afin dan lokaci kakkarfan kawance ya kullu tsakanin matan biyu a aikin Hajjin bana.
Sati daya bayan nan Alhazai suka soma shirin komawa gida.
Ranar Asabar Nenne da Princess Firdausi suka koma gida Lagos. Yayinda Haj. Zainab jirgin kusan karshe suka bi suka koma gida Gombe don saida aka gama kwashe ‘yan jihar su kaf.
**** **** ****
Tunda Haj Zainab ta koma Gombe Kusan kullum sai ta baiwa Maigidanta Mal. Yunus labarin kawarta mai karamci Hajiya Sappa ta Lagos da suka hadu a Minnah, kawar da tayiwa Petel dinta kyautar warawaran zinare ta yaya zata manta ta?
In ana haddace labarin mutanen kirki Malam Yunus ya dade da haddace wannan labarin na Haj. Sappa daga bakin matarsa. Shima kuma ya yaba da kirkin nata duk da bai ganta ba. Domin ya san matarsa sarai shishshigi gun masu kudi ko dukiya ba halinta bane, sannan ya shaideta kan ita din ba mai kwadayi bace, kuma mai wadatar zuci ce. Allah – Allah take Aisha-Siddiqah wadda take kira (Petel) dinta tazo hutu, ta gwada mata warawarannan da suka fito daga hannun Haj. Sappah, Baban Petel ya tabbatar mata na danyen farin zinare ne (white gold) kirar kasar Saudiyyah.
Ta san Patel da son warwaro, kusan kullum baka raba hannunta da awarwaro, kamar wata ba’indiya haka zata yi ta rawa ita kadai tana juyasu tana kadasu idan tana cikin farin cikin wani abu, an sha ‘seezing’ dinsu a makaranta amma hakan bazai hana gobe ta sake rokon Ummanta ta sai mata wasu ta sake sakawa ba.
Ranar hutun 'yan makaranta Aisha - Siddiqa Yunus, siririyar budurwa ‘yar shekaru goma sha shidda, Aisha mai sassanyan kyau, ma’abociyar yalwar suma (gargasa) a gira da saman idonta, wadda kaurinsu ya fallasa adadin yawan wadda zaka tarar a gashin kanta, da tsakar rana ta dawo gidan su daga Billiri. Motar haya ta biyo yadda ta saba ta dawo gida, ba tareda anje daukota ba.
Data shigo dakin ta wata irin mika Aisha tayi ta gajiya da farin cikin dawawo gida, tana fadin "Oh no place like home!". Sannan ta ajiye jakar goyonta da bacconta ta fada wanka.
Bata samu Ummanta a gida ba ta shiga makwabta gidansu Umman Abdul dubiya, don haka Aisha take ta kissima kome da me Ummanta ta sayo mata daga Saudiyyah a hajjin bana? Ta san dai tsarabarta tafi ta kowa yawa a wurin Umma. Allah dai yasa bata manta da sakonninta na Abaya da dogayen riguna ba.
Umman Siddiqah (yadda ake kiranta a unguwar su ta Jeka da Fari) ta dawo gida gefen la’asar daga dubiyar data shiga a makwabtansu, ta tadda Aisha-Siddiqah ta fito daga wanka kenan har ta saka kayan sallahrta koren jilbaab ta tada sallah. Don haka ta wuce ta hada mata abinci, sannan ta koma dakinta ta janyo jakar tsarabarta ta soma fidda tsarabar Aisha din a gefe. Musamman (bracelet) din wajen Nenne, ta san sai Aisha tafi murna da shi fiye da duk tarkacen abayoyin data kwaso mata.
Aisha na idar da sallah ta ma kasa tsayawa ta shafa addu’a tsabar dokin ganin Umma, sai ta wuce dakin Umma da gudu ta fada jikinta cike da farin cikin dawowarta lafiya, rabon ta da Umma yau wata uku kwarara tun komawarta hutun farkon zango. Lokacin visiting dinsu duk tana Saudiyyah. Umma ta rungume ta itama tana dariya tana fadin.
“Petel am miyelwi ma (Petel dina nayi kewarki)”.
Bada bata lokaci ba ta shiga fiddo warawaran na na wajen Haj. Sappa, guda shidda rus ta shiga zurasu a hannun Aishah daya bayan daya. Kasancewar Petel ‘yar karama mai karamin jiki kuma ‘yar siririya, komai na halittar Siddiqah karami ne, hanci ido da baki, sai suka shige hannun nata sukuf babu gargada, kuma basa zamewa sun zauna cif-cif kamar saida ta gwadasu tun farko.
Rashin kumari irin na Petel yana matukar damun mahaifiyarta, don sam bata da jiki kuma bata da kauri hakanan bata da cika ido, wasu lokutan Aisha bata da kuzari idan Asma dinta ya motsa. Tana da Asma kadan (Mild Asthma), a gida ne ko a makaranta koyaushe baka rabata da inhaler a tare da ita.
Bakin Aisha ya fadada har kunne, don murna, warawaran sun burgeta wadanda bata san ina Ummanta ta samo su ba, ta san dai Umma ko tana da kudin sayensu bazata saye su haka kawai ba, Petel (Siddiqah) ta kasa boye mamakinta da farin cikinta, don ta san ko guzurin Ummanta gabadaya aka hada bazai sayi bracelet dinnan ba, in dai na danyen zinare ne kamar yadda suke zagin idonta. (Bayeraben mutum nada son ajiye kadarar zinare, don haka shine kadara abin ajiyewa a wurin Nenne Sappa da ‘ya’yan ta mata, Taiwo, Firdaus da Fatima).
Aisha-Siddiqah tace da Umma cikin mamaki “Umma ina kika samo awarwaro mai kyau da tsada haka?”
Nan Umma kamar jira take don har zuwa lokacin shaukin haduwarta da Hajiya Sappa da karamcinta na makale a ranta, kullum da tunanin sake haduwa da ita take kwana take tashi, nan ta kwashe labarin haduwarsu da Haj. Sappa a filin Muna ta labartawa Aisha, yadda ta tsinci jakar kudinta da yadda ta maida mata, irin amincin da ya shiga tsakanin su sanadin hakan. Ta ce ta dai lura matar Basarakiya ce ko matar