kasance. Discipline Master da Aisha tayi masa narai-narai da ido cikin rokon ta tuba bai san sanda ya zabura don kwato kansa daga tasirin idanun Aishah ba, ya buga dorinarsa a kasa cikin barazana.
“Zaki fada muji ko ba zaki fada kowa ya ji me kike yi mata ba?”
Maimakon Aisha ta bada amsa sai ta soma tumami a kasa tana kuka tana shura kafafu.
“Malam in ka dake ni Asma ta tashi zata yi, Malam ni asthmatic ce. Ummana kafin a kawo ni tace ayi mata alkawarin ko me zan yi za’a bani punishment, na aiki ko kneel down kowanne irine a bani, amma kar a taba mata lafiyar jiki na.
Wallahi Malam nima a bakin yaran unguwarmu naji”.
Discipline Master da sauran malamai duk suka saki baki da ido galala! Suna kallon Aisha-ikon Allah, irin kukan da take yi da tumami a kasa na shagwaba kamar karamar yarinya alhalin tayi 15, bayan ko dukan nata ma bai yi ba ya hanasu sake ce mata komai. Ta sake sakin kuka tana cewa Bisola ta mata sharri. Ai kuwa Disdipline Master ya fusata ya zuba mata dorinar a gadon bayanta guda daya, kafin ta farfado ya daddage ya sake zuba mata wata akan siraran kafafunta, yace “bari in saki kukan shagwaba da hujja, ko kinga Umman naki anan da zaki mana shagwabar banza da wofi? Tukunnama makarantar nan ta Babanki ce da zaki uzzurawa ‘yar mutane?”
Aisha suma ne kawai bata yi ba, don bulalar ta shigeta yadda ya kamata, muryarta fal kuka tana mutsu-mutsu tace “Na tuba Uncle, na tuba nabi Allah na bi ka, na daina wallahi Uncle, daga yau bazan kara yi mata ba, kuma na daina cewa Yarbawa masu kwalo-kwalo ne”.
Malam Sayyadi ya kara shimfida mata lafiyayya wadda tafi ta baya shiga tsokar jikinta, Aisha tayi flat a kasa wannan karon sabida yadda bulalar ta shigeta har wani dan karamin fitsari ta saki ta cikin uniform dinta.
A wahale ta ce tayi “na maida kalamai na, Bisola ki yi hakuri, Yarbawa basa tukin tuwo da duwawu, Yarbawa basa kashi a kwano, ke ba bayerabiya bace mutum ce ‘yar najeriya kamar mu, na tuba na bi Allah na maida kalamai na Uncle”. Daga malaman dake gefe har Discipline Master din saida Aisha ta basu muguwar dariya amma suka hadiye don so suke sata a saiti.
Suka rufu wajen yi mata fada da nasiha cewa abinda take yiwa Bisola ba daidai bane ko a addini, Bisola musulma ce kamarta, ‘yar kasa cikakka kamarta, abinda takeyi din kabilanci ne da wariyar launin fata.
Sannan a matsayinmu na ‘yan Najeriya dole mu kaunaci juna, mu cire banbancin yare da na al’ada har ma dana addini inta kama, in har ana son a samun cigaba da hadin kai a tsakanin al’ummar Najeriya.
Bisola ta dinga basu labarin irin uzzurawar da Aisha ta dade tana yi mata, ta ce komai tayi sai Aisha ta kushe, tana jin dadin kiranta “bayerabiya” a cikin yara ‘yan uwansu, kai sai ka rantse da Allah kiran bayerabe da Aisha ke yi cikin ‘mockery’ na nufin bayeraben mutum ba cikakken mutum bane wani abu ne daban, (kusan haka yake a idon Aisha-Siddiqah) a kabilancin data dade da sawa ranta akan Yarbawa.
Ita a tunaninta Bayerabe wani kalar mutum ne daban wand bashi da katabus a cikin hausawa da Fulani, kamar wani alien take kallonsa. Ko kuma ka dauka wani ‘yanci bahaushe ko bafillacen mutum yafi bayarabe in dai a idon rigimammiya… ‘yar Ummanta, Aisha-Siddiqah Yunus ne.
**** **** ****
Labarin jinyar da AbdulRasheed yayi bayan fadowa a Doki ta kai kunnen Kakansa Emir of Ilorin, ai kuwa ya tubure sai an shirya masa tafiya har Qatar don gano jikin Kehinde. Inda su Turaki da Mutawalle da Shettima har ma da Waziri mahaifin Kehinde din suka taru suka ki amincewa da hawansa jirgi a yanzu, don a lokacin jikin girma ya fara motsawa ba lafiya ce ta isheshi ba, in ya sa rikici kan yana son yayi abu, su duka goman damuwa suke shiga saboda basa iyawa rikicin tsufansa.
Daga baya suka yanke shawarar su kira Abdulrasheed din yazo kawai sai dai Kakan ya ganshi ba tare da an gaya masa zai zo ba.
Turaki shi ya kira dan nasu Engnr. AbdulRasheed a waya, yace lallai yazo cikin satinnan Emir ya ganshi hankalinsa ya kwanta ko suma nasu ya kwanta da rikicinsa.
Bai jima da komawa Qatar ba, yanada tarin ayyuka a gabansa amma kuma, baya hada lamarin Kakansa da komai, don haka Abdulrasheed ya ajiye komai dake gabansa ya shirya zuwa Ilorin a sati mai zuwa don ya ga Kakansa.
**** **** ****
Sarki Abdulrashid ya rika ina yaka-saka-ina-yaka-aje da jikansa mafi soyuwa a gareshi Prince AbdulRasheed (Kehinde) ta bakinsa, lokacin da ya sauka a Ilorin, tarba ta girma aka shirya ma babban jikan na Sarki Prince AbdulRasheed, kuma takwaransa.
Basu samu kebewa ba shida Sarki sai da daddare kasancewar saukar safe yayi, ya gaya masa raunin da dokinsa mai tarihi wato SAHEEB yaji sosai sanadin tsautsayin da ya samesu shida dokin. Yanzu haka ya daina wasan Polo dashi sai sauran dawakansa.
Sarki da karawa aya zaki wajen taya jikan nasa son Polo da duk abinda yake so