ata ba, al’adu da dabi’u sun banbanta, amma gradually tayi hobbasa ta koyi yarensa duk da wahalarsa cikin dan lokaci, shima kuma dama ya iya fulatanci, wannan ne ya taimaka mata sosai wajen zama a cikinsu.
Sai ya zamanto Idris tun daga kanta bai kara marmarin auren kowacce mace ba har zuwa inda yau ke motsi da suka cimma shekarun girma shi da Nenne Sappa, da zaratan tagwayen ‘ya’yansu saiti biyu.
Bayan aurenshi da Sappa da kadan ya samu aiki da wata masana’antar safarar jiragen ruwa a kasar Japan (Japanese shipping authority), sai ya dauketa da karamin ciki ya tafi da ita Japan, ya saka ta a makaranta tayi ilmin zamani mai zurfi a fannin aikin jinya (Nursing) ba don tayi aiki ba sai don ta samu ilmin kula masa da lafiyar yaransu a gida.
Sappa ta fara da haihuwar ‘yan biyu mace da namiji a haihuwarta ta fari. Yaran da al’adar Yoruba ta riga ta basu suna “Taiwo” da “Kehinde” watau Hassana da Hussaini. Taiwo sunan Kakarsu ta wajen uba mai rasuwa taci wato “Olori Murjanatu”, Kehinde kuma kai tsaye ya samu sunan Kakansa Emir (Abdulrasheed) ake kiransa “Prince”, kenan Sarki aka yiwa takwara.
Taiwo da Kehinde sun taso cikin koshin lafiya da samun kulawar iyaye wanda ya haifar musu da saurin girma, saidai kowannensu da irin halinsa da irin dabi’unsa.
Kowa ya shaida Taiwo nada fitina, korafi, da mita tun tana karama, duk wani hali na matan yarbawa Taiwo nada shi musamma daukan tsegumi daga kannenta. Nenne Sappa bata shiri da Taiwo saboda kiriniyarta da wadannan halayen nata, gata da tsokanar yara ‘yan uwanta, Abdulrasheed kuwa gashi dai bas hi da aboki na jiki kamar Taiwo to kwatakwata halinsu ba daya bane, mahaifinsa na kiransa “Prince” Emir kuma yace masa “Kehinde”, a zahiri shi irin yaran nan ne kamammu, salihai, introvert, wadanda magana ma wuya take musu a zahiri saidai suyi action a gani, wato Abdulrasheed lumbu-lumbu ne da ake cema wutar kaikayi saidai yanada temper, babu mai sanin abinda ke zuciyarsa don fuskarsa bata bada expression na abinda yake ransa, wato kwarai ya iya waskewa da shanye expression, Nenne Sappa kadai ke iya karantarsa tana ganewa in abu yayi masa a fuskarsa ko bai masa ba. Babansu da suke kira “DADE” sanda suka fara budar baki shi da Taiwo, yaga yadda Prince yake saka Taiwo kuka ta ruwan sanyi, ba tareda iyayensu sun san me yayi mata ba, ya kance “Prince GREEN SNAKE ne”.
Sun rayu tsayin shekaru kusan goma sha biyar shi da Sappa da ‘ya’yansu na fari a kasar Japan, domin saukar su a Japan da watanni kadan suka haifi ‘Prince Kehinde’ da ‘Princess Taiwo’.
Abdulrasheed ya shiga ran Kakansa matuka, kasancewarsa namiji kuma jika na farko a gareshi, ya zama (favourite jika) ga Kakansa Emir of Ilorin, kuma babban aboki na jiki ga Kakansa Sarki Abdulrasheed.
AbdulRashid (Kehinde) da Murjanatu (Taiwo) sunyi primary da secondary duk a Tokyo/Japan, ba tareda an yi masu kanwa ko kani ba, Taiwo na gama sakandire akayi mata aure da Toufeeq Adam Adebayo, wanda aure ne na (family friends) tsakanin iyayen su, Toufeeq Bayarabe ne dan abokin Engnr. Idrees ne, sun zauna a Ilorin da farko inda ta shiga Unilorin ta fara karatu, Taiwo ta jima tana karatu kafin ta fara haihuwa.
Sau da yawa mahaifin Idris Akanni wato (Emir) yana yin tattaki har Japan in yana son ganawa da babban dan nasa Engnr. Idris Akanni, ko kuma in yana son ganin jikansa mafi soyuwa a ransa wato ‘Prince AdulRasheed’, sai da ya soma tsufa sosai ne ya daina yawon bin Idrisu kasar Japan inda yake zaune, don sauran ‘ya’yansa maza sun kawo karfi, sun taru sun hanashi fita daga Najeriya kwata-kwata, ko don kula da lafiyar sa data fara samun tasgaro da maida hankali ga hakkin talakawansa dake rataye a wuyansa.
Daga baya Idrisu din yayi ritaya daga kamfanin safarar jiragen ruwan da yakewa aiki ya dawo gida Najeriya gabadaya da iyalinsa, amma still yaki zama a Ilorin, don gudun sarautar yake, baida sha’awar sarautar gidansu ko kadan, don ma kada watarana a kwadaita masa ita a matsayinsa na babban Da ga Emir, sai yai nesa da gida Ilorin. Inda ya zabi Jihar Lagos don zama na dindindin tareda iyalinsa bayan barinsa aiki da ‘Japanese Shipping Authority’.
Kowannen su cikin ‘ya’yan Sarkin Ilorin (wadanda duk maza ne) su goma dinnan nada ‘title’ na sarauta da mahaifinsu ya nada musu da hannunsa. Suna kuma rike da ‘chieftaincy’ kala-kala na kasar Ilorin.
Idris Akanni, a matsayinsa na babban Da, yanada ‘title’ na Waziri of Ilorin, sai mai bi masa Abdulyaqeen Akanni shine Turaki of Ilorin, sai Zanan of Ilorin mai binsa. Abdulganiyu Akanni ya biyo Zanan, sai Dan Iyan of Ilorin mai suna Abdulfatahi Akanni, sai Abdullateef Akanni wanda shine GrandMufti of Ilorin, sai Malami Ubandoma wato Abdulrazak Akanni.
Biye dasu sune Madawaki, Tafida da Shettima da Mutawalli of Ilorin, duka kannensu ne dake binsu a haihuwa daga iyaye mata daban-daban guda hudu da sarki ke aure bayan rasuwar Olori Murjanatu