NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 13 of 44

kabilar Yoruba da basu yarda da ko bakar al’adar nan tasu ta a fara yin ciki a waje kafin aure ba, sannan bai da amini kaf zuri’arsu irin Adetokumbo Abdulfatahi Akanni. Adetokumbo shine (favourite cousin) dinsa a cikin tarin kannensa maza da suke ‘yan maza zar kaf a family din Emir Abdulrasheed Akanni, wanda ya kasance Da yake ga Dan Iyan of Ilorin, daya daga cikin kannen mahaifinsa. **** **** **** ASALINSU (ILORIN EMIRATE) B ari mu dauko tarihin tun daga tushe, wato asalin kafuwar masarautar Ilorin. Kamar yadda kowa ya riga ya sani Masarautar Ilorin da aka fi sani da ‘Ilorin Emirate’ tana nan a jihar Kwara a yammacin Najeriya, tana daya daga cikin manyan masarautun Najeriya masu dimbin arziki, Ilorin Emirate, wata babbar attajirar masarautar Musulman Yarbawa ce a kasarmu mai dimbin albarka, wadda kafuwar tarihinta ya faro ne daga rayuwar Shaihu Salih Janta, da aka fi sani da (Shehu Alimi). Kenan su din duk da kasancewarsu Sarakai, kuma manyan sarakunan kabilar Yoruba, to manyan Malamai ne, ma’abota sani na na addinin Musulunci da kyakkyawan riko dashi. Su din, har ila yau, sun kasance Shehunnan Yarbawa ne masu dauke da sani na Alqur’ani da Hadisi, wadanda sukayi gadon sahihiyar sarauta ta malunta da arziki mai dimbin yawa daga Kakan-Kakan su Shehu Alimi, sarautarsu sarauta ce mai asali da da kyakkyawar nasaba tun kafuwar kasar Ilorin. Ilorin Emirate, ta kasance (multiethnic Muslim Kingdom) wato cakude take da kabilu da yarurruka daban – daban na kasar Najeriya guda hudu, wadanda suka hadu suka samar da Ilorin Emirate din, sun hada da; Balogun Gambari (Hausa), Balogun Ajikobi (Yoruba), Balogun Fulani (Fulani), Balogun Alanamu (Yoruba). Kowanne bangare wato kowanne Balogun, nada (district head) wato sarkin dake wakiltar wannan bangaren/yankin, karkashin babban Sarki Emir of Ilorin, dattijo mai ran karfe Sarkin wannan zamanin da muke ciki a lokacin yanzu, wato Emir AbdulRasheed Dan Abdullateef Akanni. Engnr. Edrees Abdulrasheed Akanni, ya kasance Da na farko ga Sarkin Ilorin; Maimartaba Sarki AbdulRasheedu Akanni, (the 11th Yoruba-Speaking Fulani Emir) wato Sarkin Ilori na goma sha daya. Engnr. Idris shikadai ne Da a wurin mahaifiyarsa marigayiya Olori Murjanatu (Olori na nufin Queen bisa ga al’adar masarautar), tun Edrees yana yaro ta rasu sanadin cutar sankarar mahaifa. Sai bayan rasuwarta ne aka bawa Emir Abdulrasheed Sarautar mahaifinsa, aka kuma kawo masa mata har hudu daga garuruwan yammacin Najeriya daban-daban ya sake aure, sune suka haifa masa sauran ‘ya’yan sa maza guda tara, har Edrees da matarsa ta farko Morjanatu ta haifa in an hada su goma kenan gabadaya maza ‘ya’yan Sarkin na Ilorin. Emir Abdulrasheed da ya tashi yiwa dansa na fari aure wato Edrees Akanni, sai ya tsallaka ya auro masa Gimbiyar Gombe mai suna (Sappa) diyar abokinsa maimartaba Sarkin Gombe, Ahmadu Umar Jalloh (CFR) daga can cikin yankin jihar Gombe dake arewacin Najeriya. Engr. Idris Akanni tun lokacin da mahaifinsa ya aura masa Sappa Allah ya zuba masa matsananciyar soyayyarta, aure ne na gata irin na ‘ya’yan sarakuna don bai wuce shekaru 27 ba lokacin da aka aura masa Sappa, ita kuma bata fice 17 ba, tun daga lokacin yake kula da ita, don yana matukar son ta kamar ya hadiyeta. Sappa a hannun mijinta Engnr. Idris ta karasa girma ta kuma san rayuwa, ya shiga da ita duniya ta budi ido, wata irin soyayya Idris Akanni yake mata irin dai soyayyar Yarbawa ga kyawawan matan Fulani, (mazan Yarbawan Ilorin na matukar son matan Fulani) har dai in aka yi katari kyawawa ne masu farar fata da gashi yalalaa kamar dai ita Nenne Sappa din. Auren nan nasu ya kafa tarihi a cikin duka zuri’arsu daga bangarensa da nata, domin aure ne irin wanda ba'a taba yi a masarautar Ilorin da masarautar Gombe ba, wato aure tsakanin masarautar Ilorin data Fulanin Gombe, albarkacin amincin dake tsakanin Babansa Emir da mahaifinta Sarki Ahmadu Umar Jalloh (Uban Kasar Gombe). Sarki Ahmadu Jalloh Umar wato (Uban Kasar Gombe) da Sarki AbdulRasheed Abdullateef Akanni (Emir of Ilorin) sun hadu ne tun kafin su zama sarakuna magadan iyayensu, wato tun suna samari ‘yan bana bakwai a jami’a, sun hadu ne a yayin karatun digiri na farko da sukayi tare a can kasar Venezuela (South America) da iyayensu suka turasu inda dukkanninsu suka karanta siyasar duniya (International Politics). Kenan mahaifinsu Idris Akanni wato Emir of Ilorin (AbdulRasheed Abdullateef Akanni aboki ne na jiki tun na kuruciya ga Baban Nenne Sappa, sarkin Gombe Ahmadu Umar Jalloh. Kowa da ya sansu ya shaida Idrisu Akanni na ma Sappa wani irin mashahurin so, kamar babu wata mace a fadin duniya bayan ita. Banbancin harshe da yare bai zamo musu barrier ga soyayya ba. Da fari Nenne ta samu kanta cikin bakunta, kasancewar ta shigo cikin wata kabila da ba t
🏠