NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 33 of 44

uka bai fi girman a hada tafin hannu biyu ba. Farin jininta a wurin tsararrakinta kuwa sabida kiriniyarta da kyawunta da kaifin bakinta, ga wauta da gwalangwaso abin ba’a magana. Bisola Akanbi kullum Aisha ta fara mata waka saita koma gefe cikin muzanta kamar mujiya a cikinsu, don yadda Aisha tasa ‘yan dakinsu suke nuna mata wariya da kyama wai don kasancewarta bayarabiya daya tal a hostel dinsu, cikin dalibai masu yawa hausawa da fulanin Gombe da suka fi yawa a FGC Billiri, wadda aka kawo daga jihar Ibadan, aikin asibitin federal government ne ya kawo iyayenta garin Gombe, har yayi sanadin da aka yi mata transfer zuwa FGC Billiri. Bisola Akanbi musulma ce gaba da baya. Yarinya mai hakuri da rashin sakewa da hausawa. Har ya zamnto daga zuwanta Billiri zuwa yanzu su Aisha da gang dinta su Amintako, Ramatu da Zannura suna neman jaza mata ciwon damuwa, sabida yadda Aisha ke nuna kamar itaba cikakkar mutum bace, ko kuma ba daya take da sauran dalibai ba, wai tunda ita bayarabiya ce. Kabilanci muraran a wurin Aisha abin ba’a cewa komai. Yau dai abinna Aishatu-Siddiqah Yunus, ya kai Bisola Akanbi bango, duk hakurinta Aisha ta kaita karshe, don ta sa an wareta daga cin abinci tare dasu a dakin, sabida itace gang leader ta dakin gabadaya, ‘yan dakin tun kan a kawo Bisola suna yin ciyayyar abinci a dakinsu. Da aka kawo Bisola daga baya suna ci har ita, yau Aisha tace idan har basu cire Bisola daga ciyayya ba ita zata daina ci tareda su, don ita bata son cin abincin yarbawa ko ci tare dasu, alhalin taji ana fadin suna kashi a kwano, don haka Bisola ita kadai aka zuba mata nata a plate, aka tura mata gefe wai don ita bayerabiya ce. A cewar Aisha Yunus, gang leader ta ‘yan aji hudu (SS 1) bazata ci abinci da Yarbawa masu cin dodon kodi da hannunsu ba. Wannan abu yaima Bisola ciwo. Kasancewar ta dade tana shaqa daga Aisha, ta yi hakuri mai yawa da Aisha, hakurin da ya hada da dan tsoro-tsoro, kasancewar Aisha nada wasu ilhamomi, watau kwarjininta da kyawunta da kaifin harshenta dake sawa aji ana shakkarta, sannan duk ‘yan gang dinta su Amintako halinsu daya da ita na tsokana da fin karfin wanda bashi da baki kamar Bisola. Amma yau? Dama aka ce mai hakuri bai iya fushi ba. Da kuka Bisola taje (staff room) ta gayawa Discipline Master duk abinda Aisha ke yi mata a hostel, a aji, a library, a wajen wasa ne dama duk inda ta ganta tun zuwanta FGC Billiri. “This is Mockery! Derision!” Inji Malamin cikin bacin rai. Discipline Master Uncle Sayyadi ya cika da mamaki, ransa kuma dana sauran malamai ya baci sosai, ace a makaranta ta gwamnatin tarayya (unity school) ta Najeriya ake irin wannan abin Allah wadai su malaman basu sani ba? Nan ya aika Head Girl Hasiya Mato, yace maza-maza ta kawo masa Aisha-Siddiqah Yunus ofishin malamai (dead or alive), sannan yace Bisola ta zauna a gefe, yau sai ya ga uban Aisha. Bisola ta koma gefen Teacher din tana sharar hawaye domin hakika Aisha Yunus, ta zame mata matsala cikin makarantar, ta dade tana cutar da feeling dinta. Head girl Hasiya din taje har dakinsu ta sako Aisha a gaba har ofishin malamai, duka malaman sun hada kai a ofishin suna tattauanawa akan al’amarin da Bisola ta kawo kara tana neman ayi mata iyaka da Siddiqah Yunus. Discipline Master yafi Bisola jin bacin rai, koda yace a kawo masa ita, kafin sui so ya shirbinawa dorinarsa man shanu sau uku kuma dama gashi lokacin san yi ne, yace a ransa yau zai ga karshen kabilancinta, zai gani idan ubanta ne ya wanzar da hausa bakwai da banza bakwai. Malaman kowa na tofa albarkacin bakinsa akan kabilancin ‘yan arewa ga ‘yan kabilar Yoruba, da yawa ana samun hakan, wanda ko kadan bashi da amfani musamman ga yara masu tasowa ana saka musu wani nagetive tunani daban a ransu akan kabilar Yarbawa. Kamar su din wata halitta ne daban da hausawa da Fulani. Ko Hausa/Fulani din sun fisu wata martaba ne. Aisha ta iso sumui-sumui da ita don tasan kiran Malam Sayyadi ba alheri bane, ganin Bisola a gefensa tana kuka yasa ta gane kwabarta tayi ruwa yau, wato yau Bisola ta kai kararta, ai kuwa nan da nan cikinta ya duri ruwa. Aisha da Bisola suka gurfana gaban Discipline Master, kan Aisha a sadde da ganinta kaga maras gaskiya. Discipline Master ya daka mata tsawa yace “maimaita tsokanar da kike mata kullum a kunnen mu muji, isashshiya diyar barbushe da tsimbirbira”. Aisha tayi narai-narai da sexy eyes dinta akan malamin bafillacen, wadannan idanun na Aisha masu kama da hawaye ne fal ya taru a cikinsu, shi kansa Discipline Master din sai da ya kauda kai sabida kwarjinin idanun Siddiqah, ya taba cewa wani Teacher dan uwansa mai suna Malam Tafida ya daina kallonta, Malam Tafida yace shima bai san meyasa yake yawan kallonta ba, Uncle Sayyadi yace da Malam Tafida cikin takaici, “yarinyar nan in ka cika kallon ta musamman wadannan maganadisun idanun nata alwala bazata zauna a jikinka ba”. Bai manta dariyar da malam Tafida yayi ta yi ba a ranar, to yau ma hakan ce ta
🏠