kuma da wadda ta kwanta masa da yake ganin zai iya aure, gobe-goben nan zasu aura masa mata hudu, akai masa su gidan sa, kuma sun yi rantsuwa da Allah dole ya zauna dasu gabadaya in yana son albarkarsu, bijirewa wannan umarnin na nufin zasu cireshi cikin ‘ya’yansu tunda dai Allah yasa ba shikadai suka haifa ba.
Shine babba cikin family duka, amma yafi duk kannensa basu wahala akan maganar aure da janyo musu magana daban-daban daga al’ummarsu duk akan rashin aurensa”.
Prince AbdulRasheed Idris Akanni, tunda iyayensa suka fara wannan cece ku ce din yake sauraronsu, ya rasa irin amsar da zai bayar da zata gamsar da iyayensa maza hujjarsa ta gudun aure a yau. Cewa mata sun dade da sire masa, bashi da wani buri a kan diya mace yanzu, ba macen da zai kara so a rayuwarsa.
Shin shi mai maganar cewa yazo ga kannensa nan a gida ya bashi wato, Abdulfatahi Akanni, yanada masaniyar cewa dansa ne ya raba shi da mata bakidayansu???
Ko yanada masaniyar cewa dansa Adetokumbo ne yayi masa cin amanar data sa ya tsani mata koda gold aka kerasu tun daga kan Hasinah Ambursa???
He is speechless a lokacin, sai zufa, jibi, da gumi da yake ta yankawa daga zaune cikin kurkukun idanun iyayensa da suke zazzare masa su daya bayan daya irin nasu na jiga-jigan yarbawa.
Da suka takura da jin ta bakinsa sai yace musu yana jin nauyin dukkanninsu, su yi masa alfarma ya gayawa Nenne amsarsa in yaso ta gaya musu.
Ganin irin halin da ya shiga ne na rudu mai yawa da gigita yasa suka kyaleshi, domin sun tado masa kwantaccen bacin ransa, aka yi addu’a aka rufe taron a haka.
Suka ce lallai a gobe suna jiran jin amsa daga bakin Nennensa, in ba haka ba, zasu dauki matakin da ya dace ne kawai wanda shine aura masa kannensa mata hudu kuma a rana daya daga cikin ‘ya’yansu mata.
Ita kanta Nenne din zille mata yayi ta yi basu hadu ba har ya koma Qatar. Ya san kuma bazata jira zuwansa ba don a ranar da asubah zata tashi zuwa pilgrimage (aikin hajji) daga hukumar alhazai ta jihar Lagos, kuma in ta tafi Hajj sai tayi kwanaki arba’in wato jirgin karshe sannan take dawowa gida.
Kafinnan ya samu ya yanke mai fishsheshi, su kuwa kannen Ubansa yasa a ransa bazasu kara ganinshi nan kusa ba.
Bayan tashin Nenne zuwa Hajj, ya koma Qatar, ya cigaba da fuskantar aikin sa na (Oil Refinery), wata irin rayuwa Prince Abdulrasheed keyi ta cikawa kai aiki a gida da ofis da daukewa kai kewa a ‘stable’ din dawakansa a kowanne yammaci ta hanyar bankawa cikinsa Nescafe (coffee) alhalin likita yayi limiting shan (coffee) dinsa, a cewarsa in ya sha yana jinsa fresh babu damuwa ko kankani a cikin ransa, shan coffee yana kara masa kuzari, kwana biyu dai bai hau Doki ba don har zuwa lokacin hadewar karayar jikin sa bata bar dan motsa masa lokaci zuwa lokaci ba.
**** **** ****
ZAMAN HEMAR ALHAZAI A MINNA
N
enne Sappa, ta sauka a kasar Saudiyyah domin sauke farali na wannan shekarar tare da diyarta autarta Princess Firdausi.
A zaman Hema ne na kwana uku da ake yi a Minna, ana zuwa jifan shaidan ana dawowa Hema a huta ko ayi kwanan ibada, Nenne ta hadu da Haj. Zainab. Wadda tazo daga jihar Gombe, maigidanta Malam Yunus ma’aikacin hukumar alhazai na jihar Gombe.
Ba Hemar su daya ba, don kamar yadda kowa ya sani ne Hema din (is state by state), Haj. Zainab na Hemar Alhazan Gombe, Nenne tana Hemar Alhazai Yarbawa na jihar Lagos.
Wajen tafiya jifan Shaidan ne suka tafi tare, tafiya ce da alhazai ke yi mikakka wadda bata karewa kamar bata da karshe, zuwa inda za’a jefi la’anannen Allah. Suna tafiya suna Hailala, Princess Firdausi bata biyo su ba yau, tana kwance a Hema domin rashin tsarki da ya sameta a ranar.
Jiki na girma, tafiya tayi tafiya sai Haj. Zainab taga Nenne na neman faduwa, domin ba karamin jigata tayi ba.
Sai ta kama hannun Nenne, ta karfafeta, tace “baiwar Allah don Allah mu dan tsaya mu sha zam-zam ko ma samu karfin cigaba da tafiya.”
Nenne tace “kin kyauta diyata, ni fitsari ma nake ji”.
Suka sha zam-zam suka koshi, suka zagaya bayan wata Hema don shiga bayan gida.
Nenne Sappa ita ta fara shiga ta fito ta gama zata wuce ba tareda ta jira Haj. Zainab ta shiga ba, don dama ba wai tare suke tafiyar ba a’ah, hanya ce kawai mai hadin zumuntar dole.
Da ta fito, bayan sun yi sallama ta kuma gode mata bisa kulawar data nuna mata. Har ta gaya mata ita daga Lagos tazo, ita kuma tace mata daga Gombe tazo.
“Ashe ‘yar kasata ce, madallah dake. Nima asalina ‘yar Gombe ne, aure ne ya kaini jihar Lagos”.
Sukayi sallama, Nenne ta wuce ta cigaba da tafiyar ibadah, Haj. Zainab kuma ta shiga toilet din.
Har ta gama abinda zatayi ta fito, ta lura da bakar jakar nan ta guzurin mahajjata ta matar can ‘yar Lagos rataye a jikin kofar bandakin. Wato ta manta guzurinta gabadaya.
Ta dauka ta bude, yawan dalolin data gani ‘yan dari-dari a ciki ya firgitata, domin ya zarce normal dalolin