guzurin mahajjata da ake basu, daloli ne tsura abin tsoro da firgitarwa, domin ita dai da idonta bata taba ganin irin wadannan takardun kudin a zahiri ba.
Da sauri Haj. Zainab ta fito ta duba hagu da dama, gabas da yamma, kudu da arewa babu Hajiyar lagos babu alamarta, ta bace a cikin dubunnan mahajjata masu sanye da fararen kaya da bakake kusan bakidayansu, kalar kayan jikin maza fari, na mata baki ne tako kasa gane ko mai kama da ita.
Haka ta daure jakar nan a cikin jikinta taje ta karasa jifanta ta dawo Hemarsu, tana ta addu’ar Allah Ubangiji ya hada fuskarta da Hajiyar Lagos kafin su gama zaman Minna su koma Makkah.
Dadin abun ma ba’a sayen abinci a Minna, da bata san yaya Hajiyar zatayi ‘coping’ a wannan lokacin ba.
Duk inda ta ga ‘yar Najeriya sai tayi kokarin ganin fuskarta, ko Allah yasa ta dace da ganin wannan kyakkyawar bafullatanar baiwar Allah, wadda haka kawai ta shiga ranta domin ta ga tsantsar mutunci da kamala a tareda ita.
Washegari Haj. Zainab din tayi wani tunani, me zai hana taje Hemar alhazan Lagos ta duba ta a can? Sai ta kira maigidanta wanda tare sukazo kasancewarsa ma’aikacin hukumar alhazan jihar Gombe, sun samu kujerar Hajji ne ma sanadin aikin nasa ba karfine dasu cancan ba. Maigidan nata Malam Yunus, tsohon malamin (federal government) ne da ya jima yana koyarwa a makarantar sakandiren ‘yammata ta Bajoga, shekaru biyu baya Allah ya tarfawa garinsa nono aka dauke shi aiki a Gombe State Pilgrims Board (ma’aikatar alhazai ta jihar Gombe).
Tun daga lokacin ne kuma suka samu damar da duk shekara yake samun kujerar hajji biyu, karkashin hukumar alhazai don su zo su kula da mahajjatan Gombe a Saudi. Shine yake baiwa maidakinnasa.
Da kyar ta samo Hemar ‘yan Lagos, bayan ta ci tafiya da zagaye a cikin Minna har ta gode Allah. Haka Haj. Zainab tayi ta bin fuskokin mata Yarabawa daya bayan daya tana dubawa amma ko mai kama da wannan kyakkyawar dattijiyar bafullatanar bata gani ba, ita gashi ko sunanta bata sani ba balle ta tambaya, amma tabbas ta rike kamannin fuskarta da kyau. Ita gani take ma fuskar na mata yanayi da wata popular fuska data sani ko a hoto ne ko a zahiri, amma ta kasa gane inda ta san fuskar Hajiyar Lagos. (A rashin saninta, fuskar Haj. Sappa na mata yanayin kama ne data Sarkinsu na Gombe, wato Uban Kasar Gombe na wannan lokacin, wanda suke kamar an tsaga kara da Nenne Sappa, don shi ya sha nono ya saki ta kama.
Allah bai tashi hada su ba sai ranar hawan Arfah a kan dutsen ARFAH. Bayan Haj. Zainab ta fidda ran ganin Nenne Sappa don damka mata dukiyarta. Har ta fara tunanin kaiwa hukumar kasar Najeriya ta Saudiyyah kudin tayi musu bayani. Haduwar tasu a filin Arfah ya zo ne indirectly ba tareda zaton kowaccensu ba.
Addu’ar data ji matar bayanta ta daga hannu sama tana yi a fili ne ya ja hankalinta gareta. Hannayenta biyu matar ta daga cikin kaskantar da kai ga Ubangiji da tsananin ikhlasi da tawali’u cikin addu’arta, sannan cikin zubar da hawaye mai yawa a kan dutse mai alfarma na Arfah, ranar da Ubangiji yayi alkawarin baya juyar da addu’ar bayinsa akan wannan tsarkakakken dutse, taji matar tana yin addu’a ga haularta (abinda ta haifa) a fili cikin harshen fulatancin Gombe ziryan.
“Ya Ubangiji ga Dana ABDURRASHEED dan IDRIS ABDURRASHEED (Kehinde), managarcin bawanka mai kyautatawa iyaye da kula dasu, mai tsantseni wajen ibadarka da kulawa ga ‘yan uwasa mata, mai yawan alheri ga danginsa da kyakkyawar zuciya ga kowa, mai tarin halayen kwarai na kyautata zumunci.
Na roke Ka, Ka dubi halin da Kehinde yake ciki na rashin aure. Ya Ubangiji ka yanke masa, kasa yana da rabon yin aure a rayuwarsa, ka kare min shi daga duk wani nau’I na aikin sabon ka a dalilin rashin aure, Ya Allah”.
Ta shafa addu’arta a daidai lokacin da take ji a zuciyarta Allah ya amsa mata, Mala’iku sun ce Ameen Abdurrasheed zai yi aure, kamar yadda Hajiya Zainab dake bayanta ma tace “Ameen” a fili, ta kuma tayata da shafa addu’ar itama zuwa tata fuskar cikin tausayawa, ganin yadda Nenne ke kuka tana addu’ar.
Sai Nenne taji an dafa kafadarta a hankali ta baya, anyi mata sallama cikin nema mata amincin Ubangiji.
Da far’a ta juya ta amsa tana share ido, kuma nan da nan suka gane juna. Suka rungume juna suka sauko daga kan dutsen Arfah tare rike da hannun juna.
Hajiya Zainab ta kwanto lalitarta daga cikin jikinta, ta damkawa Nenne Jakarta hannu da hannu.
“ga nan kudinki ne masu yawa da kika manta nake ta nemanki in baki. A bandakin da muka shiga a Munna kika mantasu, na nemeki kamar ba gobe, har Hemar ku ta ‘yan Lagos naje nemanki Allah baiyi haduwarmu ba, inata addu’a dai da rokon Allah ya hada mu cikin sauki in baki, don in aka shiga Makkah bansan halin da zaki fada wajen sayen abinci ba idan babu guzuri a tare dake, don kamar dukkan guzurinki yana cikin jakar nan.”
Baki Nenne ta saki tana mamaki. Ta tuna zunzurutun dalolin dake cikin jakar. Sai ta kara rike hann