NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 32 of 44

e yake gudun mata tun zamanin samartakarsa? Ta dade bata kara jin komai game da Hasinah din ba. Ko daga bakin aminiyarta uwar dakinta (Taiwo) bata kara jin zancenta ba. Wacce a baya kullum suka hadu bata da aiki sai lallashin Nenne ta barshi ya auri Haseenah. A lokacin AbdulRasheed ya koma ya jingina da filo a jikin gadon jinyarsa, ya runtse idonsa a hankali yana motsa hannunsa na dama kadan da aka kwance daga daurin karaya. A can kasan zuciyarsa magana yake shikadai wadda baisan tana fita a fatar bakinsa ba, tana shiga kunnen mahaifiyarsa. “I am now a hopeless romantic. I want an idealist (true love)”. Wanda ya riga yayi amanna da cewa babu shi sam-sam a zamanin yanzu. Babu irin soyayyar da yake burin samu! Domin y agama yardarwa kansa a wannan qarnin da muke ciki, wani qarni ne da mafi yawan mata suka daina soyayya irin wadda yake buri ta domin Allah, ba don komai ba sai don zukatansu sun zarme da kwadayi da son rayuwar duniya da ta wuce kima, hakan yasa suka zama insatiable ga mazan da Allah ya basu masu yi musu kauna ta gaskiya, suka maida kawunansu sex slaves to rich men (sun zamar da kansu bayin biyan bukatar gangar jikin maza masu kudi ko mulki, soyayya ta hakika ta gushe a zukatan mata. Engnr. Abdurasheed ya kara kishingida sosai yana cigaba da cewa da kansa da kansa. “I am a hopeless romantic. I want true love!”. (Karin haske). “Prince AbdulRasheed (Kehinde) Idrees Akanni, yana nufin ya riga ya yardarwa kansa cewa babu soyayya ta gaskiya, true love is hard to find, or does not exist at all, matan yanzu duka are incapable of that...!”. **** **** **** Ba jimawa saboda irin kulawar da yake samu ya karasa warwarewa, aka sallamesu. Suka koma gidansa. A wannan dan zaman jinyar da Nenne Sappa tayi na dan ta Prince AbdulRasheed Kehinde, a kasar Argentina, ya basu damar samun shakuwa da wani irin kusanci da juna na uwa da data wada y agama mallakar hnkalinsa amma still yana bukatar kulawar Nenne da zamanta a gefensa, shekaru da yawa basu samu damar zama tare na lokaci mai tsaho irin haka ba, saboda yawace-yawacensa na Polo a duniya. Nenne ce ke dafa masa duk abinda zaya ci da kanta kullum, wanda shi da kansa yake zabar abinda zata dafa masa, haka take saka shi a gaba sai ya ci sosai, sannan ta tabbatar da ya sha magungunansa akan kari, wanda take barowa da hannunta akan farin tafin hannunta ta zuba ruwa a tambulan mai garai-garai ta bashi ya hadiya akan idonta don Abdurasheed baya son kwayar magani sai akan idon Nenne don baya son abinda zai bata mata rai tun yana yaro. Saida AbulRashid ya warke ragas har ya fara shirin komawa wajen aikinsa a Qatar sannan sukayi sallama shi da Nenne da ‘yar uwarsa Fatima, Taiwo ta tabbatar masa zata sameshi a Qatar in ta samu leave ta ga jikin nasa. Sun kwana hira shi da Nenne yau, zancen da baya so ko kankani a yi masa wato zancen aure itama tana avoiding dinsa yanzu, don bata son ganin yanayin tashin hankalin da yake fadawa a duk lokacin da tayi subutar bakin yi masa zancen aure. Su Nenne zasu koma Lagos a washegari, don lokacin tafiyar Nenne aikin Hajj na wannan shekarar ya kusa. Sun tashi zuwa Lagos da kwanaki biyu, shikuma ya tashi zuwa Qatar inda ya koma bakin aikinsa cikin koshin lafiya. **** **** **** FGC BILLIRI, GOMBE “ Yarbawa masu kwalo-kwalo, da Duwawu kuke tukin tuwo!!!”. Bisola ta kauda kai bata kula ta ba, ta ci gaba da tukin Teba da take yi da ludayin karfe a cikin robar cin abincinta mai fadi. Wannan duk bai ishi siririyar yarinyar ba mai siririn hanci da manyan idanu masu walainiya, hakoranta yiri-yiri farare kal kamar kankara, ta sake leka fuskar Bisola cikin matukar tsokana da iblisanci irin na ‘yammata ‘yan makarantar kwana da aka fi sani da teenagers. “Nace ko ba ku bane? Yarbawa masu kashi a kwano?!” Jikake kyal-kyal-kyal. Yaran dakin da duka ‘yammata ne masu tashen balaga wadanda a shekaru basu fice shekaru 15 zuwa 16 ba, in sun yi da yawa 17, dukkansu sun kara kyalkyalewa da dariyar shakiyanci da shegantaka (mockery). Karo na sau ba adadi da AISHATU-SIDDIQAH YUNUS tasa Bisola Akanbi kuka, sanadin wannan wakar da irin wannan cin zarafin da take mata a gaban sauran yara tsararrakinsu da suke kwana daki daya. Ko a aji ko a filin wasa ko a hostel kai har a masallaci in taga Bisola sai ta mata irin wannan tsokanar. Sauran daliban kuma, wadanda suke gang din Aisha duk sanda Aisha ta fara yima Bisola wannan wakar ta shakiyanci wadda take yi tana juya siririn kwankwasonta (irin dai na yadda yarbawa ke juya mazaunansu) wanda baya wani motsawa sabida sirantarta sai sun daddage sun barke da dariya. Ba Bisola ce take basu dariya ba, karewa ma tausayi take basu, sabida yadda Aisha ta matsa mata, ita Aishar ce take basu dariya yadda take daddagewa tana juya kwankwaso da ‘yan mazaunanta da sunan kwaikwayon tukin tuwo ko Tebar Yarbawa, alhalin kwankwason nata d
🏠