hi, tace “Kikinshi” ko “Kikinsa”.
A lokuta da yawa idan ana hirarsa, kasancewarsa ‘Polo Celebrity’ ne, ‘yar uwarsa Murjanatu data fi kowa kusanci dashi ta kan gayawa kawayenta daliban LUTH, musamman wadanda ke bibiyar kallon wasan shi a kafar talbijin ta “Global POLO TV, suke kuma mayatar son jin wani abu da ya shafeshi personally, Taiwo kan basu labarin irin son yaransa ne, ta kan ce da dai ace maza na haihuwa da kansu, ba mata ke haifa musu ba, da tasan shi zai yi nakudar Kiki ya haifeta, wato da bazai bar mata ta haifota ba, saidai shi da kansa, saboda sonda yake mata a matsayin karamar diyar ‘yar uwarsa, wadda duk duniya bashi da makusanci, amini, amar ita ‘yar uwarsa Taiwo. Ya sha gaya mata cewa ya raina adadin kulawar da take baiwa Kiki, tunda har ta zabi karatun likitanci akan zaman gida ta kula da kyautar ‘ya’ya biyun da Allah ya bata.
Tana basu labarin irin yadda yake bata lokacinsa in yana gaban Kiki, don mayar da shekarunsa yake daidai da nata, su taru suyi ta zuba shirme na (Daddy and Daughters’ love).
Wani lokacin Taiwo har addu’a take yi tace Allah ya bashi nashi ‘ya’yan shima. Saboda son yaran shi har yaso yayi yawa.
Tana matukar marmarin ganin yaranshi, ko ba don komai ba don ta taya shi son su, irin dai yadda yake tayata son Kikin data haifa.
Murjanatu kullum addu’arta kada Allah ya baiwa dan uwanta matar da zata raba soyayyar shinnan da ‘yarsa Kiki. Don ko ubanta Toafeeq albarka.
“Kiki rigimammiya amanar Uncle dinta “Prince!”.
Wakar da Aunty Taiwo ke yawan yi mata kenan, wadda ainahin sunan Kikin na yanka (Ruqayyat). To amma tana ji tana gani ala dole Prince ya mayar mata da sunan diya “Kiki”, wai a cewarsa saboda kibar ta, da kazarniyarta, da rikicinta irin dai na yara lukutaye ‘yan shekaru uku, yace Kiki ne ya dace da ita ba sunan Nanin Gombe ba. don kam ita Kakarsu Nani Oummana bata da rikici kona tsufa, balle irin na Kiki.
Murjanatu na tafe ne tana tuki take wannan tunanin na dan uwan haihuwar nata, mafi soyuwa a ranta a duk cikin ‘yan uwanta da suke iyaye guda, kuma namiji daya tal a cikinsu. Gabadaya gidansu tafi shiri dashi watau shi Hussaininta, wanda suka zo duniya a tare, ta tuna ya hanata barin Kiki a gun masu raino, ba sau daya ba ba sau biyu ba, to amma yaya zata yi tunda ta saka ma ranta son zama likitar mata kota halin kaka?
Shi, a matsayinsa na (lifetime) dan “Polo” ba zai taba gane hidimar aikin asibiti bata haduwa data kananan yara ba, dole sai da taimakon mai raino da raba hankali gida biyu, da kuma taimakon makarantar nursery ne kadai kowannensu zai samu isashshen lokacinta. Kuma dai tayi sa’ar samun Bunmi wato mai rainon Kiki yarinyar kirki ce, bata da matsalar komai sannan gata musulma don kuwa daga Ilorin ta taho da ita, tana kula mata da Kiki sosai.
A yadda Prince yake son niece din nashi Kiki, wadda ainahi soyayyarsa da yarinyar ta samo asali ne daga sunan Kakarsu da taci wato Nanin Gombe Hajiya Ruqayya da suke kira (Nani Ummana), Taiwo ta tabbata da ace zata bashi ita ya rike a inda yake zaune, ta san tsaf zai karba babu musu, zai iya aje hidimomin Polo dinsa na wasu lokutan, ya zauna ya kula da Kiki da kansa sabanin ita, tunda gidansa babu mace har yau har gobe, amma kuma hakan bai hana shi kwadayin ta bashi rikon Ruqayyatu-Kiki ba.
Fatanta dai yanzu shine Allah ya taimakesu iyayensu wato “Nenne” da “Dade” su amince da maganar marainiya Haseenah, dan uwanta ya samu abokiyar rayuwa, yayi settling rayuwar iyali hakanan (at the age of 30) kamar kowanne lafiyayyen matashi.
Ita tasan ba wani uzuri da zata baima dan uwanta ya karba akan cewa kulawar da take yima Kiki tayi kadan, a wurinsa Kiki tafi karatun nata muhimmanci dari bisa dari don shi bai ga dalilin da Murjanatu zata ce sai tayi aikin likita ba.
Watakila ko don yana ‘life-time’ dan Polo ne yasa yake ganin kowanne Profession na duniya wahala ne, sannan takurawa kai ne, kuma babu riba a cikinsa banda Polo Sport, don ko tabbataccen aikinsa na man fetur an shaida, baya baiwa muhimmancin da ya baima wasan Polo dinsa.
A cewar Murjanatu ita kuma, karatun data zaba take yi na kishin kasa ne, bashi da alaqa da matsayin gidansu, reputation na gidansu ko na mijinta Toufeeq Adebayo. Sarauta bazata hanata yunkurin kokarin amfanar da al’umma ba ko neman abinci ta hanyar ilminta, don kuwa sun kere ma hakan. Taimakon kasarta takeso ta yi da nata dan effort din (with full patriotism) sabida karancin likitoci mata da ake dasu a kasarta, tunda kuwa gwamnati take da burin yiwa aiki da mata ‘yan uwanta ba private ba a ganinta aikinta mai hujja ne babba ba karama ba ko a cikin addini. Har ila yau, bazai hanata hidimar iyali ba.
Bayan kasancewarsu ‘ya’yan sarauta mai suna sarauta data amsa sunanta, sarauta irin ta gado bata taka-haye ba, kuma jikokin manyan sarakuna gaba da baya, maigidanta Toufeeq Adebayo, har ila yau, ma’aikacin majalisar hadin kan turai ne (European Union