NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 30 of 44

raduate, soyayya ta gaskiya ba irin wadda bai yi mata ba, har da ta kauce hanya, domin ta saka shi ya danyi deviating daga tarbiyyar da Nennensa ta bashi, duk don ya faranta ma fiancée dinsa Hasinah ya kuma katangeta daga sha’war wasu mazan ba don yana so ba. A dalilin ganewa da yayi cewa ta soma wayewa da irin wannan rayuwar da tazo ta tarar ‘yammata da samari kamarta nayi a jami’a, lokacin da ya fahimci ita din mai son wannan rayuwar ce sai ya biye mata, bisa dalilai guda biyu; na farko son da yake mata, na biyu tsoron shi na kada ta kwadaici wani, idan shi din yaki biye mata. Da wannan Hasinah ta dulmiyar dashi a baya cikin rayuwar soyayyar shan minti, kazamar rayuwar da ’yammata irinta ke yi a turai, rayuwa ta rashin tarbiyya da baya ko son tunawa yayi da Hasinah yanzu. Duk da haka a kullum yana godewa Allah da bai taba sanin Haseenah diya mace ba (as in having sex) bai taba ba. Sai abinda ba’a rasa ba bisa jagorancinta. Amma duk da soyayyar shan mintin da ya biye mata suka soma ba don yana jin dadin afkuwar hakan ba, saboda a irin son da yake ma Hasinah yafi so ko meye zai shiga tsakanin su sai ya mallaketa ta hanyar aure, amma ta nuna ita bazata iya jira har zuwa wannan lokacin da Nenne zata amince da maganarta ba, dole ya biye mata suke kananan abubuwan da har ransa baya so. Don kuwa mace duk inda take komai kankantarta shaidaniya ce, balle shaidancin Hasinah mai license ne tunda ‘yar kwararo ce, amma duk da hakan biyemata din domin ya katangeta bai sa ya iya ya rike sha’awarta da hangenta da kwadayinta na abinda shi har lokacin ya kasa yi mata ba, saboda addu’ar Uwa ta dare da rana dake tasiri a kansa, ya kasa rike sha’awar Hasinah daga sauran mazan da basu kaishi komai ba. Amma a bukatun rayuwarta kam na yau da gobe baya jin ya gaza, sai dai don ta kasance mai son bushasha da sha’awar rayuwar kere sa’a. By Allah! Yayi duk wata bajinta da namiji kamarsa mai gata da asali da nasaba tsarkakakkiya ta sarauta da ilmi mai zurfi da malanta bazai yi akan matar da ya tsinto a kwararon gidan marayu ba! Bayan duk wannan wane irin sakamako ya samu a mahaukacin son nan kuma gurbatacce da yayiwa Hasinah??? Prince ya runtse ido da karfi, yana tuna Hasinah a ranar, da kazantaccen yanayin da yazo ya samesu ba zato, mantuwa yayi ya dawo, abin mamaki tareda kaninsa Adetokumbo Abdulfatahi Akanni, the worst part dinma kuma a dakinsa sannan a kan gadonsa. Saboda kawai Abdulfatahi ya fishi kudi, ya fishi iya shege ya fishi rashin tsoron Allah, uwa uba yanada ra’ayin yin bushashar arzikinsa ga matan banzan duk da zasu bashi jikinsu, don a lokacin shi Abdulfatahi wani babban Automobile Business Mogul ne, kasancewar a tsakanin Japan da Spain yake harkar shigo da motocinsa, to duk sanda ya shigo Tokyo a wajen dan uwansa Prince Abdulrasheed yake sauka, baya sauka a hotel, kuma ta haka ne ya san Hasinah a matsayin fiancée din dan uwansa, har suka saba shi da ita suna tsokanar juna irin dai wasan nan na kanin miji da wadda Yayansa zai aura. Yaya akayi-yaya akayi suka sarke a bayan idonsa kuma bai taba gane komai a tsakaninsu ba banda sani da yayi tun fila azal Hasinah mai dogon buri ce, mai kwadayi ce, mai son kyale-kyalen mata na fita tsara ce wato (Hasinah is a designer baby) sannan yana ankare da cewa tana son wannan harkar, a hakan kuma yana iya bakin kokarinsa akanta, don ganin bata rasa komai take bukata ba, kusan duk abinda iyayensa ke aiko masa a matsayinsa na dalibi a lokacin akan bukatun Hasinah masu dan Karen tsada yake karar dasu da kwalliyarta na sittiru tsadaddu, da kayan kawa da khyale-khyale ba tareda Nenne ta sani ba. Ko dama ita Nenne from day one, Hasinan bata kwanta mata ba tunda aka ce a gidan marayu aka daukota, tun a lokacin Nenne tace “NASABA” wato tsatso, wani abu ce mai girma da muhimmanci a neman aure to amma Hasinah fa? Suwa zata bugi kirji ta kira Kakannin jikokinta na wajen uwa na jikin Abdulrasheed Kehinde? Shikuma har a lokacin lallaba Nenne yake yi akan ta yarda ta karbi Hasinah a matsayin surukarta, ita kadai zuciyarsa keso, ita yake yiwa kauna ta saboda Allah ba zai iya auren kowacce mace in ba itaba. Shi ya bata surname da Bello Ambursa lokacin da zai shigar da ita makaranta, sunan abokinsa Bello da ya rasu. Sakamakon da ya samu a duk wannan sadaukarwar da yayiwa Hasinah shine Hasinah ta bige da cin amanarsa, itada dan uwansa mafi kusanci dashi, mafi kazantar cin amana har a gadon barcinsa kuma a gidansa. A cire maganar girman zina wadda lahani ce mai girma ga martabar diya mace. Abin ya kara dawo masa sabo. Kamar yanzu-yanzu ya faru. Shekaru goma sha hudu kenan da faruwar al’amarin a can baya, amma kullum sabo scene din yake koma masa a idanu da zuciyarsa, in ya tuna ko aka yi masa fadan yin aure ko ya kamata ya zabi matar aure a family dinshi. Nan da nan jikin sa ya hau tsuma, zazzabi mai zafi ya rufe shi, makwallatonsa na kaiwa da komowa, zuciyarsa kamar ta hudo kirjinsa ta
🏠