NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 99 of 172

et kafin ta kara juyowa tace "Yaya!" Ya kalleta tace "abincin bai huce ba?" Yace "me kikesan ji? Da alama wadannan maganganun naki akwai abinda kike san ji." Tace "bakomai." Ta shige toilet. Da kallo ya bita ya dade kafin yacigaba da cin abincin. Tana fitowa yana gama cin abincinsa, tadan tsaya a jikin kofar saboda ciwon da mararta yakeyi gashi daga bayanta yake tahowa.Da kyar ta taka ta zauna akan kujera tadan tukunkune. Mikewa yai daga kasa ya juyo ya kalleta, bai kawo komai a ransa ba ya dauka dai kwanciyar tai ko toilet din data shiga ne ya sa ta. Komawa yai ya zauna ya dau littafi, dan nishin datai kadan ne yasa ya juyo da sauri ya kalleta. Yace "Jalila!" Dagowa tai ta kalleshi a hankali tace "naam." Ganin haka yasa ya sauko da sauri yazo kusa da ita inda take a kwance, kusa da inda kanta yake ya zauna sannan yasa hannu ya dagota. Kallanta yai itama ta kalleshi yace "menene?" Tace "bakomai yaya..." Yace "menene kikeyi to hakan?" Tace "me nayi?" Idanu ya kara kura mata sannan yace "menene? Karkisa na sake tambayarki." Ta kalleshi tace "marata" Yace "ciwo?" Ta daga kai alamar eh. Yace "kinayi ne ko yau ne kika fara?" Tace "inayi dama." Shiru yai yana kallanta yace " menstrual pain?" Kallansa tai sannan ta saukar da idanta kasa. Yace "ko muje asibiti?" Tace "a'a yaya zai daina zuwa dare." Idanunta tadan runtse dan abin karuwa yake yi. Sa hannu yai ya dagota ya kawota jikin gado yace "kwanta." Kallansa tai sannan ta kwanta. Zama yai kusa da ita yana kallanta, ita kuma idanuwanta a runtse suke tasa hannunta kan kasan cikinta. Wayarsa ya dauko ya shiga google ya rubuta how to relieve menstrual pain. Nan ya shiga dubawa, kallanta yai sa hannu ya gyara mata kwanciyarta zuwa rubda ciki. Juyowa tai ta kalleshi yace "menene?" Kai ya girgiza alamar ba komai sannan ta gyara kwanciyarta. Shiru yai yana tunani, massage lower back and abdomen? Ta ina zai iya? Mikewa yai tsaye da sauri ya koma kan kujera ya zauna dan jin yanda zuciyarsa ke bugawa da sauri. Jalila kam abin ne ya kara motsawa juyawa tai ta kara dukunkunewa tana dan nishi kadan. Kallanta yakeyi sai dai hankalinsa duk ya tashi. Ya mike ya taso kusa da ita ya gyara mata kwanciyarta zuwa na dazu, idanunta ne suka ciciko ta kalleshi tace "yaya hakan bayamin dadi." Yace "na sani daurewa zakiyi." Tace to sannan ta gyara kanta tana runtse ido. Jitai hannunsa akan kasan bayanta inda yake mata ciwo, kallansa tai, ya kalleta shima fuska a hade yace " ki kwanta ba wani abin zan miki ba." Shiru tai ta kwanta, janye rigarta yai yana neman kaita wajen kirjinta, da sauri tasa hannu ta rike sannan ta kalleshi. Kallanta yai idanunsa na kanta ya sa hannu ya zare mata hannunta, shiru tai tana kallansa. Sai dayakai rigar saman cikinta sannan ya tattareta a gun. Hannu ya saka a bayanta yana mata tausa da hannayensa suka biyun. Idanunta ta rufe gaba daya jikinta yai sanye, Hassan kam tausa yake mata sai dai daurewa kawai yakeyi. Kallanta yai yace " kinajin sauki? Naga haka suka rubuta haka akeyi." Ta daga kai idanunta a rufe dan bazata iya kallansa ba. Hassan ya cigaba da yi mata, tun tanajin abin har bacci yai gaba da ita. Ganin alamar bacci takeyi yasa ya kalleta, kusa da ita ya matso ya sa hannu akan gefen fuskarta yadan shafa kadan, meyasa kike sani yin abubuwan da ban taba tunani ba?Ganin motsin idanunta sun canza da alama nauyin baccin nata ya fara raguwa, komawa yai ya sa hannu ya cigaba da yimata. Sai can ya tsaya ya kalleta tana bacci hankalinta a kwance, murmushi yai wanda shikansa bai sani ba. Sannan ya mike ya cire kayansa ya daura towel ya shiga wanka. Bai dade ba dan yana tunanin karta tashi, a hankali ya bude kofar ya fito ya zo zaisa kaya. Wayarta ce tai kara da sauri ya matso ya dauka, number Ummy ce ya daga a hankali yace "Ummy." Cikin mamaki tace "Hassan?" Sageer dake kusa da ita ya kalleta, Ummy tace "Hassan kaine? Ina Jalilan?" Yace "bacci takeyi bata danjin dadi ne." Da sauri tace "lafiya? Me ya sameta?" Yace "ba wani abun bane Ummy sako ne?" Samun kanta tai da wani murmushi tace "a'a bakomai kace kartai abinci ta kwanta ta huta." Yace to ya kashe wayar. Da kallo yabi wayar sannan ya kalleta, me nakeyi hakan? Ajiye wayar yai ya zo ya saka doguwar riga ta jallabiya sannan ya zauna akan kujera ga dau littafi wanda ya kasa karanta ko layi daya. Sai kallanta da yakeyi, duk motsin datai a kansa. Can ya daure ya koma ya maida kansa kan littafin, motsinta yaji, ya mike ya zauna a bayanta ya dan fara yi mata tausa a gun. A hankali ta bude idanunta kallansa tai, yace "kin tashi?" Da sauri ta kalleshi tace "yaya, bansan nayi bacci ba wlh yahkuri." Mikewa yai tsaye yace "ya jikin?" Tace da sauki sosai, yace "ki tashi ki sake wanka amma yanzu kiyi da ruwa mai zafi, sannan kisha ruwan tea black ne." Tace "to." Juyawa yai da sauri ta riko rigar jallabiyarsa. Juyowa yai ya kalleta, yace "menene?" Tace "yaya nagode, sannan kayi hakuri." Shiru yai yana kallanta, yace "kin gode dame?" Tace "taimakon
🏠