) kuma yanada matsayi mai girma a cikinta.
Don haka Toufeeq ba mazaunin gida Nigeria bane sosai. Karin dalilin da yasa Taiwo tayi amfani da damar wajen yin karatunta cikin nutsuwa a Ilorin, wanda ta tabbatar zai amfanar da al’ummar kasarta musamman mata ‘yan uwanta (Obstetrics & Gynaecology).
Babban burinta mata su amfana daga ilmin likitancin data wahala tayi, a Public University ta Ilorin.
Ta fara karatun ne da farko saboda rashin Taofeeq a kusa, madadin tayi ta zaman gida miji baya kusa, don a kalla Toufeeq sai yayi watanni uku ba tare da ya leko su ba ko meyasa? Nenne kance ita bazata iya zaman da Murjanatu ke yi ba na bin miji agindi-agindi akai-akai. Don itace tafi zuwa masa da yaran lokaci-lokaci inda yake, in ta samu hutu, wanda shi bai cika son haka ba. Toufeeq yafi son su zauna a gida inyaso duk sanda ya samu sarari shi ya zo, amma Aunty Murja bata yarda sai taje.
Kenan zamu iya cewa Dr. Murjanatu da aka fi sani da (Taiwo), tana karatun aikin likita ne ba don albashin da zata samu ba, sai don dalilai guda biyu; debe kewar mijinta tun na auren saurayi da budurwa hutsun bature Dr. Toufeeq Adam Adebayo, da kuma burinta na amfanar da al’ummar kasar ta, musamman mata.
Hassana (Taiwo da harshen Yoruba) wadda ainahin sunan ta na yanka (Murjanatu) da Hussaininta Prince Abdulrasheed (Kehinde da harshen Yoruba) tagwaye ne masu abin mamaki. Su din ‘yan biyu ne da aka haifa tare amma ta girmeshi da awanni biyu, suka kuma taso tare bisa doron tarbiyyar islama cikin shakuwa da kaunar juna mara misaltuwa, duk da kasancewarsu mace da namiji, sai suka maida kansu sune aminan junansu daga kuruciyarsu har girma basu da abokan shawarar da suka fi junansu.
Taiwo (Morjanatou), da dan uwanta Abdulrasheed (Prince) wasu irin twins ne kebabbu a cikin kafatanin zuri’arsu saboda sune manyan jikoki kowa na girmamasu, amma a halayya da dabi’a basu da alaqa da juna don Taiwo mai wasu baudaddun halaye ce, wanda iyayenta ne kadai da shi dan uwanta kadai suke iya gane inda ta dosa, sune kuma kadai suke iya tafiyar da ita da baudadden halinta, amma ko Toufeeq wani lokacin haurawa suke su fado kasa saboda bashi da hakurin jurewa halin Mourja.
Hadin kansu itada Prince shine kan gaba wajen nuna cewa su ‘yan biyu ne masu fahimtar juna, da tolerating each others’ attitude. Prince ne kadai in Taiwo tayi ba daidai ba zai zare ido ya gaya mata tayi ba daidai ba ba tare da yayi la’akari da girman awannin data bashi ba da cika idon ta ga al’umma, nan kusa babu irinsu a family dinsu ta fuskar closeness da sincerity ga juna.
Su haka su rufe su binne sirrin juna ba wanda ya ji ba wanda ya gani, don haka wajen hadin kai da kaunar junansu basu da na biyu. Zumuncinsu ga juna mai burgewa ne, ban sha’awa da ban kaye, in kai mai nazarin ilmin mu’amala da zamantakewa ne har kaso yin rubutu a kansu, domin kuwa zumuncin su ya zarta normal irin wanda ke tsakanin ‘yan biyu na ciki daya, wadanda akasari kusan koyaushe zaka samu suna against junansu, ko yiwa juna cin diddige wato suke yin rivalry da junansu. Su kam nasu zumuncin na musamman ne, a kullum AbdulRasheed da Murja cigaban juna da farin cikin juna suke hangowa junansu. Abin hannunsa nata ne da ‘ya’yanta.
A wasu lokutan har feelings na zukatan junansu suna iya ji a jikinsu, na farin ciki ko akasinsa, idan ya samu dayansu.
A takaice tagwaitakarsu extraordinary tagwaitaka ce ta bada labari da bugawa a jarida. A wancan lokacin da na waiwaya na hasko muku su (flashback), Hassana Murjanatou da Hussaininta Prince, sun mallaki shekarun matasa ne talatin da haihuwa tana housemanship dinta a Lagos State Teaching Hospital.
Ta iso gida kenan tana kokarin sanya motarta a ma’adanarta, wayar ta dake aje gefe ta hau ruri kiran Hasinahn Prince ya shigo mata. Da far’a sosai Aunty Murjanatu ta daga kiran Hasinah, duk kuwa da gajiyar dake tare da ita, ta kwana biyu bata ji ta ba dama, don kusan kullum sai sunyi waya tun barinta gidanta da fara karatun Digirinta a kusa dashi a birnin Tokyo.
Taiwo ta daga wayar Hasinah (fiancée din Prince) tana tsokanarta da waka cikin yarbanci yadda ta saba koyaushe sukayi waya.
“Hasinah ta Prince, Hasinah kanwar Taiwo, Hasinan Taiwo & Kehinde, ta Abdulrasheed PRINCE bada kanki a sare kije gida kawai kice ya fadi!”.
A baya a duk lokacin da take mata irin wannan wakar mai kama da kirari kan Hasinah kumbura yake yi tayi ta blushing ita kadai kamar Aunty Taiwo na kallon ta, domin hakika tana jin dadin wakar gtana alfahari kwarai da son da Aunty Murja ke mata, amma a yau sabanin kullum sai tayi shiru tana kakarin magana amma maganar taki fita daga makogaronta tiryan-tiryan. Murjanatu ta fakamota ta kashe sai ta zauna a ciki ba tareda ta fito ba, ta ce.
“Yaya akayi ne kanwata nake jin muryar ki a shaqe kamar mai fama da mura? Kin fadar min da gaba. Kwana biyunnan ban jiki ba dama, Dear Haseenah in ce ko lafiya?”
Shiru Hasinah tayi bata ce komai ba ta daina kakar