NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 31 of 44

fito sabida yadda take hawa da sauka don bacin rai….. Ya dade bai shiga bacin rai irin na yau ba sakamakon wannan dogon tunanin da yayi. Ita da kanta Nenne ta lura da halin canjin mood da kalamanta suka jefa dan ta Prince AbdulRasheed, sai taji wani irin babu dadi a zuciyarta da kasan ranta. Ita ta san Abdulrashid dinta is always bold and smart fiyeda Taiwo, kasancewarta mace tanada saurin nuna rauni (sai karambani da rawar kai da shiga sharo ba shanu), but today he looks pale har fiyeda Taiwo uwar kankanba idan ta raunana. A ganinsa tunda har uwar data haifeshi ma ta fara yarda da zargin da duniya ke masa na cewa wai (he is gay), don kawai yana rayuwa a cikin turawan yamma, kuma yana practicing wasansu na tseren Doki a matsayin sha’awar ransa kuma sana’a mai girma, hujjar kowa ta makala masa wannan zargin shine kawai don ya ki yarda yayi aure ko kawo mace gidansa da sunan matarsa? Zargi wani abu ne mai girma da muni a musulunci balle zargi irin wanda duniya ke masa. Auren ai Sunnah ne ba farillah ba tunda Alhamdulillah yana iya rike kansa ta hanyoyin da addini ya koyar. Kusan kullum baka Abdulrasheed da azumin litinin da alhamis a bakinsa, baya kallon haramun, balle kai kansa inda ake aikatata, he is always busy planning and scheduling his Polo time-tables across the globe da tsara ayyukansa na Consultation a matatar man fetur a (Qatar refinery). Zina ai sai mutum ya bata kafa take shigowa rayuwarsa. Ga kuma addu’ar tsayayyyar Uwa irin Nenne Sappa a kansa kullum wadda zamu iya cewa itace babban makamin dake katange Abdulrasheed ga ayyukan sabo in akayi la’akari da yanayin rayuwar ‘yan Polo. Duk da cewa Nenne ta yi dana sanin furta masa damuwarta, amma kuma hakan ya taimakawa zuciyarta, yanayin da ya shiga kadai yasa ta rage tasirin zargin na mutane daga ranta akan dan nata, ko daga irin halin rudu da damuwar da ya shiga akan maganar kadai ta gane ba haka bane, zargi ne mai muni ake masa da shaci-fadin mutane da basu da gadon ka sai gadon magana akan ka. Ita kawai tayi la’akari ne da fadar nan ta hausawa dake cewa “ka haifi Da, amma baka haifi halinshi ba” kuma akace wai “ba’a shaidar ‘ya’yan yau”, da kuma yadda kana tufka a matsayinka na uwa; modern society da influence na ilmin zamani na warware maka tufkar ta baya, musamman shi AbdulRasheed da in akayi la’akari da irin ‘life-style’ dinsa, wato yanayin rayuwarsa da yadda yake gudanar da ita gabadaya kome aka ce akansa al’umma bazata musa ba. “To me ya hanaka aure har yau Kehinde? Na roke ka da girman Allah yau ka gayamin. Ni mahaifiyarka ce da baka da wanda ya fini ba kuma wadda zata rufa asirinka a duniya irina. Shin idan baka sanar dani hakikanin matsalarka ba, wa zaka sanarwa a duniyarnan?” Zuwa lokacin ya soma dawowa cikin hayyacinsa, amma maimakon ya baiwa Nenne amsar data dace da tambayar data yi masa, wato menene hakikanin abinda yasa ko zancen aure baya kaunar a yi masa? Sai ya bige da maida zancen wani kala daban, don Nenne ta bar zancen, don har gobe babu wanda ya san abinda Adetokumbo yayi masa kaf cikin zuri’ar su, daga shi sai shi Tokumbon, sai kuma Taiwo, sai ita shaidaniyar HASINAH! Da bai san a wace duniyar take yanzu ba. Sai kuma Allah da ya haliccesu. Zai kuma cigaba da barin wannan zancen a ransa yana haunting dinsa shikadai ba tareda ya gayawa wani a danginsu ko iyayensu ba bayan Taiwo, albarkacin zumuncin Akanni’s da hadin kan gidansu. Yau ace wani cikin zuri’ar Emir Abdulrasheed Akanni yana zina da macen da ba tasa bama abu ne da zai taba mutuncin su bakidaya, abun kunya ne ba karami ba, ga zuri’ar sarki Abdulrasheed Abdullateef Akanni a idon talakawansu dake ganin martabarsu da girman nasabarsu, wanda zai iya lalata hadin kan gidansu gabadaya wanda gida ne ko kuwa zuri’a ce data zamo abun buga misali a ciki da wajen jihar Ilorin. Sai ya maida abun zolaya ga Nenne, bayan ya maida murmushi mai sanyi akan fuskarsa, Prince ya soma magana cikin lallashin mahaifiyarsa. “To yanzu Nenne, ki gayamin saboda Allah, duk fadin Najeriya wacece kike ganin zata aureni da tsillin furfura kamar yadda Fatima tace, umh? Ta kuma kaunace ni da furfurar nikadai ba tare data hada soyayyata data wani na ba? Ba kuma don abin duniya da reputation dina (shaharata) a kan wasan Polo ba, soyayya pure nake nufi tsarkakakkiya ta saboda Allah! A dai yawan shekaru irin nawa, wadanda babu sauran kuruciya a cikinsu yanzu? Believe me Nenne, duk matan zamanin nan, ina fade ina karawa kullum (are nothing but gold-diggers) sannan karnukane babu daraja a tare dasu. Daga kan HASINAH AMBURSA… na gama rufe babin mata Nenne, (they just want money over pure LOVE), don haka basa gabana gabadayansu Nenne, har abada babu ni babu ‘ya’ya mata”. Nenne sai ta bishi da ido zuruuu! Ta kasa gane inda zantukansa suka dosa. Me Hasinan da ta san yanaso kamar ya cire ransa ya bata tayi masa da ya karya zuciyarsa haka? Ashe a kanta n
🏠