A daidai wannan lokacin fitar sunan AbdulRasheed Idris Akanni a wasan Polo, zamu iya kwatanta shi da hada kafada dana manyan ‘yan wasan Polo na duniya irin su Nacho Figueras, Mariano Aguerre, da Lia Salvo. A kasashen Africa kuma irin su Adolfo Cambiaso na South Africa, Bello Buba na kasar Najeriya, da matashin dan Polo mai tasowa a arewacin Najeriya wato Khalil Halilu, wanda bai kai su shuhura ba.
A shekarun da suka gabata Abdulrasheed ya sha ciyowa Africa kofi a USPA Gold Cup, haka ya ci kofin World Polo Championship, Concacaf Gold Cup, Dubai Gold Cup, U.S Polo Championship, da Cartier Queen’s Cup.
Duka wadanan siraran kofuna suna nan a jere akan makeken tebirin ofishinsa dake cikin (Qatar Petroleum Refinery) a birni mai tashen arziki (Qatar), inda ya samu muhimmin aikin yi irin wanda mahaifinsa yafi na’am dashi.
Har zuwa lokacin cikarsa shekaru arba’in a duniya Prince bai kara sha’awar soyayya ba, bai kara sakawa ransa son yin aure ba, ya tattara maganar aure da mata ya tura su can wani gefe mara amfani na shafin rayuwarsa, ya zamo yana cigaba da playing Polo for fun and pleasure da kuma debe kewa kadai. Amma aikin da ya samu da (Qatar Petroleum Refinery) bayan kammala PhD dinsa akan (Oil and Gas Engineering) yasa dole ya bar kasar Polo ta Argentina ya tare a Qatar, sabida aikin refinery yafi cinye lokacinsa yanzu fiyeda wasan Polo.
A halin yanzu da yake da shekaru arba’in da biyu a duniya, Engnr. AbdulRasheed Idris Akanni, zamu iya cewa ya gama accomplishing komai na daukakar aiki akan Oil and Gas, tunda yana kan matsayin ‘Star Engineer’ na ‘Qatar Refinery’, AbdulRasheed ya gama cika duk wasu burika na rayuwarsa, saura kaiwa makura a gasar Polo wato (10+ goal handicap).
Kudi yake samu kawai daga kasashe daban-daban ta harkar Polo da kuma aikinsa, har bai san abinda zai yi dasu ba, babu Da, ba jika, balle matar da zata taya shi mora (babban tashin hankalin iyayensa kenan). Don haka AbdulRasheed ya himmatu wajen aikin alkhairi ga ‘yan uwansa mata guda uku musamman Taiwo, ya tsaya musu, ya tsayawa cigabansu, baya barin iyayensu su yi musu hidimar komai ta karatu kota yau da kullum, balle mijin Taiwo da yake da kankamo sai ya zamanto komai nata shine, har ila yau yana raba arzikinsa da iyaye da ‘yan uwansa na Uwa dana Uba (duk da kasancewarsu ba mabukata ba). A gefe kuma a boye, Prince Abdulrasheed ya dage wajen tallafawa gidajen marayu dana gajiyayyu a kasarshi Najeriya inda a irin haka ya samo HASEENAH.
A halin da ake ciki yanzu (he mainly consults for the refinery) fiye da zama a ofis yayi aiki. Don haka ne yake samun lokacin da yake fita ‘tournaments’ kadan-kadan, to really play his passion which is ‘Polo’. Amma dai rayuwarsa yanzu tafi yawa a birnin Qatar.
Wannan shine tarihinsu Prince AbdulRasheed da iyayensa, ‘yan uwansa, da komai da ya shafi rayuwarsa ta yau da kullum, rayuwar da kowa yake kallo masa a matsayin ‘incomplete’ wato wadda ba cikakkiya ba, mai wawakeken gibi, duk da tarin achievements din da ya cikata, da tarin arzikin dake cikinta musamman mahaifiyarsa, Kakarsa da mahaifinsa da ‘yan uwan haihuwarsa gabadaya suke cikin damuwa da rashin cikarta, domin kuwa har zuwa wannan lokacin da ya tasamma shiga shekaru 43 ba wanda ya san dalilin sa na kin yin aure ko yin budurwa in ka cire Murjanatu.
Wanda ya zamo na jikinsa sosai ne kadai zai iya gane cewa, duka lokutansa na yanzu ya mallakawa wasan ‘POLO’ ne, da kuma aikinsa na matatar man fetur, sannan Prince yana ibadah musamman ta yawan azumi a gidansa, ba abinda duniya ke zarginsa dashi ne a gabansa ba.