NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 20 of 44

i da kasumba. Ta yarda soyayya masifa ce (ga wanda bai yi sa’arta ba) sannan cin amana daga wanda kake so, ka kuma yarda dashi da zuciya daya, ka wahaltawa rayuwarsa a lokacin da yake tsananin bukatar taimako kamar Haseenah da Adetokumbo yafi komai lahanta zuciyar dan adam wato (butulci). Balle Abdulrasheed da zata rantse bai taba cin amanar kowa a rayuwarsa ba, mai kirkine mai alkhairi ne shi, zuciyarsa mai kyau ce kuma mai tsafta ce akan kowa da komai, komai zai yi ma mutum yana yi ne saboda Allah ba don ya rama masa ba. Taiwo ko kafin ta ko huta kicin ta shiga ta samar masa abinda zaya ci mai zafi da nauyi wato Amalar bawon doya miyar Ewedu data ji naman turkey da smoked fish zuku-zuku. Saida ta tabbatar ta masa favourite food dinsa ya ci sosai ya sha tea na nescafe mai zafi, sannan ya kishingida akan sofa da Kiki a gabansa yana wasa da ita. Ko a kwayar idonsa ta lura yunwa tayi masa lahani a kwana biyar ba kadan ba, kasancewarsa mutum mai yawan cin abinci, kullum Nenne na cewa “his best friend is food”. Idan akwai abinda yafi karyawa namiji zuciya toh Hasinah ta karya maza, ta karya zuciyarsa raga-raga. A daren shi da Taiwo sun zauna sun kara tattaunawa kan al’amarin da ya faru dashi da Hasinah, kuma Taiwo bata barshi da mummunan tunanin da ya riga ya tsirga ya samu muhalli a zuciyarsa ba na cewa duk mata haka suke, tayi ta bashi baki da kwantar masa da hankali da bashi kyawawan misalai iri daban – daban na halin lalacewar da al’umma ke ciki a wannan zamanin, tace don haka wannan bazai zamo wani abin mamaki daga halayyar dan adam ba. Taiwo ta kara da cewa “ka yarda ba kuma duka mata muka taru muka zama daya ba a halayya da dabi’a, ta kara da nuna masa cewa Hasinah ba itace karshen rayuwarsa ba, sannan ba itace autar mata ba, wasu matan ma nagari ko haihuwarsu ba’a yi ba, tace kada hakan yasa ya fidda kyakkyawan fata akan mata tagari. A cewar Taiwo, “mata nigari yanzu aka fara haifarsu”. Shirmen Kiki ma ya taimaka kwarai wajen cheering dinsa up. Ya fara murmushi, murmushinnan nasa mai matukar kyau da aji, da Kiki ta hau jan kasumbar daya bari a fuska wadda bata saba gani a tareda shi ba, ya dan fara sakin ransa da mantawa da damuwar Hasinah Ambursa don ita tafi bashi mamaki fiye da Adetokumbo wanda dama su maza ai kunyarsu ragagga ce akan macen da zuciyarsu ta kwadaita musu. Shikuwa Tokumbo Akanni a ranar bai kara kwana a Tokyo/Japan ba, yana jin karshen shigarsa kasar Japan din kenan gabadaya, har dai in Abdulrasheed yana cikinta, duk da a can ne harkokin kasuwancinsa suka fi yawa. Taiwo da Kiki, basu baro Tokyo ba saida suka kwashe sati tare da Prince Abdulrasheed (Kehinde), har sai da ta tabbatar Prince din ya manta da damuwar da Hasinah ta haddasa masa, ya koma harkokinsa da rubutun project dinsa amma ko sunanta yace kada ta kara ambata masa. A zahiri Prince Abdulrasheed ya saki ransa sosai yadda Taiwo keso, har ya koma harkokinsa na baya ya soma duba schedules na tournaments, yayi kokarin da ya kammala project dinsa kaf tun kafin barin su Taiwo gidansa. Musamman da komai Taiwo ke masa cikin gidan na kula da abincinsa da tsaftar gidansa da lallashinsa shi kawai aiki yake wuni yi akan kwamfuta. Amma abinda Taiwo bata sani ba shine mummunar illar da incidence din yayi a zuciya da tunaninsa, ya riga ya gurbata psyche na tunanin sa akan mata da soyayyar dukkan diya mace in general. Ranar da suka kwana bakwai tare dashi Taiwo da ‘yarta suka juyo gida Lagos cike da kewarsa. Da alkawarin sai sun zo bikin kammala karatunsa nan da ‘yan watanni masu zuwa. ***** ***** **** WACECE NENNE SAPPA? N enne (na nufin ‘Uwa’ kenan), da harshen fulatancin Arewacin Najeriya na sassan Gombe, Adamawa da Taraba, wanda Hajiya Sappa ta fito daga cikinsu, kuma da shi yaranta ke kiranta, Nenne Sappa, irin iyayen mun nan ne na zamanin da, masu halin zuhudu (gudun duniya), taqawa, da tsananin yawan ibadah wadanda duk halaye ne na NANI OUMMANA. Mahaifiyar ta Nani Ummana ta kasance mace mai yawan kaskantar da kai, da gudun rudin duniya, wadannan sai suka zamo halaye ne wadanda dasu ta raini Sappa, duk wani halin tawali’u wato humbleness (a down to earth personality) Nenne Sappa ta hada shi cikin kyawawan halayenta. Nenne Sappa ta kasance kyakkyawar dattijiya, fara ce kal, jazur da ita mai yalwar sumar kai, gira data idanu, mahaifiyarta Nani bafullatanar garin Gombe ce don haka kusan zamu ce kamanninta Sappa ta debo, wadda yawan shekaru baisa kyawunta ya gushe ba sabida hutun da take ciki kuma jikinta mai boye shekaru ne, yanayin jikinta ya nuna cewa an zuba kyau da farin jinin manyan sarakuna a zamanin kuruciya. Kai kace Sappa ita ta zabarwa kanta duk wata kankanuwar halittar dake jikinta don kyawun fasali, har zuwa yanzu data baiwa sittin da biyar baya, Nenne Sappa, na nan da extra added beauty dinta (zallar kyawunta). Kenan a takaice sai mu ce Nenne, (Hajiya Sappa) ta
🏠