nsu, to kullum suna tare a inda ba idon kowa nasu a kansu, yace da Murjanatu yana tsoron watarana ayi abinda ba shikenan ba duk da yana fin karfin zuciyarsa, amma Nenne ta kafe ta ki. Soyayyarsu shi da Hasinah tayi tsananin karfi a lokacin har suka soma sakin layi. Sun buga sun buga da Nenne ta bari ayi auren har lokacin ta ki, don zaman da take yi dasu ma Nenne bata so, tafi so kowanne irin taimako zata yi maka tayi maka shi daga nesa, ba tareda ta dauko ka ta saka cikin zuri’arta ba gudun kada a bata mata tarbiyyarsu. Wannan ne dalilin da yasa suka kawo har lokacin da Hasinah ta shiga mataki na uku a jami’a suna soyayya ba tareda sunyi aure ba.
A irin hakane har ta saba da cousin dinsa mai zuwa gidansa lokaci-lokaci yana sauka a wurinsa wato Adetokumbo Akanni.
Tokumbo a Japan yake harkokin kasuwancinsa, Automobile Business Mogul ne. A daya gefen shi da Murjanatu suna cigaba da fama da Nenne akan dai ta yarda ayi auren haka, amma Nenne tayi tsalle ta dire tace sai a bayan ranta danta zai auri adopted orphan.
A girman nasaba irin tasu, wannan babban abin gori ne a gareta ko a wurin faccaloli, ace duk matan duniya da wadanda ke cikin family din mahaifinsa da nata ace wai Prince ya rasa matar aure sai akan Haseenah da take tsintacciya zai kare kamar wanda uwa tacewa jeka ka gani?
Cikin wannan rikicin suke shi da Nenne har kawo yau, Murjanatu na taya shi fighting gun Nenne don shi Dade dinsu duniya ta shaida mijin tace din Nenne ne, shima da bakinsa yana fada “I obey her decisions because she leave no stone unturned”. Duk hukuncin da Nenne tayi bashi da ja, saboda tsabar yarda da sahihiyar soyayyarsa gareta.
A ganinsu shi da Murjanatu babu wadda zai aura da zata girmama shi, ta kaunace shi saboda Allah irin Haseenah, ga Prince da son girma musamman daga matar da yakeso, kai duk bayeraben basarake akwai tsananin son respect daga mace, a ganinsu ita kadai zata aure shi ba don arzikin su ko don tarin “FAME” dinsa ba (shahararsa a idon duniya).
Duk wata mace da zata aure shi a halin yanzu abubuwan da zata duba kenan (sarauta, kyau, arziki, da shahararsa), sun yi amanna banda ‘yar da ya raina ya ginawa rayuwa da kansa, har a yau take jera kafada da ‘yammata masu gata da ilmi ‘ya’yan manyan Najeriya a jami’ar da take wato Haseenah Bello Ambursa.
Hasinah ta tsinci kanta rana daya a soyayyar ubangidanta kamar koma fiye dashi, bata kuma san daga wane lokaci shakuwarsu ta rikide zuwa soyayyah ba. Duk da banbancin yare dake tsakaninsu, ita Hasinah bata tuna cewa ma ita bahaushiya ce saboda cakuduwa dasu Aunty Murja dashi kansa Prince da ba hausar yake yi bama kwatakwata, ko ya iya ko bai iya ba Allah masani. Duk da ita Haseenah na ganin bata kai matsayin da Prince zai aure ta ba, amma kaninsa Tokumbo dake tare da shi kuma suke shiri itada shi irin sosai kullum yana yawan karfafata da cewa.
“If she’s lucky…. Probably zata iya samun auren PRINCE!”
A bakin Tokumbo Haseenah taji cewa Mamanshi ma bahaushiya aka auro musu ita, tazo ta haifesu shi da su Murja. Shiyasa taga shi da Prince duk da suke ‘yan maza zarr basa kama da juna.
Yace su din surki ne na yare guda biyu; Fulani/Yoruba wato sun hada duka jinin yammaci da arewacin Najeriya, ba kamar sauran ‘ya’yan family dinsu ba da gabansu da bayansu Yarbawa ne.
**** **** ****
Taiwo tayi ajiyar zuciya data tuna asalin haduwar shi da Hasinah da kuma irin sakayyar da Hasinah tayi musu yau. Ita ba suruka ta dauki Haseenah bama face ’yarta ko kanwarta. Don haka taji ciwon lalacewarta duk da tayi iya kokarinta a kanta.
Tafi ganin laifin Haseenah akan na Tokumbo. Ko maiyasa? Don itace mace, kuma ita ta bada kafa har ya sayi mutunci da martabarta daga ido da zuciyar Prince.
Ta tabbatar Hasinah tayi rashi, rashin da duk duniya ya kamata ta taru ta jajanta mata, domin tabbas tayi rashin mai kaunarta da gaskiya sabida son duniya, kwadayi da biyewa zuciya da rashin sanin girman zina da illarta aikatata ga mai yinta a addinin musulunci. But who knows? Ko itama ta hanyar da aka sameta kenan? Sannan bata yi islamiyya ba.
Dr. Taiwo, ‘yar uwa mai rike sirrin dan uwanta, ko bai roketa ba, ya san wannan magana zata cigaba da zama sirri ne a tsakaninsu su kadai, sai ko Allah da ya halicce su, da kuma Hasinan da Adetokumbon. Ko iyayensu tayi alkawarin bazasu ji wannan mummunar maganar daga bakinsu ba.
Domin wani abu ne da zai kawo hargitsi mai girma ga zuri’ar Akanni gabadaya, watakila har ya jawo rarrabuwar kai, wanda basa fata. Jiharsu bakidaya ta shaida hadin kan zuri’ar Akanni da duniya bakidaya, na kasancewarsu tsintsiya madaurinki guda, don in wani ya yarda Adetokumbo zai aikata hakan a gareshi, duba da irin amintakar dake tsakaninsu, da irin taimakon da Abdulrasheed din keyi ga business din Tokumbo, wani bazai taba yarda ba, za’a ce sharri ne, ba don komai ba sai don kasancewar zuri’ar Sarki Akanni tsaftatacciyar zuri’ar