NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 29 of 44

nar yau daga bakin mahaifiyarsa shine babban abinda yafi tada hankalinsa. Amma ko kadan babu tashin hankalin maganar akan fuskarsa sai tsantsar damuwa da yanayin da mahaifiyarsa ke ciki. Abdulrasheed yace (cikin despair). “Nenne in kowa zai min wannan mummunan zargin ke UWATA (mahaifiya) ya kamata ki kyautata min zato. Ban taba zaton Nenne ranki zai yi bacin da zakiyi duba da wannan banzan zargin na mutane marar tushe da hujja ba, tunda kin san irin tarbiyyar da kika yi mun da hannunki, ba wani ya tarbiyyantar miki ni ba, kuma kinada tabbaci a kan ingancinta, na cewa ko bayan ranki bazan zubar da ita ba, balle da ranki da lafiyarki in yi wannan mummunan aiki. Anyway, bazan musa ko daya ba, cikin abubuwan da ake zargina dasu din. Allah ne kadai ya san zahiri da badinin zuciyar bayinSa, da abinda suke aikatawa na fili dana boye, kuma shaidarsa nake nema bata mutane ba Nenne, tunda ke kanki da kika haifeni kin kasa shaidata….…”. Yayi shiru, ya koma ya kwanta yana maida numfarfashi da sauri da sauri kamar mai ciwon asthma. A hankali AbdulRasheed ya rufe idanunsa…. Mummunan ‘scene’ din na Hasinah da dan uwansa kuma wanda ya rika a matsayin “amini” duk cikin family dinsu Adetokumbo akan gadonsa na gilma masa. Abinda ya faru kusan shekaru goma sha hudu a baya, amma har yau yake ‘haunting’ dinsa… ‘trauma’ din abun ya kasa barin ransa ya huta, zuciyarsa ta sake da mata. Cousin dinsa Adetokumbo Abdulfatahi Akanni da fiancée dinsa Hasinah Ambursa turmi da tabarya, kuma a kan gadonsa sannan a dakinsa mallakinsa a gidansa dake kasar Japan. Wani ‘incidence’ ne da kullum yake komawa ‘GREEN’ a idanunsa… ya kasa barin duhun idanunsa su huta ko hasken wata mace ya ratsa ta cikinsu. Shikuwa me zaiyi da mata yanzu? Ai ya dade da rufe babinsu daga kan Hasinah Bello Ambursa. A cewarsa dukkansu are nothing but ‘Gold-Diggers’, wadanda in dai namiji zai basu kudi to ya gama samun mutuncinsu, kowanne kare da kowanne doki ma yazo ya fanshi mutuncinsu da diyaucinsu in dai yana da kudi. A tasa mummunar fahimtar da ya dade da yiwa mata daga kan Hasinah, wadda ta dade da yin babakere a zuciyarsa ya gama yardarwa kansa duk matan yanzu irin Hasinah ne, masu son holewa ta jiki data aljihu, ya yarda mafi akasarinsu namiji daya ba zai taba isarsu ba, batare da sun zagaya sun ci amanarsa ba ko me zai musu na halacci kuwa, ko me zai basu iya karfinsa don kula da lalurorinsu, kuma koda zai yagi naman jikinsa ya basu bazai hana su hango wanda ya fishi samu ba, they are totally greedy, rashin wadatar zuci ya yiwa zakatan ‘yammatan yanzu katutu, babu soyayya ta saboda Allah a zuciyarsu yanzu. Shiyasa yake ganin bashida mata a duniya, ba’a haifi macen da zai kara gangancin so ba, bazai kara yarda da mace a duniya da sunan soyayya ba in ka cire soyayyar da yake yiwa Nennensa da ‘yan uwansa mata. Bai ki ba dai a gidan aljannah in yana da rabo. Me yasa mostly kyawawan mata kamar Hasinah ne kullum suke yin dage, domin hango wani wanda bai kama kafar mijin da Allah ya basu a komai ba? Marasa shararren kyau zaka samu basu cika dage ba. Me ya rasa da Da namiji ya rasa daya cancanci abinda Hasinah tayi masa? Me Tokumbo zai nuna masa banda cikar aljihu a lokacin? Idan har aljihun wani namiji dan uwansa ne zai sa Hasinah yi masa haka, to kuwa duk matan duniya ya dade da yi musu jimilla da ‘gold-diggers’, kwadayayyu, hadamammu, ma’abota manta halaccin mai halacci, wadanda burinsu kawai namijin da zai basu kudi suyi bushasha, ba wanda zai so su saboda Allah ba, kuma wanda zai kwatanta irin soyayyar da suke so ta banza da da sunan itace soyayyar da zata bulle dasu, koda kuwa ace babu abinda Allah ya rage ka dashi a rayuwa. Ya rasa wane irin jin dadi mata ke nema a wurin namiji fiyeda daya. Shi kuma Allah da ya halicceshi yayi shi mai matukar kishin kansa da kishin macen da yake so, watakila shine dalilin da yasa daga kan Hasinah ya daina sha’awar kowacce mace sai Polo dinsa, yanada kishin kansa fiyeda yadda harshe zai iya bayyanawa! Nenne ta rainesu akan turbar tsoron Ubangiji, tana tare dasu ko bata tare dasu suna tuna Allah, ta rigada ta dorasu akan turbar gujema ketare iyakokinSa. In aka duba kuma, a rayuwa ba abinda bai yiwa Hasinah ba, a matsayinta na wadda yaso aure da dukkan zuciyarsa ba tareda tunanin banbancin nasabarsa da tata ba, kuma marainiyar da ya fiddo daga gidan marayu, ya maidata daliba mai ‘yancin higher education, ta hanyar sponsoring karatunta daga gidan marayu zuwa Lagos eventually zuwa kasar Japan ba tareda sanin kowa nasa ba bayan Taiwo. Bayana fara karatunta na jami’a ya zama shine uwarta shine ubanta a Tokyo, shine cinta shine shanta, shine sutturarta da duk wani shopping dinta duk don ya katangeta daga neman wani abu ta rasa a rayuwarta duk da shima a lokacin ya dogara ne da abinda Kakanshi ke turo masa duk wata, da na mahaifinsa, a matsayinsa na dalibin postg
🏠