un Haj. Zainab gam. Tare suka zauna akan kananun katifunnan na filin Arfah Haj. Sappa ta rasa da bakin da zata godewa wannan baiwar Allah.
Abinda ya bata mamaki shine na farko da ganin matar ba wata wadata ce irin tasu a tareda ita ba, amma ta iya wannan halin na mutanen kwarai, mai wuyar samu a wannan zamanin.
Dala na gugar dala da har dala dubu biyar ne a cikin battar, data kirga suna nan cif yadda ta lankwasasu ta ajiye a cikin zip ko guda daya bata yi ciwon kai ba.
Ashe dama har yanzu akwai mutane masu wadatar zuci da gudun abun duniya irin haka? Nenne Sappa, ta tambayi kanta domin kwarai Haj. Zainab ta burgeta. Kudine da Abdulrasheed Kehinde ya bata domin tayi guzurin aikin Hajjinta dasu kamar yadda ya saba bata duk shekara. Da ta tabbatar ta yar da su taji babu dadi amma bata yi mamaki ba sabida irin gajiyar datayi da tafiya a lokacin a Munna, ji take kamar ta yanke kafafunta bakidaya ta yar, don suma sun mata nauyi da kyar take iya cirasu, balle jakar guzuri.
Nenne da Hajiya Zainab basu rabu ba daga filin arfah ba sai da suka karbi adireshin junansu na hotel din da kowacce take zaune a cikin Makkah.
Bayan sun koma Makkah Nenne ta soma tunanin me zata baiwa wannan matar a matsayin kyauta ta jinjinawa, sabida taji dadin wannan halin kwarai data gwada mata har fiye da kudin data maido mata. Nenne Sappa na matukar son mutum mai tsoron gamuwa da Allah, mai gudun duniya mai cin halal.
Don haka da taje sayawa Princess Fatima warawaran zinaren data bata sautu a kasuwar Jiddah, sai ta sayi wasu warawaran (bracelet) again, sak irin na ‘yan biyunta Firdausi da Fatima wadanda kudinsu mai kima ne da daraja sosai.
Data dawo daga Jiddah shagon zinaren kai tsaye ta wuce gidan ‘yan Gombe wato masaukin ‘yan jihar Gombe a Makkah.
Da yake ta rike lambar dakin da haj. Zainab ta gaya mata, sai ta hau lifta (elevator) ta isa har kofar dakin, ta danna ‘door-bell’ daga ciki akayi mata iznin shiga sannan tasa kai ta shiga dakin da sallama abakinta.
Nan ta tadda Haj. Zainab ita kadai a dakin dawowarta kenan daga Dawafi. Haj. Zainab tana ganinta nan da nan ta shaidata, ta kuwa shiga lale marhabin da hidima da ita da duk abinda take dashi a dakin na sakawa a baka, itace kawo Laban(Al-mara’i) itace kawo ‘Aseer’ wato jus mai sanyi. Kai har Gahwah data koyi sha a kasar ta hada mata wadda ake kira (Gahwah Al-Arabiyyah) ta zuba musu a kananan kofunan karau suka zauna a gefen gadon Haj. Zainab suna sha sai suka balle da hira.
Ko daga yadda Nenne Sappa take magana kadai cikin yanayi na kasaita Haj. Zainab ta alakantata da Sarauta mai girma cikin zuciyarta, in kuma ba sarauta ba to da arzikin da ya zauna a muhallinsa, komai na jikinta kadai dake walwali cikin zobban zinare ya fallasa hakan. Sun dade suna hira kafin Nenne ta ce zata koma hotel dinta, don ta baro autarta Firdausi a daki kwance bata jin dadi tun dawowarsu Arfah a nasu Fundaq (hotel) din. Ta ciro warwaron data zo dasu a cikin battarsu ta damkawa Haj. Zainab a cikin hannunta.
Ta ce kyauta ce tayi mata don su rinka tuna juna in su koma garuruwansu mabanbanta. Tana son mutane masu irin halinta na gaskiya da rikon amana. Sama da komai tsoron abin duniya.
Haj Zainab ta ce “ba’a maida hannun kyauta baya, don hakata gode”. Kuma duk da bata san darajar wadannan warawaran ba, amma ko ba komai aka ce ido ba mudu ba ya san kima.
Tayi godiya mai yawa sosai ga Nenne, tanakokarin gwada warawaran, cikin ‘yar dariyar jin dadin alkhairin da aka yi mata Haj. Zainab tace da Nenne.
“Yo ni wannan ai bazasu shiga hannu na ba, sun min kankanta na yara ne, sai dai in kaiwa PETEL (AISHAH-SIDDIQAH), yafi kama da na ‘yan mata”. Nenne ta ce “har nawa kike da bazakiyi kwalliya da awarwaro ba?” Nan ta daga nata hannun tana nuna mata nata warwaron guda shidda tace “bana rabo dasu a hannayena don su din adon diya mace ne. suna karawa kwalliyar mace kima su da zobuna, wacece Petel-Aisha-Siddiqah kuma? Halan kinada ‘ya budurwa ne kema kamar su Fatima?
‘Yan biyuna (Firdausi da Fatima) na sayawa, shine kema nayi miki sha’awarsu”.
Cike da far’a Haj. Zainab tace “eh, inada Petel-Siddiqah a gida, itama ‘yan biyu ce, su biyu aka haifa tun lokacin Hassanar ta rasu a wurin haihuwa, ita kadai ta saura mana.
Allah ya dora min iftila’in WABI, domin kuwa haihuwata goma amma AISHA-SIDDIQAH ce kadai Allah ya bar mana a raye”.
“Allahu akbar!” Inji Nenne, “lallai dole ki so AISHAH-SIDDIQAH. Har nima yanzu zan tayaki son nata, naji a raina ina son SIDDIQAH. Ajinta nawa yanzun?”
Murmushi sosai Haj. Zainab tayi tace “Petel na ajinta na biyar a makarantar gwamnatin tarayya ta Billiri Gombe”. Sun dade a bakin kofar suna hirar Aishah, kafin Nenne ta karbi lambar wayar Haj. Zainab ta gida Najeriya, da alkawarin duk ranar da Allah yayi mata shigowa Gombe (kasancewar tana yin shekaru kusan biyu bata zo ganin gida ba), zata nemi Haj. Zainab har unguwarsu su gaisa. K