samo personality dinta na (Down to Earthiness) ne daga mahaifiyarta Nani Oummana, wadda ta kasance uwargida a cikin duka matan Maimartaba Uban Kasar Gombe, Sarkin Gombe na goma, wanda duk da kasancewarsa basarake to gawurtaccen Shaihun malami ne shima. Nenne itace ‘ya ta biyu cikin ‘ya’yan da ya haifa masu tarin yawa da matansa na aure hudu.
Cikinsu duka yafison Oummana da suke kira Nani wadda ta kasance mahaifiya ga Haj. Sappa. Bayan rasuwar Sarkin Gombe wato mahaifinsu Nenne a dakinsu ne aka gaji sarautar.
A halin yanzu Yayanta da suka fito ciki daya ne akan karagar mulkin Gombe wato Maimartaba Sarki AbdulYassar Jalloh Umar (CFR).
Tsohuwa Oummana ta cigaba da zama ne a dakinta bayan rasuwar sarkin Gombe Ahmadu Jalloh Umar, yayinda sauran matan da yake da sauran kuruciyarsu duk suka fita suka sake aurarraki. Don haka ta zama uwa ga ‘ya’yan sarkin Gombe bakidaya wadanda ta haifa da wadanda bata haifa ba wato diyan kishiyoyinta duk ta hada ta rike ta mayar nata don yanzu babu iyayensu mata a gidan.
Sarki AbdulYassar babban dan Nani Oummana shi Hajiya Sappa ke bi haihuwa, sai autan Nani Abdulmajid wanda ke kasar Morocco da iyalinsa, sukenan ‘ya’yan da Nani ta haifawa uban kasa, sauran ‘ya’yansa maza da mata guda goma sha biyu duk na kishiyoyinta ne amma bazaka taba iya banbance wadanne ne wanda Nani Oummana ta haifa da wadanda take rikewa marigayin mijinta ba, saboda adalci da halin dattaku irin na mutanen da.
Da irin wadannan kyawawan halaye Nani Oummana ta raini diyarta Sappa mace daya (Nenne Sappa) cikin maza har itama ta girma suka aurar da ta ga zuri’ar Akanni’s tun mahaifinta yana raye, har itama a yanzu gashi ta tara nata bataliyar iyalin.
A yadda Hajiya Nenne take gudanar da rayuwarta wajen kula da tarbiyyar ‘ya’yanta hudu dake gabanta, sak halin mahaifiyarta Nani Oummana, ba bazaka taba cewa ita din ‘yar Sarki kuma jikar Sarki, sannan matar babban dan Sarki, uwa ga jikan Sarki na farko bace.
Sabida yadda take nuna musu gudun duniya da mantawa da madaukakiyar nasabarsu, ita dai burinta shine su bi Allah, su kasance masu tausayawa mara karfi, su kiyaye sallah akan lokaci, su nisanci zinah kowacce iri kowanne nau’I ce, wannan itace tarbiyyar Nenne kullum ga yaranta hudu, duk wani burinta a yanzu shine ya zamo cewa halinta suke kwaikwayo, halin kankan da kai da tawali’u, shi takeso Taiwo da Kehinde da kannensu twins mata guda biyu wato Firdausi da Fatima su siffantu dashi.
Amma me? Cikin ‘ya’yan nan nata guda hudu kowa halinsa daban da nata, babu mai irin halinta na kaskantar da kai. Suna gudanar da rayuwarsu ne bisa tsari na ‘ya’yan manyan sarakuna da irin tarbiyyar gidansu na Akanni’s wato yadda suka taso suka tarar a masarautarsu ta Ilorin. Kakansu Sarki Abdulrasheed da kansa ya taba cewa Nenne ta haifo masa jikoki masu halaye daban-daban da yake tinkaho da dabi’unsu na sarauta. Abdulrasheed baya rayuwa irin wadda take so, baya zama a kasarshi, rayuwa ce yake yi daidai data ‘ya’yan gata kamarsa, domin Kakansa ya tsaya masa.
Taiwo kuma miji ya tsaya mata don ba karamin dukiya Toufeeq ya mallaka a turai ba.
Sannan Fatima da Firdausi Yayansu Abdulrasheed da suke kira Hamma wato (Prince) ya dade da tsayawa rayuwarsu matuka, tun shigarsu jami’a yake dawainiya dasu, bai yarda Dade (mahaifinsu) ya kashe komai akan karatunsu da bukatunsu ko dawainiyarsu tayau da kullum ba, shine komai nasu, baya so su kannen sa su nemi wani abu komai tsadarshi su rasa tunda shi ba iyali ya ajiye ba, so kusan zamu iya cewa komai na Prince na ‘yan uwansa ne baida wani buri bayan walwalarsu da wadatuwarsu.
Princess Fatima da Princess Firdausi nada albashi mai tsoka duk wata kai tsaye daga account dinsa zuwa nasu. Haka Kiki da Hakeem ‘ya’yan Taiwo.
Hajiya Sappa kullum tsaye take a kansu da addu’a, shine kadai saukinta. Musamman shi da yayi nisa da ita, kullum ko a waya bata fasa tunasar da shi bin Allah, kaunar musulunci da kiyaye sallah, ko yana dauka ko baya dauka ita dai Nenne bata fasawa kuma bata fasa yi masa addu’a ta musaman a duk inda yake cikin duniya Allah ya kare mata shi daga rudin zamani dana kuruciya, kasancewarsa namiji daya tal a cikin mata uku da Allah ya bata.
A yadda Hajiya Sappa take rayuwa cikin yawan ibadah kullum, da kula da bautar aure da mijinta uban ‘ya’yanta, kai sai kayi tsammanin ita din wata waliyya ce. Shigarta kullum cikin hijabai (jilbabs) kala-kala kamar bata da alaqa da kowacce sarauta.
Duk shekara Hajj da umarah basa wuce Nenne Sappah, bata azumin Ramadhan a gidanta dake Lagos sai a birnin Makkah da Madinah duk shekara, wani abun burgewa da Nenne in zata je Hajji bata bin International saidai Pilgrims duk cikin halinta na (down to earthiness) da kaskantar da kai, wanda take bi duk shekara daga hukumar alhazai ta jihar Lagos zuwa Saudiyyah.
Shekarun Nenne Sappa a halin yanzu sun kai kusan sittin da biyar a duniya. Yayin da mahaifiyarta Nani tayi