nan take yayi alkawarin sayawa AbdulRasheed sabon yaron Doki (Criollo Horse), a karshe yace.
“Baka hau doki ba kayi me jikana? Ride it with passion the great Prince of the Ilorin Emirate!!!
Tsautsayi na Allah ne don ka fadi doki sai ace ka daina Polo kwata-kwata? To wa tsautsayi ya bari inace abu ne da baya wuce ranarsa? Rabu dasu takwara duk jinsu nake kawai ina biye musu don a zauna lafiya, amma ba mai hanaka yin abinda kake so kaji. Don duk sun hada baki wai na hanaka hawa Doki daga yau, fau-fau.
Allah na tuba “Prince” din duk da bai hau doki ba ai bai cika “Prince” din ba”.
Shiyasa fa AbdulRasheed ke matukar son Kakan nasa, yake kuma amsa kiransa a duk lokacin da ya bukaci ganinsa a ko’ina yake kuma kome yake komai muhimmancin abun zai bari yazo. Sabida a duniya ba mai son farin cikinsa irin Sarki.
A daren ranar sunyi hirarraki iri-iri wadda ta shafi lafiyar Kakan nasa, da cigaban rayuwar AbdulRasheed kacokam. Wani abu da yasa Abdulrasheed yake sakewa da Kakansa yake kuma yin doguwar hira dashi saboda shi baya matsa masa akan maganar aure, kullum addu’a yake masa don ya yarda rashin auren AbdulRasheed har zuwa yanzu ba haka kawai bane, akwai dai abinda Allah ya boye a ciki, ko dai aljana ta aureshi, ko kuma akwai wani boyayyen dalili da kowa bai sani ba.
Bayan sunyi sallama da Kakan kan zai je ya kwanta, kafin AbdulRasheed ya kai ga isa turakarsa dake gidan sarautar Ilorin, Kawunsa Turaki, wato mai bin mahaifinsa a haihuwa ya aiko ace dashi lallai suna son ganin shi su duka gobe (kannen mahaifinsa Akanni’s gabadayansu) kafin ya koma Qatar.
Tun daga nan AbdulRasheed ya sha jinin jikinsa, cewa ganawa ce ta musamman iyayen nasa maza zasu hada a kansa, ayi masa taron dangi a titsiyeshi kuma ba’a kan komai ba sai akan maganar aure da baya ko son jin an alaqanta shi da ita.
Ya so ya gudu cikin daren kafin wayewar garin, to ‘booking’ dinsa sai akayi rashin sa’a na jibi talata ne. Haka yayi ta kokarin canza ‘booking’ don dai ya samu ya kubucewa wannan haduwar wadda yasan bazata yi masa dadi ba, Akannis sun gama zura masa ido da bata yawun bakinsu akan maganar aurensa, duk yadda yayi kokarin barin Ilorin a daren don gujewa fushin iyayensa maza bai samu damar hakan ba.
A washegari mahaifin Prince wato Engnr. Idrees Akanni da shima suka gayyato don ayi zaman tare dashi ya iso Ilorin, a ranar taron ya iso don ta jirgin sama ya taho daga Lagos.
**** **** ****
THE TEN AKANNIS’
S
u goma dinnan, wato kannen mahaifinsa da mahaifin nasa haka suka saka shi a tsakiya yau suka zagayeshi a fadar Maimartaba Sarkin Ilorin, akan yau ba inda zaije sai ya gaya musu ‘exactly’ me ya hana shi aure a rayuwarsa?
Duk kannensa na cikin family dinsu sunyi aure, ga albarkar ‘ya’ya, daga mai yara hudu sai mai biyar. Wannan masifa a cewar Akanni’s, sun kasa gane mata. Yo masifa mana?!
Rashin aure babu dalili wanda addini ya yarda dashi ga mai shekaru sama da 40 ya zama masifa a cikin zuri’arsu.
Suka hada baki wajen cewa “bazasu amince ya bata musu ‘image’ na gidansu da maluntarsu ba, don kawai ya ga Sarki yana daure masa gindi yana abinda yaga dama, ba don komai ba sai don yana gudun bacin ransa.
Suka ce Sarki yafi kowa damuwa da son yayi aure ya dauki ’ya’yansa yana raye, kawai baya nuna masa ne don ya ga baya so, amma su sun sani, Sarki baida damuwa a halin yanzu sai ta rashin aurensa, suka taru akan cewa bazai kashe musu tsoho da damuwa ba dole ya bashi tattaba kunne ya dauka yana raye.
Mutawalle Abdulfatahi ya ce “idan macece bai samu ba, su iyayensa maza zasu bashi ko guda nawa yakeso a cikin ‘ya’yansu mata matasa da basu kai ga yin aure ba.
Idan kuma baya son auren gida, ya fadi duk diyar Sarkin da yake so a masarautun Najeriya, na kudu dana arewa, su kuma za suje su auro masa.
In kuma lafiyar yin aure ce bashi da ita, itama yau dai sunaso su sani, zasu shiga ko’ina su fita daga nan har birnin Sin, su nema masa magani, su iyayensa ne da suka haifeshi, ya yarda cewa babu boye-boye yau a tsakaninsu.
Tunda ya nuna Ubansa wato Waziri bai isa dashi ba, saboda Polo da abunda yake samu cikinta dake rudarsa, suka ce to Waziri Idreesu ya basu dama su yanke masa duk hukuncin da suka ga ya dace da shi yanzu.
Su kuma a adalci irin nasu da Allah yace musu su yiwa ‘ya’yan su, bazasu yanke masa kowanne hukunci ba, sai sun bashi dama sun ji ta bakinsa tukunna, wato sai sun ji hujjarsa ta kin yin aure daga bakinsa. Alhalin mahaifinsa nada shekaru 25 mahaifiyarsa Sappa nada 15 aka yi musu aure, wanda albarkar hakan ne har suka sameshi cikin kuruciyarsu suka girma tare dashi.
Shi yau Abdulrasheed shekaru 43 yake nema, me kuma ya rasa a rayuwarsa?
The Akannis’ suka kara da cewa; wannan rashin auren nasa masifa ce babba a garesu da zuri’arsu. Suka kuma rufe zancen da cewa, “idan har bashi da hujjar kin yin aure, bashi