NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 23 of 44

lass mai garai-garai, yana cikin tunanin yadda tournament dinsa na gobe zai kasance. Wani wasan tseren Doki ne wanda ya jima yana jiran zuwan lokacinsa, da yi masa kyakkyawan shiri. Ba don komai ba sai don kasancewar wasa ne da zai gama daga darajar sa a duniyar wasan tseren Doki, da shahararsa a Polo a kasar da yake yiwa Polo tana biyansa (Argentina). A wannan wasan ne yake saka ran kaiwa sauran taki kadan din daya rage masa…. In Allah yasa yayi nasara, zai samu ya kai matakin karshe na kwarewa a wasan Polo da ya dade yana harin kaiwa wato (10+ goal Polo Handicap). Shi kansa Saheeb kamar ya san shirin da ubangidansa keyi akan fitarsu ta gobe, da burinsa akan tournament din gobe, don haka in ka ganshi sai kayi mamakin yadda yake annashuwa, sai harbin iska yake da haniniya cikin sabo da yanayin da koshin lafiya a tare dashi. Hausawa suka ce wai rana bata karya saidai uwar diya ta ji kunya, kome aka sawa rana cikin yardar Allah zai iso kamar kiftawar ido, gobe ne wannan ranar da Prince Abdulrasheed (Kehinde) Idris Akanni ke ta dakon zuwanta wadda yake yiwa wannan babban shirin da kyakkyawan fatan, wato ranar tseren Dawaki na duniya da Argentina ta shirya tsakaninta da sauran kasashen Polo na duniya. Amma shin ba masu azancin magana ta tsinkaye sunce mafarkai kamar dan da ba’a haifa bane? Wani a haife shi a raye, wani kuwa a mace ake haifarsa. Ba kowanne fata, ba kowanne buri ne yake tabbatuwa a lokacin da mukeso, ko muka tsara yuwuwar tabbatuwarsa ba! Sai lokacin da Allah ya so, ko ya ga damar tabbatuwarsa. **** **** **** RANAR GASAR KOFIN TSEREN DAWAKI NA DUNIYA A KASAR AJANTINA (ARGENTINIAN INTERNATIONAL OPEN POLO TOURNAMENT) S ahu biyu ne na mahaya Dawakai zaka iya hange, suna masu kallon juna sashe-sashe sun jeru reras akan layi. Duka Dawakai goma ne a kawanne sahu, nashi dokin yana tsakiyar sahun farko, Dawakan sun tsaya car da kafafuwansu, suna kartar kasa da kofatonsu gwanin ban sha’awa cikin koshin lafiya sai faman ragaji da harbin iska suke tsabar koshi, sai sheki suke kamar zasu fashe sabida tsaftar da suke samu, ‘Polo Riders’ din (mahayan) sun yi irin tsayuwar nan ta jiran umarni daga ‘umpire’ bisa ingarmomin Dawakan tseren Doki na musamman wadanda ake kira (Polo Horses). Dawakan duka murdaddu ne kuma kosassu, sannan dogaye sambal, kalolinsu sun hada da farare, bakake da ruwan kasa, ga gashi yala-yala a kansu, da ka gansu kaga lafiyayyun Dawakai rainon gidan gona saboda koshinsu da cikar tsokar naman jikkunansu. Wadannan Dawakai ana rainonsu ne musamman don wasan tseren doki (Polo Tournament) na kwatankwacin irin wannan da ake yi yau, ko kuma don mallakar manyan Sarakuna da masu kudin gaske, dake da sha’awar wasan tseren Doki a matsayin ‘hobby’ dinsu ko ‘sport’ dinsu. Irin wadannan Dawakan zaka samu ba’a ko’ina ake kiwata su ba, kuma ba’a sayar dasu a ko’ina kamar yadda ake sayar da sauran normal Dawakai na kasar Hausa. Su din Dawakai ne na musamman, da sai a wannan babbar kasa kuma hamshakiya a sha’anin wasan Polo (Argentina) kadai ake kiwata su, wadda sanin kowa ne ta shahara fiyeda kowacce kasa a duniya in dai akan sha’anin wasan Polo ne, wato birnin Buenos Aires (Capital of Argentina). Ana kiran wadannan Dawakan da suna; ‘Thoroughbred Argentinian Horses’. Gabadaya mahayan nan suna sanye da kaya iri daya, wanda ya zame musu (uniform) na wasan tseren dawaki wato; fararen riguna masu kwala da farin wando (Polo t-shirts and white Trousers). Kamar yadda na fada a sama ‘team’ din mahaya Dawakan guda biyu ne, sukayi sahu-sahu suna masu fuskantar juna cikin jiran a kada kararrawa, su fara. Kawunansu sanye da ‘polo helmets’ wadda itama fara ce kal da ratsin shudi kamar kalar kayan jikin su. Yayinda kafafunsu ke sunke cikin fararen takalmannan tsadaddu da ake kira ‘Brogues’ da 'Chukka boots' da kuma ‘loafers’. Umarnin ‘umpire’ kawai suke jira ya kada kararrawar bada umarnin farawa, su kuma su fafari dawakansu ta hanyar baiwa Dawakan umarnin tafiya, wato daga nan za’a fara ‘match’ din. ‘Umpire’ (mai bada umarni/alkalin wasa) ya duba lokaci a agogonsa, yaga lallai lokacin da aka saka domin farawa ya cika, karfe hudu na yamma ta cika daidai (agogon kasar Argentina). Sai kawai ya kada kararrawa… and the match begins marvellously (wasan ya fara da matukar ban sha’awa, da burge idanun dubban masu kallo matuka gaya), masu gani physically cikin ‘yan kallo da masu gani virtually. Abin takaici Dokin kowa ya tafi, amma nasa Dokin bai ko motsa ba, sai ya tsaya yana kartar kasa cikin ‘yan mutsu-mutsu da alamu na kin son tafiya, babu gaira babu dalili kuma, hasali ma dai Doki Saheeb bai taba yin irin haka ga ubangidansa ba tunda ya mallakeshi. Wanda hakan ya bashi mamaki, at the same time ya kuma fusata shi matuka. Da kakkausar muryarsa ta ‘yan Polo, wadda ta fito very harsh and unpleasant (r
🏠