nyar ta dago jin an ambaci sunanta, yayi mata murmushi ya karaso har gabanta yace “sannu da karatu Haseenah!” ta amsa, ta kuma gaishe shi sai ya karbi littafin hannunta yana dubawa. “Basic Science and Technology” ya ga an rubuta a jiki. (For junior secondary schools). Yarinyar zatayi sa’ar Hakeem dan abokiyar tagwaitakarsa Murjanatu. Don haka kawai babu shawara da Nenne yace bari ya dauketa daga nan ya kaiwa Murja in yaso ta hadata da Hakeem su cigaba da makaranta. Kyawunta ya fisgeshi sosai a matsayinsa na namiji, sannan jan ajinta. Dama ance irin wadannan ‘ya’yan kyau ne dasu.
“Ajinki nawa Haseenah?”
“Bana na gama JSS” (tana magana kai a sama, cikin ko’in kula) da gani ba wadatar tarbiyyah.
“Kinada burin cigaba?”
“Sosai ma kuwa, Enginiya nake so na zama”. Sosai yaji yarinyar ta bashi tausayi ko don yadda take magana kanta tsaye da boldness kamar ba marainiya a gidan marayu ba, don mostly yaran zaka same su basu da karsashi, basu da ko guts na karfin gwiwar kallon mutane ma cikin ido, sabida (inferiority complex) dake dabaibaye dasu, amma ita kar take kallonsa cikin ido, idanunta a tsaitsaye, ko kuma don kasancewar fanninsa kenan wanda ta zaba din a matsayin burinta yasa yaji ta burge shi?
Don haka koda suka koma ofis shida Mrs Taibat yayi abinda bai taba yi ba tunda yake zuwa gidan marayu daban daban, watau yabi duk process din da ake bi na daukar yaro a gidan, na daga cike-ciken takardu ha a karshe yayi (adopting) dinta.
Amma a ransa ya san ba dai ya kaiwa Nenne ba, yayi abunsa kai tsaye without a second thought, saidai ya kaiwa Murjanatu, it ace mai biyewa komai yake so mai kyau ko mara kyau, in yaso ya dinga daukar nauyin karatunta a makarantar kwana, shi dai yaji ransa na son kyakkyawar yarinyar, in yaso in akayi hutu ta zauna gidan Murjanatu har ta isa shiga jami’a ya nema mata admission a fannin Engineering din duk da take so. Ko iya haka aka tsaya ya gina rayuwarta, tunda in ta gama zata iya samun aikin da zai isheta kula da kanta har watarana ta tallafi gidan marayunsu da marayu ‘yan uwanta.
***** ***** ****
Ya damka amanar yarinyar a hannun wato Aunty Murjanatu, ya kuma fara biyan komai na karatunta tareda Hakeem yaron Murja. Lokacin ba’a haifi Kiki ba. Murja ta kaisu makarantar kwana ta British int’l school a garin Lagos. Kasancewar duk abinda dan uwanta ke so bata opposing tana taya shi ne su cimma abinnan.
Ta dade da sanin philanthrophic heart dinshi, na cikin dabi’un shi masu kyau, da suka banbanta shi da sauran matasan zuri’arsu kaf!
Ta yarda ta amince babu mutum mai zuciyar halin girma da daukar girma tun bai girma ba cikin jikokin gidansu kamar Prince, duk wani hali irin na Kakansu Emir Abdulrasheed ya kwashe shi ya bar kowa da sudin kwano. A kafatanin zurri’ar gidansu ba mai kyakkyawar zuciya ta taimakon mara galihu irin ta dan uwanta Prince. Tun daga kan kannen mahaifin su, har zuwa tulin ‘ya’yan da suka haifa, ba wanda baya shan rabar taimakonsa (in one way or the other).
Shi Da daya ne tamkar da goma ga iyayensu. Gidansu ba’a tara ‘ya’ya maza ba, shikadai ne namiji a cikinmata amma ya tarewa iyayensu gurbin misalin yara maza goma!
**** **** ****
Shekaru uku suka zo suka wuce da tarin cigaba ga yarinya Haseenah, bai yi kasa a guiwa ba yana biyan kudin karatunta tare dana Hakeem duk shekara, wadda da aka tashi bata permanent name a makaranta sai ya bata surname da sunan marigayin abokinsa Bello Ambursa, wanda ya rasu gaba kadan da daurin aurensa.
Hakika Prince ya ji mutuwar Bello ba dan kadan ba, kullum ya ga Hasinah sai ya tuno shi har kaunarshi da Bello Ambursa ta shafi Haseenah Ambursa, ko bakomai sanadinsa yaje har inda take ya daukota. Daga kan Bello bai kara yin aboki ba sai Tokumbo wanda dama Cousin dinsa ne da suka taso tare.
Duk sanda ya zo kasar Najeriya zai je wajenta a makaranta suyi ta tadi, in kuma suna hutu ne tana gidan Murjanatu acan yake ganinta har sabo mai tsanani ya gitta a tsakaninsu.
A haka har Haseenah ta gama sakandire, a shekarar data kammala ya samar mata gurbi ya kuma yi sponsoring karatunta a wata jami’a a kasar da yake nasa karatun a lokacin, wato Tokyo.
Wannan ne ya kawo kusanci na kamshin soyayya tsakanin sa da marainiyar da yake riko Haseenah, wanda (in no time) ya rikide musu zuwa soyayya. Har shi da Murjanatu suka yanke shawarar ya aureta kawai, don a zamanta a Japan duk da a hostel take rayuwa, tofa kullum tana like dashi a gidansa fiyeda sanda take hannun Murjanatu da gaisuwa da hirar makaranta kadai ke shiga tsakaninsu, acan kuwa bata san kowa ba sai shi, shiyasa koyaushe take like dashi a gidansa a lokutan da bata da karatu, musamman da idanunta suka fara budewa da maza ta san menene soyayya.
Sun yanke shawarar shawo kan Nenne don ta yarda ya auri Haseenah shida Murjanatu gudun sharrin shaidan ya gifta tsakani