Basarake. Sannan kuma bafullatanar Gombe ce itama.
Aisha ta koyi wasu abubuwa guda biyu cikin labarinnan da Ummanta ta gama bata yanzu, wato “gaskiya da amana su ke sawa a so mutum!” tace a ranta “na shaida Ummana mai gaskiyace, amana da rashin kwadayi halin Umma na ne, nima daga yau zan koye su don kowa ya so ni.
A karshe hirarsu Aisha ta yarda idan ka rike gaskiya, amana da rashin kwadayi suka zama symbol dinka watarana zasu samo maka abinda baka taba zaton samu a rayuwarka ba, da kauna da amincewar mutanen da kake zagaye dasu”.
A yinin ranar bakidaya har dare labarin da suke yi kenan itada Umma wato na Hajiyar Lagos, tsakanin Aisha da Ummanta aka rasa wanda yafi wani dokin son sake haduwa da Nenne Sappa, Aisha ta ji itama tana son matar har cikin ranta duk da kuwa labarin kirkinta kawai Umma ta bata.
Kwanan Aisha-Siddiqah uku da dawowa hutu Asthma dinta ya tashi haikan, tun asali (she’s asthmatic) wato mai fama da ciwon Asthma ce (mild asthma) da sai ta dade bata motsa ba. Wannan karon tashin da yayi yafi karfin a kwantar dashi da (inhaler) dinta don a karshe har sai da ta kai su ga kwanciya hajaran majaran a babban asibitin Gombe wato (FMC Gombe) ake ta treating Aisha.
**** **** ****
Maimartaba Uban Kasar Gombe wato Yayan Nenne (Sarkin Gombe na lokacin) ya aika mata sammacin kira yana son ganawa da ita a gida Gombe, ido da ido, ba maganar waya bace. A ganin Uban kasa har da daurin gindinta a rashin auren da Prince Abdulrasheed ya ki yi har shekarun kuruciya suka fice masa, domin in tayi masa umarni a matsayin ta na uwa in har yana son albarka dole yayi ko yana so ko baya so. Ya gaji da maganganu akan Abdulrasheed, ko’ina ka shiga sunan Abdulrasheed Idrees Akanni ne a bakin samari ‘yan bana bakwai a kasar Najeriya, har wani lakabi suke binsa da shi “The Latest Yoruba Demon (Prince). Ita kuwa Nenne ta fannin ta Allah ya gani bata san ya zata yi da Abdulrasheed ba kuma, tunda har hawayenta ta zubar masa, hakan kuma bai sa ya amsa cewa ya yarda zai yi aure ba. Iyayensa maza ma sunyi iya bakin kokarinsu duk a banza, bai amsa musu da komaiba har gobe, bazata dorawa kanta ciwon da baida magani ba akan abinda bata da maganinsa. Duk da cewa tafi kowa damuwa da al’amarin idan ta tuna yawan shekarun Abdulrasheed na yanzu. Watakila baida rabon auren ne a gidan duniya, in haka ne tana masa fatan samun masu albarka a lahira, ba kowa ke samun rabon aure a rayuwarsa ba, ta yarda da danta dari bisa dari ba lalata ce ta hana shi aure ba. amma mafarkin data ke ta yi a ‘yan kwanakinnan fa?
Don haka Nenne ta taho Gombe ranar wata Lahadi da nufin zata yi kwana uku a gida, ta ga ‘yan uwa da dangi ta kuma gana da dan uwanta Uban kasa da ya kira ta officially, don ta jima rabonta da Gombe, ko bai kirata ba tayi niyyar zuwa a wannan watan.
Nenne na shigowa garin Gombe tana kwance a bayan mota ‘Ford’ direba na sharara gudu da ita, babu wanda ya fado mata a rai sai kawarta ta filin Arfah da Filin Munnah wato Haj. Zainab Yunus.
Don haka ta yunkura tun a cikin motar kafin su isa fadar Gombe, ta dubi direban Uban Kasa daya daukota dake ta aikin sa na tuki tace “tsaya a gefen titi!”, sannan ta ciro wayarta a jaka ta kira layin Haj. Zainab da tayi saving da (Zaynaba mai gaskiya).
Haj. Zainab na dagawa da sallama taji muryar Haj. Sappan Lagos kamar a mafarki, tana fadin “Zaynaba gani a Gombe, maza turomin adireshin ki, in fara tsayawa wajenku yanzu in ga Aisha-Siddiqah kafin na isa cikin gida in kasa samun lokacin sake fitowa kuma”. Ta kara da cewa “ina fatan na sameku lafiya cikin alkhairi keda malam Yunus da diyata Petel Siddiqah?”.
Haj. Zainab cikin ‘yar damuwa take amma kuma taji dadin ji daga Nenne Sappa ta ce “barka da zuwa Haj. Sappa, Jabbama-jabbama da Hajiyar Lagos maraba da isowa gida jewel in the savannah (Gombe kenan) inji ‘yan boko” duk suka yi dariya.
“Sai dai kash! Bama gida, kin ganmu nan a FMC tareda Petel din babu lafiya, asthma dinta ya tashi, tashin da ya jima bai yi irin sa ba.
Ina cikin damuwa da asmar nan tata Haj. Sappa domin Siddiqah itace ‘ya ta goma sha daya dana samu a duniya kafin Allah ya bar min, ban sani ba ko itama a shekarun girma Allah bazai bar min ita ba”.
“Ashsha Zaynaba, daina fadin haka, da yardarm Allah Petel zata ji sauki, kada ki girgiza imaninki akan ciwon ’ya’ya, ciwo ba mutuwa bane kin ji? Diyata Firdausi ma tana da (brittle asthma) haka muke ta fama. Allah zai bata lafiya da yardarSa”.
“Nagode da karfafawa Hajiya Sappa kuma ma dai yau din alhamdulillahi tana warwarewa ba kamar jiya ba, don har ta karbi shayi ta sha sosai”.
Nenne ta ce “to bari kawai in karaso asibitin in sameku can, ai bani ita zakiyi in tafi da ita Lagos kawai ko na sati biyu ne taga likitan Firdausi, tunda an yi hutun makaranta, Dr. Femi ya kware sosai akan treating asthma”. Umman Siddiqah ta kwatanta mata inda zata same su a female ward. Tana