NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 24 of 44

aspy voice) yace da dokin nasa; “SAHEEB!!!” Saheeb din yayi haniniya cikin amsawa, amma bai tafi ba. Ya kara cewa da sauti mai karfi fiyeda na farko “SAHEEB, Go!”. Wanda hakan ya zama fusataccen umarni na biyu ga Dokin da aka kira da suna “SAHEEB” abinda bai taba faruwa ga Dokin ba (ubangidansa yayi masa umarni sau biyu). Shi kansa dokin sai ya rikice. (Thoroughbred Horse) ne wato haihuwar Argentina kuma acan aka raine shi har ya girma, mamallakin nasa ya kwashe shekaru yana kiwata shi cikin gata da kula da lafiyarsa da tsaftar jikinsa da akaifarsa, kasancewarsa (favourite horse) dinsa cikin duka Dawakan da ya mallaka a (stable) din dake Ranch House dinsa (wajen kiwon Dawakai a jere cikin gidan gona). Ba Saheeb ne kadai Dokinsa ba, Dawakan hawansa sun kai shida, amma shine na gaban goshinsa, babu mai ganin soyayya da gatan da Saheeb ke samu. A ka’ida duk bayan shekaru biyu sai ya sake lafiyayyen Doki, amma shi wannan da ya kira “Saheeb” abokinsa ne da bai taba sake shi ba, kula yake da shi kamar dan cikinsa, kasacewar ya fito daga hannun daraja, wato hannun Kakansa da yake matukar so (dattijo mai ran karfe), tun lokacin da Kakan nasa yayi masa kyautar sa har kawo yau yake son Dokin sosai. Kakansa ya saya masa Dokin ne a wani zuwa da yayi musamman har kasar Argentina da kansa, don ganewa idonsa yadda babban jikan nasa yake gudanar da wasan nasa na Polo, a lokacin gasar ‘World Polo Championship’, wanda shima an gudanar dashi ne anan kasar Argentina. Haka yake bata lokacinsa da aljihunsa wajen kula dashi da lafiyarsa, kamar yadda yake kula da tasa lafiyar. Abincin da ake masa cusa dashi daban dana sauran Dawakai ‘yan uwansa, haka yanada kwararren Vetrenary Doctor dinsa (likitan dabbobi), wurin kwanan Saheeb na musamman ne cikin duka Dawakansa. Saheeb yana kwana ne a cikin korran ciyayi masu taushi (pitch grass) dake cikin (stable) dinsa. Mai kula da taje gashinsa da rage shi da gyara shi da yankan kumbarsa zaman Dokin yake a gidansa dindindin, ma’aikaci ne specialist akan raino da kula da Dawakai yake zaman albashi domin kula da Doki “SAHEEB” a (ranch house) din mamallakinsa shine Pareto. Albashi na musamman Pareto yake lamushewa daga aljihun maigidansa don kula da hamshakin Dokin nan nasa (Saheeb). Shi wannan saurayin Ba’ajantine (Pareto) wani kwararren ‘Horse Breeder’ ne, wanda yayi karatunsa da kwarewa musamman akan kiwon Dawakai da kula dasu. **** **** **** Umarni na biyu wanda ya fito cikin matukar fusata daga Ubangidansa, da dukan da yayi masa da sandar Polon dake hannunsa (polo mallet), shi ya sanya Doki SAHEEB yin fitar kibiya don bin umarnin ubangidansa, ya daddage ya taka a guje, yabi bayan sauran Dawakan har nan da nan kamar kiftawar ido ya cimmasu. Daganan mahayan suka saki ragamar Dawakan a guje, da wani irin gudu mai gigitarwa. ‘Helmet’ din dake kan kowannensu, wadda ta rufe rabin fuskokinsu ta bar rabi a waje, shi zai sa ka gane cewa Abdulrasheed (Kehinde) shikadai ne bakar fata dan Africa a cikin su, kuma dan kasarmu ta “Najeriya” mai wakiltar hadakar kasashen Africa ta yamma a ‘tournament’ din. Baka jin komai na tashi daga bangaren ‘yan kallo (sashen ‘yan Africa) sai ‘applause’ na kiran sunansa da fito da usur, cikin ambaton “…. PRINCE!!! PRINCE! PRINCE!” Suna masu daga masa hannu cikin tarin kauna da bada karfin guiwa…. As he started to lead the match now…. wato ya zamo shine akan gaba, dokinsa ya yiwa sauran fintinkau, duk da kasancewar dokinsa yayi jinkiri da farko, amma daga bisani dokin gudu yake baya ko sassautawa kamar ma ya fita a hayyacinsa sabida sabo da yayi jinkiri, gudu kawai SAHEEB yake zubawa kamar zai tashi sama dashi, har shi da kansa ya sha jinin jikinsa cewa gudun da Saheeb yake yi yau ya zarta kima. Gab da zasu isa ‘goal’ ne mummunan tsautsayin mara dadin ji da gani mai muni sosai ya afku. Taki kadan kafin isar su ga ‘goal’, PRINCE ya fado kasa daga dokinsa ji kake timmm! Sakamakon faduwar bazata da dokin nasa Saheeb yayi, alhalin yana gab da isa ‘goal’. Nan da nan hankula suka tashi, ‘yan kallo suka mike tsaye cikin alhini, Alkalan gasa ma haka suka dakata, aka kawo gado nan da nan aka dauke shi daga wajen zuwa asibiti, bayan an fara bashi duk wani taimakon gaggawa tun a hanya kafin a isa asibitin dashi. Karo na sau ba adadi da faduwarsa a Doki, a duka tarihin hawa dokinsa tun na kuruciya, bai taba faduwa yaji rauni irin na wannan karon ba, Saheeb ya raunata shi sosai, bayan kwashe kusan shekaru masa dan dama yana wasan Polo dashi a wurare daban daban cikin kasar Argentina. Duk da bashi kadai yake hawa ba, wato wani zubin yana hawa wasu Dawakan bayan Saheeb kuma lafiyayyu kamarsa, amma ya camfa cewa yafi jin kaimi da sakewa da nishadi idan ya hau shi don yin wasan Polo, kuma yafi samu nasara idan Saheeb ya hau. Ko babu komai ya fito ne daga
🏠