NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 25 of 44

hannu mai albarka, hannun Kakansa Sarki AbdulRasheed Akanni. Playing Polo has been the hobby of his life. Ya sha cin kofin zinare a wasan ‘polo’ a ciki da waje, a garuruwa daban-daban na kasashen duniya. Don haka wannan faduwar bazata da ta faru yau da Prince, ba ‘yan Africa kadai masoya Prince ta dagawa hankali ba, har dasu Turawan na Ajantina, wato (host country) na wasan da ake gudanarwa, da mahukunta gasar na kasar ta Argentina. Wani hamshakin asibiti mai zaman kansa aka kai Prince AbdulRasheed yake zaman jinya a can ba nisa da gidansa. Zaka yi mamaki in kaji cewa, duka raununnukan nan da yaji a jikin sa, har da karaya a kafa da hannu, sabida ba karamin faduwa yayi ba, domin Dokinnan sai da ya wulwula shi a sama sannan ya tika shi da kasa, amma raunukan nan basu dame shi ba, haka zugin ciwon su bai dami Prince Abdulrasheed ba, kamar subucewar kofin gasar nan, na ‘champion’ din duniya a POLO daga hannunsa.…. Wanda da wannan tsautsayin bai faru ba, ya saka ran zai kai shi ga attaining 10+ goal polo handicap (highest rank of the world’s polo player). **** **** **** BANANA ISLAND, LAGOS P rincess Fatima, ta shigo da dan saurinta tana cewa da mahaifiyarsu Hajiya Sappa. “Ni me ya faru da kunnen Nenne na ne? Anata kiran ki a waya tun dazu kina kallonta ido hudu amma dagawa ta gagara, halan baki ji kiraye-kirayen bama Nenne? Tun daga falo nake jiyo ringing din wayarki ba kakkautawa. Nenne meke damunki haka yau? Tun safe nake ganinki haka sukuku (moody) cikin tagumi da damuwarnan, duk kin birkice”. Princess Fatima, ta karasa shigowa dakin na mahaifiyar su cikin shiga ta alfarma ta ‘ya’yan manyan sarakuna, ta fadawa mahaifiyarta Nenne Sappa kalaman cikin taushin murya, Nenne dake gyangyadi akan dardumar data yi sallahr walha ta dago tana duban Fatima fuskarta fal damuwa. A hankali ta bude ido sosai daga lumshewar data yi musu ta dubi doguwar diyarta Gimbiya Fatima, kyakkyawa ta karshe, wadda ke tsaye a kanta da wayar Nenne din a hannunta data sunkuya ta dauka a gabanta, har zuwa lokacin anata kira ba'a daina ba. Da sauri Nenne tace “Miko min wayar, Allah yasa shine, bana cikin nutsuwa Fatima, saboda yau kwana biyu bai kira ni ba, gyangyadinnan da kika ga nake yi mafarkinsa nakeyi a cikinsa, wai bashi da lafiya, dadin dadawa tun shekaranjiya rabon da ya kira ni, abinda bai taba yi ba, jinkirta kira na a duk yanayin da yake ciki (koda kuwa ace yana kan Doki ne)”. Fatima ta mika mata wayar, sannan ta zauna a gefe tana bata labarai. “Nenne jiya ne ‘Championship Tournament’ din su Hammah fa, a can Argentina, bashi da lokacin kansa kin sani. Na so inje kallo physically Dade (Baba) ya hanani, tun dazu kuma na kunna ‘PoloLine.TV’ ba’a nuno gasar ba. “I am worried too”. Ta karasa fada da harshen yarbanci. Wato itama cikin damuwar take kwatankwacin ta mahaifiyarsu. Ba tareda ta amsawa Fatima maganarta ba Nenne ta amsa wayar da ake tayi mata ba kakkautawa da sallama cikakkiya irin tata ta nutsuwa, ta hanyar nemawa wanda ya kirata amincin Ubangiji ba tare da ta san cewa katon Bayahude bane ke kiranta ba musulmi bane ba kuma Dan nata ba, duk kuwa da cewa da lambarsa aka kira ta. A wayar aka shiga yiwa Nenne bayani da harshen da ba ganewa take yi ba, wato yaren “Araucano” na Argentina. “Sunana Pareto Danny, ina magana daga wayar ubangidana, ya samu tsautsayi ne… muna asibiti, inason magana da Mother dinsa…”. Don haka sai kawai ta mikawa Princess Fatima wayar cikin yamutsa fuska tace “ungo nan Fatima, kiji me wannan yake fadi haka?”. Ba don ma taga lambar ta Ajantina bace da bazata amsa kiran ba, a ka’idarta Nenne Sappa bata amsa bakuwar lamba, amma kasancewar ta san cewa AbdulRasheed yana can, kuma yau kwanaki biyu kenan tana alhinin rashin kiran wayarsa da bata samu ba kamar kullum, domin duk halin da yake ciki baya kasa kiranta kona minti uku ne, shine yasa ta amsa wannan kiran da gaggawa don jikinta ya bata ya shafe shi. Maganar mintuna kusan uku Princess Fatima tayi da Pareto a wayar, ta fahimci me yake kokarin sanar dasu, wato Prince ya fado daga Doki, ya jikkata fiyeda koyaushe, yana asibiti a kwance da karaya a hannunsa, don haka Fatima sarkin raki sai kawai ta saki wayar a kasa ta dora hannuwa aka ta sakawa Nenne kuka. Kasancewar Fatima mai tsananin so ga Yayan nata kuma mai saurin kuka. Suna son junansu suna kula da juna shigowar bare cikinsu ne dai karbarsa sai a hankali. Nenne nata tambayarta ta gaya mata me aka ce mata? Da kyar, kafin Fatima tace cikin hawaye “Nenne Hammanmu wai, ya fado daga Doki yaji raunuka a jikinsa, yana asibiti can a kwance, an kira Dade a gaya masa ba’a sameshi ba shine aka kira ki”. “Subhanallah!” Inji Nenne, cikin kidimewa da mikewa tsaye, tana cewa “wannan DOKI!” Nan dai ta nemi fulatancin da take gwadawa akan AbdulRasheed sau tari yau
🏠