, shi nasa ciwon bai daga hankalinsa ba kamar lafiyar SAHEEB dinsa.
**** **** ****
Zaman jinyar Nenne da Fatima tare da AbdulRasheed a asibiti, ya taimaka matuka gaya wajen samun lafiyarsa da wuri, sakamakon addu’o’I na (Ayatushshifa) da Nenne takeyi kullum a ruwa tana bashi yana sha dare da rana, da kuma dorewar lafiya da take roka masa a duk bayan kowacce sallahr farillarta.
Ya fara jin sauki sosai cikin ‘yan kwanaki kalilan, har yana tashi ya zauna yayi sallah daga zaune, bakin Nenne baya hutawa da yi masa nasiha akan bin Allah da tunasar dashi soyayyar Manzonsa, saidai in basu kadaice a dakin jinyar ba.
Har ila yau Nenne bata gushe ba da nasiha sannan bata fasa ba. A kullum bata gajiya wajen nuna masa muhimmancin aure da ajiye iyali ga faein ciki da cigaban rayuwarshi, cikin nasiha da lumana, ta kan ce masa ‘ya’ya sune gatan bawa duk arzikinsa, tunda su zasu dinga yi masa addu’a a bayan ransa. Kuma su tsaya masa a sanda yake bukatar su.
Auren kuma da yakewa kallo na daban Nenne tana kokari wajen nuna masa cewa ibadah ne ba son rai bane.
Koma meye dalilinsa na gudun yinsa bai isa dalili a wurin Ubangiji ba, tunda dai ya bashi lafiya da abinda lafiya zata amfana.
Tace ana yinsa ko ba’a so domin katange kai daga sabon Allah da tsarkake kai daga daudar zinah da katange zuciya daga sha’awar aikata sabo kowanne iri ne.
Wadannan sune ire-iren kalaman Nenne Sappa ga danta Prince Abdulrasheed lokacin jinyarshi. Princess Fatima kuma ita ke bashi abinci a baki da cokali.
Yau daya gama cin abincin rana, Princess Fatima tana gyara masa filon da zai kishingida ta bayansa, a cikin tarin sumar kansa sai ta hango tsillin ‘furfura’ a cikin gashin kansa. Ta kai waje guda 20 a cikin lallausar sumar kansa, ta kuwa ce me zata yi ba sakin shakiyyar dariya ba.
Princess Fatima tasa hannu ta tsigo furfura guda daya daga saman kansa, tana dariya tana kanne ido ta nunawa Nenne, tana fadi cikin yanayi na (banter) harda neman sikewa don dariya,
“someone has finished, ooh my Dear! Getting white hair before even getting a first wife…
Nenne furfura ce fal! A kan Hamma!”. (Ta kara gishiri).
To ma yanzu sabida Allah Nenne, wacece zata yarda ta auri mutum over 40 kansa duk yaci furfura?
Ai saidai kwantan ‘yammata kamarsa dan (mid forties), irin bazawara mai ‘ya’ya biyu haka, ko widow (wadda miji ya mutu ya barta) haka dai, amma ba dai (sweet 16) ba!”.
Nenne an sosa mata inda yake mata kaikai, sai ta gyada kai tace “in ya samu sweet 16 din sai ki hana ruwa gudu! Furfura baiwa ce ‘yar nan, ba itace tsufan namiji ba, wani ma sai ya fara ta yake fara jin mazantaka da karfin samartaka, rashin aure haka kawai babu dalili shine mishkilarsa, domin tamkar izgili ne ga rahamomin da Ubangiji yayi maka Abdulrasheed.
Saidai kuma bansani ba ko abinda mutane suke fadi marar dadi a kanka din, ko gaskiyane Abdulrasheed?”
Yanayin fitar sautin muryar Nenne, a halin yanzu ya nuna helplessness din da take ciki akan situation din, wanda hakan yayi matukar karya zuciyarsa, jikinsa yayi sanyi matuka, amma dai bai yi magana ba.
Princess Fatima, ganin yanayin da suka shiga na damuwa su duka, sai ta dauki ipad dinta ta bar musu dakin, ta koma can reception na asibitin ta samu kujera ta zauna tayi tagumi itama, don taga zancen na Uwa da Danta ne, kuma yau raunin Nenne da bakin cikin ta na shekara da shekaru akan rashin aurensa yafi na kowacce rana bayyana a tare da ita da nauyin shekarunta da suka bayyana kan kyakkyawar fuskarta yau saboda damuwa.
Wai AbdulRasheed ya fara furfura ba aure!!!
Wannan al’amari ya tsorata Hajiya Sappa matukar tsoratawa.
Fitar Princess Fatima keda wuya, sai ga hawaye mai kauri ya tsinke a fuskar Nenne Sappa. Kamar jira take Fatima ta gusa.
Hankalin AbdulRasheed yayi tashin da bai taba yi ba yau, ba yau Nenne ta soma korafi da kuka akan rashin aurensa ba, amma na yau yafi na kullum daga hankalinsa ko mai yasa? Don ya ga bakin cikinta muraran a idanunta.
Abdulrasheed ya shiga rokon Nenne cikin kaskantar da kai, akan ta gaya masa menene exactly damuwarta har haka akan rashin aurensa, take irin wannan zafafan hawayen dalilinsa, masu barazanar tarwatsa rayuwarsa?
“Zubar hawayenki a kaina Nenne masifa ne a gareni kin sani”.
Nenne Sappa saida ta yi sharbe son ranta, tana gogewa da habar hijab dinta. Kafin ta soma Magana cikin rauni da karaya.
“Na soma zama cikin zargi mai girma a kanka nima!
Na soma yarda da zargin da duniya ke maka, na cewa neman maza ‘yan uwanka kake yi (you are gay) shine abinda yasa ka juyawa auren Sunnahr Ma’aiki SAW baya. Haka ne ko ba haka bane Kehinde?”
Nenne ta tsatstsareshi da jikakkun manyan idannunta da suka rine kamar garwashi suke jike shatab da hawaye mai yawa.
Ko kadan babu firgita kan kalamanta a tare da shi, ko don ba yau ya fara jin ana zarginsa da hakan ba? Jin maga