NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 2 of 44

ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari’ah kuma abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa’I Wali. GODIYA DA JINJINA Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari, tacewa da gyarawa (editing) Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aisha Muhammad, Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira. In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH. KAFIN MU FARA INA TALLATA MUKU AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR) Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control? Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da kyakkyawar mu’amala. Aisha Lame karshe ce wajen baiwa fata hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo ku bani labari. -Takorinku SHIMFIDAR LABARIN WAIWAYE ADON TAFIYA (1) D r. Murjanatu, wadda kowa a gidansu da danginsu bakidaya da “Taiwo” yafi kiranta, kannenta kuma suce mata “Aunty Taiwo”, abokan karatu su ce Murjanatu Akanni. Murjanatu baka ce ba sidik ba, bakin da akewa lakabi da (chocolate beauty) sabida sanyin kyawunsa da haskensa, doguwar mace mai ‘yar kyakkyawar kiba ta jikin hutu, irin kibar da batayi munin da za’a ce mata lukuta ba. Saboda duk da kasancewar ingarman jiki keda Dr. Murjanatu to suffar jikinta mai tsari ce duk da kibarta, gata da doguwar fuska irinta fulani da dara-daran idanun yarbawa masu haske, Taiwo-Murjanatu, nada dogon hanci sambal irin na Kakarta ta wajen Uwa wadda ta kasance bafullatanar jihar Gombe da suke kira “NANI OUMMANA”. Sannan tsayin ta masha Allah shima bai wuce misali ba. Komai na Dr. Taiwo kamar ita ta aunawa kanta ta kuma zaba. Domin dai a fasalce baza’a kira Aunty Taiwo doguwa irin sambal ba, saidai ace kamar kwalbar nan ta coca-cola ga kauri ga tsayi da dirin jiki mai zati, tana a ma’aunin daidai na tsayin da akeso a tareda mace. Shekarun Murjanatu na haihuwa a wancan lokacin da muka waiwaya talatin cif. Murjanatu-Taiwo Akanni ga tsayi ga zati irin na mace mai aji da kasaitar nasaba, girman jikinta mai ban sha’awa ne don bai sa mata muni ba. A takaice komai na jikin Taiwo irin na matasan matan kabilar Yoruba ne, wato daga kabilar Yarbawa ta fito. Tafiyar Taiwo mai daukar hankalin mai kallonta ce, domin tana tafiya ne cas-cas akan tsinin dugaduganta, cikin rangaji na jan aji da kasaita sanna ga iya ado mara misaltuwa, kullum haka take cikin tsantsar gayu da yawan ado, duk yadda ta motsa ko tayi magana ko murmushi sai kaga wannan ajin na musamman irin na jinin sarautar gidansu ya nuna kansa a tareda ita. Kallo daya zaka yiwa Taiwo da dabi’unta da iya kasaitarta kasan ta hada jini da sarautar Yarbawa mai tushe, ko daga yanayin takun tafiyarta dinnan mai kayatar da idon mai kallonta kamar Dawisun da ya baza adon jikinsa yake tafiya. Tafiyar Murjanatu cikin kasaita da iya sarrafa jikinta da yake mul-mul irin na kosassun ‘ya’yan kabilar Yoruba da suka ci suka tada kai. A daidai wannan lokacin da Murjanatu ta shigo gidanta, yamma ce lis, hadari ya gangamo, sararin samaniya yayi duhu, sai cida da iska ke kadawa, gab ake da kecewa da ruwan sama mai karfi. Wannan na faruwa ne a cikin daya daga manyan biranen Najeriya mafi yawan al’umma da kabilu daban-daban, wato birnin Legas ko Ikko da aka fi sani da jihar Lagos. Gidan nata matsakaicin gidane kyakkyawan (Duplex Mansion) wanda anan Dr. Taiwo da iyalinta ke zaune tun dawowarsu Jihar Lagos da zama daga Ilorin, gidan yana nan a shiyyar babbar unguwa mai tsari ta masu hannu da shuni ‘Eko Atlantic’, gidan Murjanatu nada farin fenti mai dan duhu da ratsin ruwan madara-madara (off-white/milk), kuma gida ne da in ka gani ko daga nesa kasan masu shi sun jima da kama kasa. Zamu iya kimanta lokacin da misalin karfe shidda na yamma, daidai lokacin da Taiwo-Murjanatu, ta shigo da kan motarta kirar ‘Hyundai Creta’ harabar gidannata, bayan tasowarta daga asibitin da take (housemanship) acan, wato asibitin koyarwa na jihar Lagos. (Murjanatu-Taiwo Akanni, dalibar likitanci ce a Lagos State Teaching Hospital). A wannan lokacin duk tunaninta da hankalinta na kan karamar diyarta (Kiki) wadda ta baro a gida hannun sabuwar mai rainonta Bunmi, tun bayan data fara housemanship ta samo Bunmi ‘yar kabilar Ibira suke zaune tare. Kiki ‘yar kimanin shekaru uku wadda saboda son da dan uwanta yake mata, yasa a yawancin lokuta bata dauka cewa ita ta haifeta, tafi dangantata da ‘yarsa shi kadai, ko cewa zata yi Kiki sai ta hada da inkiyars
🏠