NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 16 of 44

n makaranta mai inganci ba. Ya kai cewa a yanzu ya taka mataki har na digirin digirgir, a fannin injiniyan mai (Petrochemical Engineering). Duk da haka Polo Sport ya zame masa hobby din da ya kasa bari tun tashen balagarsa. A can baya Prince yana yin wasan Polo ne (for fun) kadai, a matsayinsa na jinin Sarauta gaba da baya, ba don neman kudi ko neman suna ba, haka ba tareda tsammanin zai kawo mataki irin wanda yake kai a yanzu, a wasan tseren Dawakai ba. A kan karan-kansa ya san yana yin wasan Polo ne kawai don ransa yana so, yana yi ne don biyan bukatar sha’awarsa ga wasan, da nishadin da yake samu a cikinsa. Polo ne kadai ke mantar dashi damuwarsa, wanda ya fara koyo tun yana sakandire idan sunzo hutu Ilorin tareda yaran Baffanninsa su Adetokumbo. Later on in life, ya koma hawa Dawakan turawa da yara sa’anninsa a kasar Japan, wato kafin Dade yayi ritaya. Sai kuma Allah ya kaddareshi da samun duka abubuwan guda biyu dake cikin nasarar wasan Polo lokacin da ya soma girma, wato ya samu “kudi” ya kuma suna “suna” (wealth and reputation) a sanadin Polo Sport. Wadanda bai shigo wasan Polo domin nemansu ba, amma dare daya ya wayi gari dasu dumu-dumu a harkar Polo. A sa’ilin da ya cika shekaru talatin ya zama gawurtaccen dan Polo, wato ya zama ‘Polo Legend’ na Africa da Turai, don tun yana da shekaru ashirin da biyar ya fara fita (Polo Tournaments) a manyan kasashen da ake yin Polo a duniya. Kakansa ne ya fara saya masa Dokinsa na farko, kasancewar shikadai yake mara masa baya akan wannan ‘hobby’ din nasa na Polo, iyayensa duka biyu Uwa da Uba da Kakarsa ta wajen uwa Nani Ummana basa sonsa da Polo, sabida yadda yasa wasan a gaba ya mamaye lokutan rayuwarsa masu muhimmanci gabadaya, suna tunanin Polo ne ya hana shi maida hankali ga wajibinsa (yin aure) a lokacin da ya isa aure. Bayan kuma a wurinsa ba Polo bane, yana da dalilinsa, dalilin da su har yau basu sani ba banda aminiyarsa Taiwo. A can baya lokacin da mahaifin shi zai kai shi jami’a, sai Prince ya zabi tafiya kasar ‘Argentina’ yace ba inda zai je yin karatu sai acan. Hankalin Uban wato Waziri of Ilorin ya tashi kwarai, yaji tsoron kada ya kaishi can yaki yin karatu sai Polo, don haka ya kafe kan cewa bai yarda ba shima, zai saka shi a gaba ne su koma Lagos yayi acan tunda yayi ritaya a lokacin, kuma ba zai taba yarda Polo ya zame masa sana’a ba, saidai yayi karatun a gabansu, a lokacin basu kai ga dawowa Lagos ba. AbdulRasheed fafur yaki zabin Dade dinsa, na yin karatu a kusa dasu, ba don komai ba sai don tun a lokacin ya kwadaitu da komawa Argentina, yanada masaniyar cewa kasar Argentina itace kan gaba (lamba daya) a kan wasan Polo a duniya. Rigima shi da Babansa har gaban Emir Sarki Abdulrasheed. Shikuma kuma Kakannasa Sarkin Ilorin ya bi bayansa, yace akai shi duk inda yake so yayi karatu a duniya, a kuma barshi ya hau Doki son ransa har sai ranar da ya bari don radin kansa. A bashi freedom ya shiga ko’ina yake so a duniya yayi wasan Polo, da yarda da amincewa da albarkarsa da yawun bakinsa. Sannan ya zaunar da mahaifin yaron, wato dansa Engnr. Waziri Idrisu Akanni, yana masa nasiha mai shiga jiki irin ta manya inda ya nusar dashi cewa, duk abinda danka ke da ‘giftedness’ a kai, na karatu ko na sana’a ko ‘sport’, kada kayi ‘opposing’ dinsa, indai har ba sabon Allah bane. Yace dashi da harshen Yoruba “rather encourage him, support him and uplift him on it, baka san inda Allah zai kai shi akai ba, baka tunanin Allah ya sakama Kehinde nasibinsa da baiwarsa a cikin wasan Polo ne? Don haka kada ka tauyeshi akan nasibinsa. Barshi yayi tayi, shi da kansa watarana in girma ya haushi zai bari, kaidai ka bi shi da addu’ar kariya, fatan nasara da fatan alkhairi”. Wannan ne yasa Engnr. Edrees Akanni ya kyale AbdulRasheed ya tafi yin degree na farko a kasar Argentina, ya zagaya ya hade karatun da zuwa koyon Polo. Domin koda ya sauka a makaranta domin yin karatun digiri akan (Petrochemical Engineering) kwas din da mahaifinsa ya zabar masa a jami’a kenan, cikin babban birnin kasar wato ‘Buenos Aires’, tofa duk da cewa yana karatun amma sama-sama, rabin rayuwar Prince Abdulrasheed (Kehinde) a filin tseren Dawaki na kasar wato (Argentina Polo Ground) wanda akafi sani da (Cathedral of Polo), a can yake gudanar da rabin rayuwarsa. Ya gama first degree a Petroleum Engineering da matsakaicin sakamako (2.2) wanda hakan ya dan faranta ran Dade, sai ya wuce masters a Japan tsayin shekara daya ya dakatar da rubutun masters din na lokaci mai tsaho saboda Polo, kullum yanaso ya gama ko don ya farantawa Dade. Yadda wasan Polo ya rinjayeshi ne yasa Abulrasheed bai samu kammala masters da wuri ba har ya shiga cikin shekaru na talatin, bayan ya kammala at 33 da kyar da sudin ludayi, sai ya ajiye kwalayen a kasan gado ya rungumi Polo again, baya ko tunanin saurarawa Polo ko makamancin bari, har inda yau ke motsi.
🏠