daga nan tana so Aisha ta karasa hutun wannan zangon a hannun ta. Hajiya Zainab tayi dan jimmm! Kafin tace “Babanta yana wajen aikinsa amma na san ba zai ki baki Petel ba, don ba tun yau yake da labarinki ba, zan masa bayani idan ya dawo kafin ki gama abinda ya kawo ki Gombe, kwarai nice dai zanyi kewarta, don bama raba gari tun haihuwarta sai da ta fara makaranta a Billiri. Akwai yaron da ke rikon neman aurenta Ishaqa dan makwabtanmu, yana jami’a a Ibadan, yanada da hakki shima a sanar dashi kafin ku tafi din”. Nenne tace cikin jin faduwar gaban ta sameta a take “an yi musu baiko ne?” Kafin Haj. Zainab ta bata amsa Nenne ta kira sunan Allah sau ba adadi tana neman daukinsa akan Allah yasa Aisha rabon su ce. Wani ikon Allah sai Haj. Zaina tace “A’ah tukunna, Ishaqa dalibi ne a jami’a, mahaifinsa yace sai ya kammala ya fara aiki koda zai masa aure, suna dai matukar kaunar juna shi da Petel kowa ya sani, sabida shi Aisha bata sauraron kowa. Gida biyu ne a tsakanin mu dasu, tare suka taso tun suna kanana soyayyar ba ta yau bace, kuma dai Ishaq yana da hankali da nasaba mai kyau, ya dade yana hidima da ita don haka dukkanmu mun yi na’am da shi tuntuni sai fatan Allah ya nuna mana lokacin”. Aisha na jin su, kunya kamar tayi yaya! Sai ‘yan mutsu-mutsu take kamar tace kasar ta tsage ta shige. A karshe Haj. Zainab da Haj. Sappa sunyi sallama kan sai jibi zata zo ta gana da Baban Aisha, in ya amince ta wuce da ita Lagos ganin kwararren likitan numfashi da huhu. Da Nenne zata tafi ne ta matsa gaban gadon Siddiqah. Tana murmushi tasa hannu ta shafa gashin kanta cike da damuwar ganin yadda take ta kokawa da inhaler ita kadai, tace “get well soon my dear, Allah ya baki lafiya kinji ko Siddiqah? Sai na dawo”. Har bakin mota Haj. Zainab ta raka Nenne. Suka sake kafa sabuwar hira kafin suyi sallama da kyar. Nenne Sappa ta samu dan uwanta Uban kasar Gombe da iyalinsa lafiya, suka sha hirar zumunc
🏠