NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 15 of 44

wato matarsa ta lelle da suka rayu tare tun yana karatun jami’a, kowanne cikin ‘ya’yan sarkin sunansa ya fara da ‘Abdul’ wane (sunaye dai na manyan musulman Yarbawa). Wadannan gawurtattun ‘ya’yan na sarkin Ilorin, duk da ba dukkansu ne ciki daya ba zaka samu biyu a daki daya ‘ya’ya biyu ko uku dakinsu daya. Anyi sa’a dattijon mahaifinsu mai tsayuwar daka ne akan hadin kan ‘ya’yansa, ya dade da hade kawunansu wuri guda, duk da ba duka suke ciki daya ba suna kaunar juna da kula da zumuncin da mahaifinsu ya dorasu akai. Haka Idrisu da ya taso a shikadai a dakinsu baida dan uwa na ciki daya a cikinsu basa taba nuna ba uwa daya ta haifesu ba. ‘Ya’yan Sarki su goma maza sun zama tsintsiya madaurinki daya a jihar Ilorin, sunansu ya shahara yayi tambari, kowanne cikin ‘ya’yan Sarki ya rigada ya kama kasa yadda ya kamata, mahaifinsu ya wadatasu da ilmi daidai gwargwado na addini dana zamani, kowannensu yana bin rayuwar da addini ya tsara irin wadda ya zabawa kansa da iyalinsa babu mai shiga rayuwar dan uwansa da sunan hassada, suna kokarin hada kan ‘ya’yanu kuma maza da mata, sannan wasu daga cikin ‘ya’yan Sarkin suna auren mata fiye da daya, basa takurawa junansu da kyashi da ‘yan ubanci don ilmi da wayewa da alfarmomin rayuwa ya wadacesu, sannan babu rikicin gadar sarauta a tsakaninsu sai na competition na rayuwa, wato wannan na son ace ya kere wannan a cigaban rayuwa, musamman da Allah yayiwa tsohonsu tsahon rai, hakan ya rage rikicin neman gadon sarauta a tsakaninsu, sannan babban Yayansu Idrees Akanni da akewa ganin shi zai gaji gidan ya barranta kansa daga Sarautar gidansu kwatakwata, ta hanyar ficewa daga gida zuwa kasar Japan kusan shekaru ashirin acan ya zauna, inda yayi rabin rayuwarsa kacokam, har gobe Sarki Abdurrasheed Abdullateeef Akanni yana nan daram da ransa da lafiyarsa, yana gudanar da sha’anin mulkinsa cikin adalci ga talakawansa yana kuma kara hada kan mazan ‘ya’yansa da jikokinsa maza da mata da kullum suke karuwa. Mafi yawansu basa Ilorin yanzu, suna rayuwa ne a garuruwa daban daban a cikin kasar Najeriya, duk ayyuka da sana’o’I sun sun raba musu jihohin zama, kadan ne suke a Ilorin kusa da mahaifinsu. Sannan duk cikinsu, babbansu, wato Engnr. Idrees Akanni, shikadai ne ya taba ficewa daga gida, wato ya bar gida Ilorin tunda kuruciyarsa zuwa ketare ya jima sosai, shi da maidakinsa Hajiya Sappa da ‘ya’yanta ke kira “Nenne”. Saida Prince AbdulRashid da ‘yar uwarsa Taiwo suka cika shekaru sha tara a duniya, bayan Nenne Sappa da Waziri Idrisu sun fidda rai da sake haihuwa, sannan kuma yaki kara auren kowa bayan Nenne, AbdulRasheed shi ya saka mata suna (Nenne) har sauran kannensu suka kama. Kwatsam bayan fidda rai da sake haihuwa rana daya sai Allah ya kara baiwa Nenne Sappa haihuwa. Cikin ikon Allah wannan karonma Nenne Sappa ‘yan biyu mata ta sake haifa kyawawa son kowa, daya ta debo kalar dangin mahaifinsu Bayaraben usuli, dayar kuma ta debo kalar Nenne, fulanin usuli, sai suka cakuda, kamar yadda su Kehinde suke masu hasken kala amma bakake ne, amma fa ko kusa ‘yan biyu basu kama kafar Yayyunsu Prince AbdulRasheed da ‘yar uwar haihuwarsa Taiwo a kyau da farin jini gun iyaye da dangi ba. Sabida sunzo daga baya, bayan an fiddawa Nenne rai da sake haihuwa, su nasu kyawun ina nufin (Taiwo&Kehinde) surki ne na uwa da uba (Fulani da Yorubas); wato uwar da kuma uban suka debo duka suka hada gabadaya, don haka kamanninsu kamar na half-caste (ruwa biyu) suke don kyau da ban sha’awa wato Princess Taiwo da Prince Kehinde. Ranar suna aka kira jariran Nenne da suna Princess Fatima da Princess Firdausi. Daga kan ‘yan biyunnan ba’a kara ko batan wata a gidan su AbdulRasheed ba. Har kawo recently, da Princess Fatima da Princess Firdausi sukayi bikin cikar shekarun haihuwarsu ashirin da hudu a duniya a gidan iyayensu dake yankin Banana Island a jihar Lagos. Princess Fatima da Princess Firdausi sun kammala karatun jami’a a Jami’ar Nsukka, kuma kowacce da zancen aure a kanta wanda za’ayi shekara mai zuwa. Gidan Engnr. Idris Akanni, yana nan a Banana Island wani bangare na Ikoyi, waje ne da masu arzikin kasar Najeriya da masu sarauta ke buya su zabga gininnuka na hutu da garari, gidaje na gani na fada, su zauna suna cin arzikin da suka tara a ketare ta yaki-halak yaki-haram duk, tareda iyalansu a tsakiyar jihar Lagos. Banana Island, na nan a offshore din Ikoyi, inda acan aka haifi Princess Firdausi da Princess Fatima **** **** **** THE HORSE RIDER “ PRINCE” Ya taso da azabar son hawa Doki wanda ya budi ido yaga ana yi a gidan Kakansa Emir of Ilorin. Dadin abun shine, ko muce ludufin da Allah yayima iyayen Prince AbdulRasheed shine; duk sonsa da hawa Doki wanda ya kasance masa ‘hobby’ a tasowarsa, ya kuma zamar masa azababben ‘passion’ na rayuwa tun yana matashi, hakan bai hanashi tsayawa yayi karatu
🏠