NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 22 of 44

tsufa mai inganci saboda ibadah, har yanzu cikin koshin lafiya Nani Oummana take rayuwa a Gombe da jinta da kuma ganinta garau. Tun Nene Sappa nada shekaru akalla sha biyar take gidan aure, kamar yadda na fada a baya mahaifinta Uban Kasar Gombe Ahmadu Umar Jallo, ya bada aurenta da hannunsa ga dan abokinsa kuma babban amininsa wanda ya kasance Bayeraben Ilorin (dan kabilar Yoruba). Saida Prince AbdulRashid ya cika shekaru ashirin a duniya, bayan Nenne Sappa da Waziri Idrisu sun fidda rai da sake haihuwa, sannan kuma yaki kara auren kowa saboda son da yake ma Nennen Prince Hajiya Sappa, AbdulRasheed shi ya saka mata suna (Nenne). Kwatsam bayan fidda rai rana daya sai Allah ya kara baiwa Nenne Sappa haihuwa. Cikin ikon Allah wannan karon Nenne Sappa ‘yan biyu mata ta haifa kyawawa son kowa fara da baka, wato daya ta debo kalar dangin mahaifinsu Bayeraben usuli, dayar kuma ta debo Nenne, amma fa ko kusa ‘yan biyu basu kama kafar Yayansu Prince AbdulRasheed a kyau da farin jini gun iyaye da dangi ba, sabida shi nasa kyawun surki ne na ruwa biyu; wato duk uwar da kuma uban ya debo ya hada, don haka kamanninsa kamar na half-caste (ruwa biyu) suke. Aka kira su Princess Fatima da Princess Firdausi (Princess na nufin Gimbiya da harshen hausa). Daga kan ‘yan biyunnan ba’a kara ko batan wata a gidan su AbdulRasheed ba. Har kawo recently, da Princess Fatima da Princess Firdausi sukayi bikin cikar shekarun haihuwarsu ashirin da hudu a duniya a gidan iyayensu dake yankin Banana Island a jihar Lagos. Daga Princess Fatima har Princess Firdausi sun kammala karatun jami’a a Jami’ar Nsukka, kuma kowacce da zancen aurenta a kanta. Gidan Engnr. Idris Akanni, yana nan a Banana Island wani bangare na (offshore) din Ikoyi, waje ne da masu arzikin kasar Najeriya da masu sarauta ke buya su zabga gininnuka na gidaje, su zauna suna cikin arzikin da suka tara ta yaki-halak yaki-haram tareda iyalansu tsakiyar a jihar Lagos. Banana Island, na nan a Ikoyi, inda acan aka haifi ‘yan biyun; Princess Firdausi da Princess Fatima. **** **** **** BAYAN SHEKARU GOMA SHA HUDU Y a zama cewa a halin yanzu Engnr. AbdulRasheed (Prince) ya cika shekaru 44 na rayuwarsa, shekaru ne da suka zo suka wuce kamar kiftawar ido cikin tarin nasarori masu dimbin yawa da budi da falala a gareshi da bazasu lissafu ba. Wace duniya Haseenah take bai sani ba, don bayan kammala Masters dinsa sai ya bar Japan kwatakwata. Ya koma Argentina yayi PhD a jami’ar da ayayi karatun digiri na farko. Daga baya ya koma Qatar inda ya samu aiki da ‘Qatar Refinery’. Bayan wancan incidence din da ya faru dashi shekaru goma sha hudu a baya still yana nan akan ra’ayinsa na tafiyar da rayuwarsa yadda yake yinta ba tare da tunanin aje iyali ba, sannan ba wani aikin ashsha ne a gabansa ba sabida hardly Prince ya zauna baya komai in ba lokacin barci ba, bashi ma da lokacin kansa kona tunanin abinda ya dace a gareshi don koyaushe baka raba shi da yawon fita tournaments kasashen duniya da ake ji da wasan Polo. Polo a kasashen da ta karbu babbar sana’a ce mai matukar farin jini kuma ta manyan ‘ya’ya, Prince Abdulrasheed ya samu duk abinda ake nema a cikin Polo zuwa yanzu saura taki daya ya rage masa. Polo na jika shi yadda ba’a zato har fiye da aikinsa na matatar mai, domin yana cigaba da dauko kofin zinare a yawancin tournaments dinsa, sunansa da shararsa na kara harbawa yana shawagi a sararin samaniyar duniyar wasan Polo na duniya. Saidai kuma duk dan adam mai lafiya ai baka raba shi da feelings. Ya yarda shi dan adam ne ajizi kamar kowa, amma kuma mai iya controlling feelings dinsa, by making himself always busy da harkar Dawakansa a cikin gida, da aikinsa na matatar man fetur idan yana birnin Qatar, da kuma tseren doki idan ya fita tournaments sauran kasashe. Yafi rayuwarsa a kasar Argentina inda acan yafi yin wasan Polo, kasar data zame masa uwardaki bayan kasar haihuwarsa, Argentina. A yau tana zaune a ranch house dinsa cikin wata kujera sakar kaba ta hannu, yana kallon ingarman dokinsa da ya kira da suna ‘SEHEEB` wato ‘ABOKI’ daga can nesa dashi. A tsaya fadin cewa Dokinsa Saheeb mai muhimmanci ne da tsohon tarihi a cikin rayuwarsa bata baki ne, kasancewar shine dokin da ya fara mallaka a rayuwarsa, kuma wanda yafi so cikin duka sababbin Dawakansa. Dokin na cin korran ciyayin da suka mamaye gidan daga korran shuke-shuke masu ban sha’awa da kayatar da idanun wanda duk ya kusanto su. Daga can gefe yana iya hangen duk wani motsi na hadiminsa Pareto wanda ya dukufa aiki, saurayin dake kula masa da Doki Saheeb da sauran Dawakan dake cikin stable din gidansa. Saurayin yana rage tsayin ciyayin gidan ne da inji, yana daidaita tsayinsu da cutlass, yadda zasu fi bada sha’awa. Sannan yana kwashe kashin Doki a abin shara na musamman. A sa’ilin ba komai Prince Abdulrasheed ke yi ba sai kurbar sassanyar ruwan Inibi a tambulan na g
🏠