NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 97 of 172

ngode Allah ya saka masa da alkairi." Jalila tace "Ameen." Muryar Abba sukaji yana kiran Ummy. Ummy ta falo, Jalila kuma ta dau leda tai dakin Ameera. Hassan na zaune kusa da Abba ta shigo, ta zauna sannan ta kallesu tace "d'a da uba ne suke hirar yaushe gamo?" Abba yai murmushi yace "nikaina ina jiran wannan lokaci, lokacin da Hassan zai zauna dani muyi hirar duniya." Hassan bai tanka musu ba, Ummy tace "wani abun ya faru ne?" Yace "a'a kawai dai sirikarsa ce ta nemi mu barta ta tafi tana kunyar zama gida daya da sirikinta da mu."Ummy tace "hakane munyi laifi da bamuyi wannan tunanin ba, sannan bamu tambayeta ra'ayinta ba." Hassan ya kalli Ummy yace "Ummy ita so take takoma kauye nikuma ina ganin hakan ba solution bane." Tace "mekake tunani?" Yace "gwara a nemarmata gida anan ta zauna karami, can yayi nisa." Murmushi tai ta kalli Abba tace "gaskiya kam yama Jalila nisa wanda zai sata damuwa." Kare tsuke fuska yai yace "Ummy me kike....." Katseshi tai tace " ni ba da komai nake nufi ba." Abba ya kalleta yace "wani abun kike tunani?" Tace "a'a shawararce naga tayi, me zai hana a gidan da ka siya kwananan wanda ke tarauni a maidata can? Naga gidan karami ne sannan ga yarinya ma mai kula da ita." Abba ya jinjina kai yace "hakan ma shawara ce, kinga Allah ne yasa bamu sa haya ba dan har an fara tambaya, Hassan sai ka dau Jalila kunduba gidan sai a sai abunda ya kamata." Yace "to." Bai jira wani abu ba ya mike, yanasan yama Abba godiya sai dai bakinsa bazai iya furatawa ba, harya kai kofa ya juyo yace "Ummy na hau sama." Tace "to Hassan." Ya juya ya fita, Ummy ta kalli Abba tace " Ya kagani?" Murmushi yai yace " tunda na dawo kullum Hassan sai ya bani mamaki, lalai dolene muje muyina doctor godiya ba shakka shawararsa itace babban magani a tattare dashi." Ummy ta sake yin murmushi..... Jalila kuwa tana shiga daki inda Goggo take ta hau nuna mata kaya, Ameera kam tana gefe tana mamaki, kenan mahaifiyarta ce ta asibitin nan? Me yasa a lokacin bata nuna mata itace mahaifiyarta ba? Goggo ta kalli Jalila tace "Jalila garin yaya kika barshi ya kwaso kaya haka? Kudi fa aka sa aka siya." Ameera tai dariya tace "Goggo ashe ke tayo, shiyasa takasa bari na dau kaya ko daya wai tsada, sai da yaya yazo." Goggo ta kalli Ameera tace "ke kuwa yar nan ina zan kai kayan nan?" Jalila ta kalli Goggo wani abu ya tsirga mata na tausayi, tunda Goggo take bata saka kaya masu tsada haka ba, ba ta tana samun kaya kwatan yawan wannan ba, gaba daya kayanta......." Idanunta ne suka ciciko ta kalli Goggo tace "yaya ya fadamin abinda kikace." Tace "ya sanar dake?" Jalila ta daga kai, Goggo ta riko hannunta, Ameera tai saurin fitowa daga dakin. Goggo ta kalli Jalila tace "Jalila kiyi hakuri, nasan burinki ma shirme nasan ganin mun zauna tare bayan kinyi aure sai dai ko a da can jinki nakeyi dan bazan iya zama da sirikina ba." Jalila ta daga kai alamar ta fahimta dan batasan tai kuka. Goggo ta kalleta tace "shiyasa a koda yaushe ake cewa Allah ba azallumin bawansa bane, Jalila ban taba tunanin zakiyi aure cikin gata irin wannan ba, gaba daya mutanen gidan nan zuri'ace ta albarka, dolene mu gode ma Allah akan baiwar daya miki ta samun dangin miji irin wannan." Jalila ta kalleta idanunta suka zubo da kwalla, Goggo tai murmushi tace "nikam wannan yaran kanin mijinki....." Da sauri Jalila tace "oh Ya Sageer? Oh Goggo kinsanshi ne?" Kallanta tai taga ba wani alama ta wani abun tace "a'a na dai ganshi a asibiti." Jalila tace "oh haka ne." Sundanyi hira kafin ta mike ta fito. Tunda ta shiga daki taganshi a kwance ta fito ya dawo falo ta zauna, yunwa ce ta sata shiga dakin a hankali ta dauko tiren abinci ta fito falo taci ta zauna tana danne danne a waya, daga baya ma ta sauko kasa sukai girki ta koma gun Goggo sukai hira da Ameera. Abincin ranarsu ma data kai taga yana kwance ta diba ta fito falo taci ta koma kasa sai da suka gama abincin dare ita da Ameera sannan ta dauko nasu ta hawo sama. Yanzu kam a kasa ta ganshi kan sallaya yana karatu, gefe ta koma ta zauna tana sauraran kartun nashi, tana lumshe ido saboda dadi, tana bala'in sha'awar taga tana rera karatunn qur'ani haka. Hassan na nan zaune har aka kira isha'i sannan yai sallah, itama tai. Sai binshi take da kallo tanasan tamai magana amma ba fuska. Mikewa tai ta zubo mai abinci tace "Yaya ka sauko kaci abinci." Kallanta yai yace "ban dade dacin na rana ba." Ta mike daga zaman datai a kasa ta matso kusa dashi jikin gado tace "Yaya dan Allah menene? In laifi na maka dan Allah kayi hakuri." Idanunya kura mata, a ransa yace "me kika min? Haushin kaina nakeji da duk abinda zanyi tun dazu sai naji kina raina, haushin kaina nakeji nasan na ganki kusa dani, haushin kaina nakeji na rashin sanin abinda ke damuna a kanki." Jalila ta kalli yanda ya kafe ta da ido kana gani kasan tunani yakeyi, tace "Yaya?" Littafinsa ya dauka baice mata komai ba. Tsayawa tai shiru kafin ta zauna taci abincin nasa data zuba, kadan ta iyaci dan ya mata yawa. Har dare Hassan
🏠